← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 80

Sashe 62

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan akwai sabulu Mai suna HALFCAST SOAP hmmm hajiyata duk yadda za,ai karki Bari abaki labarinshi Dan sabulune dayake aiki cikin kwana uku kacal 👌zakiga yadda kalarki zata koma kiyi haske me kyau bana bleeching ba haka Zaki dinga sheki kina haskawa acikin jama,a 🔥🔥🔥
Koda kindaina amfani dashi ba,abunda fuskarki zatai saboda natural ne Wanda sukai bleeching yabata musu jiki dafuska Kuma kunemeshi Yana dawo dakalar fata baidaya bacan Baki nan fariba 😄
Akwai cream gamasu San suhada set Wai ai hajiyata saikin zama taurariya acikin taurari mudin kika mallakeshi💃💃💃
Kira ko WhatsApp 09037870422

Karku manta muna da supplement kala kala

Na matsi
Na gyaran breast
Na hips
Na slimming
Na fari
Na gashi
Dasauransu

Haka zalika muna :

HADIN MAI JEGO
HADIN UWARGIDA
HADIN AMARYA

Kuma duka afarashi me rahusa kedai kawai kituntubeni 👇👇
09037870422

Muna garin kano muna tura Kaya ko,Ina cikin aminci 🤝

Sai Allah yakawoku

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 80*

Kabiru da sauri ya tarota dan Yana buga mata kwalbar da baisan ma Wanda ya ajiye akan center table din palon ba tayo baya ,jiki na rawa ya hau janta dan da iya karfinsa ya buga mata ya danne bakinta da hannu daya yayi d'akin Sajeeda da ita,yana janta.

Tunda yake bai tab'a shiga tashin hankali irin wanan ba, tuni jini ya wanke masa jiki da kasan tiles din palon dan kanta ya fashe yana Jin tana sallati kasa kasa kafin ta sume Yana shigar da ita d'akin Sajeeda ya ajiyeta yayi waje cikin tashin hankali sam baisan ma abinda ya dace yayi ba,idan har ya bari aka shigo gidan dole zaa ga jini duk da yasan ba Mai zuwa,hankali a tashe ya nufi kitchen ya d'auko tsumma da ya gani a rataye ya hau goge jinin daga Kan stairs zuwa k'ofar d'akin Sajeeda,har lokacin Yana jiyo yadda Gurnanin ta daga sama,Yana gama gogewa ya fara Neman wayarsa dak'yar ya gano ta a cikin jallabiyarsa da ya cire ,sai hada zufa yake,har zai koma d'akin Sajeeda Saboda yaga halin da Yaya Asmau ke ciki sai Kuma ya fasa yayi d'akin Yesmeen dan gani yake zata iya guduwa taje ta tona Masa asiri,gwara Yaya Asmau ta sume yasan ba inda zata iya zuwa.

Yana Shiga d'akin Yesmeen yayi wajen bandakin ta ya hau tura k'ofar bandakin yaji a rufe,ya hau bugawa Yana "Ki bud'e min k'ofar Nan Yesmeen"

"Wallahi bazan bud'e ba Abba a bandakin nan zan ta zama har sai na samu mai zuwa ya taimaka min"

"Yesmeen idan Kika bari na b'alle k'ofar nan na shigo na rantse da Allah sai na kasheki ki bud'e min k'ofar magana Zan Miki ba abinda Zan miki indai kin tabbata baki taba fadawa kowa sirrina ba"

"Ban tab'a fadawa kowa ba Abba amma bazan bud'e k'ofar nan ba,Kuma wallahi Abba ko ka balle k'ofar nan ka shigo kafin ka kasheni sai na tona maka asiri,tamkar mahaifina na d'auke ka amma shine kake so ka cutar dani ka lalata min rayuwa Abba duk akan neman duniya ka cire rigar imanin ka ka cutar da umma iya nan bai isheka ka hau farautar rayuwata ta karfin tuwo sai ka ga bayana saboda nasan sirrinka,Abba gaggawan Mai kake yi mai kake nema a gidan duniya da har zaka yanki ticket din da zai maka katanga da samun Rahamar Allah ka manta da duk kudin mutum sai ya mutu,ka manta da duk abinda mutum ya tara a gidan duniya yake barin sa,ka manta da bawa baya mutuwa sai ya cinye rabon da Allah ya tsaga zai samu,Abba kayi gaggawa wanan kudin da akansa ka kauce hanya dama naka ne Allah ya rubuta sai kayi kudin,wuyanta ka cigaba da hakuri har zuwa lokacin da Allah zai Buda maka ka samu,amma gajen hakuri ya sa kaje ka jefa kanka a hallaka,umma da bata maka komai ba ka lalata mata rayuwa,yau idan ka Fadi ka mutu Kai kadai zaa binne a kabarinka ba ko cokali da zaa bika dashi,zaman duniya na dan lokacine lahira kuwa dindindin ne, duk wani abu da kayi a gidan duniya wallahi sai kayi wa Allah bayani,Ina ka Kai ilimin ka Abba duk akan duniya da kasan ba Wanda ya tab'a dawwama a cikinta duk Inda ka Kai ga tara dukiya ka sabawa Allah wallahi dole sai ka koma gare shi ka masa bayanin yadda ka tara dukiyar da ka Tara ta hanyar zalintar bayin sa"

Kabiru wani irin duka ya kaiwa k'ofar Yana
"Yesmeen ni kike fadawa maganganu yau ni na Zama sa'anki kike so ki nuna bani da ilimi"?

"Abba gaskiya na fada maka ba magana nake fada maka ba ka tubarwa Allah tun wuri kafin lokaci ya kure maka amma wallahi indai ka dage sai ka cutar dani Abba Koda kayi nassarar kasheni Zan ta rokon Allah a kabarina akan ya tona maka asiri ya bankada sirrinka kowa yasani"

naushi ya kaiwa k'ofar Yana Jin kirjinsa kamar ya fado saboda yadda yaji maganganun ta na kona shi da ace zai iya balla k'ofar wallahi ba abinda zai hana ya raba Yesmeen da ranta yaso ace ita ya bugawa kwalbar palon gashi yanzu hankalinsa ya rabu gida biyu ga yana tsoron ya tafi d'akin Sajeeda wajen Yaya Asmau gashi Yana tsoron idan ya tafi Yesmeen ta fito,tunanin kulle dakin da mukulli ne ya fado masa ya bar bakin k'ofar da sauri yayi hanyar k'ofar Yana zuwa ya zare mukullin ya fita waje ya kulle,ya tafi da mukullin dan a yau sai ya kashe Yesmeen bari ya fara tunanin yadda zai yi da Yaya Asmau.

D'akin Sajeeda ya koma Yana Shiga yaga Yaya Asmau har lokacin a sume bata farfado ba,har ga Allah bazai so Yaya Asmau ta mutu ba,a rayuwa idan akwai wacce ya tab'a yiwa shaawar mutuwa Kuma yake Jin zai iya kasheta da hannun sa Yesmeen ce.

Hannunsa wani irin rawa yake dan Yama kasa rik'e wayar sai da ta Fadi wajen sau uku kafin ya iya nemo lambar Rabiu ya hau kiransa yana share zufa gabad'aya ya rasa mai ke Masa dadi, gashi a yau ake so ya nemi mace ta baya

Rabiu na dagawa ya fara magana Yana "Rabiu na Shiga uku asirina ya tonu,Yar uwar sajeeda tazo ta kamani a d'akin Yesmeen, gashi na buga Mata kwalba na rasa yadda zanyi da ita Rabiu mai yasa banida saa ne duk wani Abu idan zanyi sai an samu matsala?kasan kuwa Yesmeen tana gani Ina zuwa dakinta tace tana kallona duk tsawon lokacin nan da na dauka ta makance ashe tana gani,duk abinda nakeyi akan idonta ne? Kaga yadda yarinya nan ta fadamin maganganu Rabiu a fadawa shugaba ya kashe min yesmeen yanzu a taimaka min,ta Sha alwashin sai ta tona min asiri idan har na nemi na cutar da ita har wani barazana take min,duk wahalar nan da nake Sha ake saka ni abu Ashe yarinya Nan ce ke warware min komai,gashi yanzu Yar uwar Sajeeda tazo ta rintsani a d'akin ta tsirara itama ta dage zata tona min asiri Rabiuu na Shiga uku yanzu ya zanyi?

"Yanzu Ina Yesmeen da Yar uwar Sajeedan??

"Yesmeen ta kulle kanta a bandaki ita Kuma Yar uwar sajeeda gata nan a sume a gabana na rasa yadda zanyi Rabiu"

"Toh ka kwantar da hankalin ka ni banga abin tashin hankali anan ba sai kayi ta Abu kamar namiji ba dai duk ka dagawa kanka hankali bane saboda Kar asirinka ya tonu, to ka kwantar da hankalin ka asirinka bazai tonu ba,akwai Wanda yasan Yar uwar sajeeda tazo gidanka"?

"Bansan zata zo ba ba Wanda yamin waya kawai ganin ta nayi ba Kuma kowa a gidan dan yayar Sajeeda da yaran sun tafi wajen Yata da nace maka ta haihu ni kadai ne a gidan sai Yesmeen da Sajeeda dake sama"

"Da kyau yanzu ka samu ka nemi Yesmeen"?

"Ina ban nemeta ba Rabiu gashi kasan shugaba yamin gargadi Kar a samu matsala wanan wane irin masifa ne Rabiu tunda na shiga kungiyar nan ban Kara samun kwanciyar hankali ba,kudin ma na kasa cin sa cikin kwanciyar hankali"

"Yayi wuri ka fara tunanin yin nadama, tun farko da mun sani an kashe wanan yarinya da bana Jin zaa samu wanan matsalar toh idan har za'a saka ka aiki ta ganka ai dole ya warware ayi ta baka wani kayi,yanzu shawarar da zan baka ba kace Yar uwar sajeeda ta sume ba,ka nemeta ta bayan ka goge jikinta da kyallen nan ka murde Mata wuya kawai daddare kaje ka Yar da ita,ka kashe wayarta saboda Kar a zargi ta iso gidanka,ka fito ka sallami mai gadi,idan ka gama da Yar uwar Sajeedan sai ka balle k'ofar bandakin ka fito da yarinya nan ka daureta ka kawo mana ita kungiya ayi amfani da jininta kawai"

Girgiza Kai Kabiru ya fara yi cikin tashin hankali Yana "Rabiu bazan iya kashe ta ba gwara dai na nemetan inyaso ayi mata abun da zata samu tabin hankali yadda bazata tona min asiri ba wallahi bazan iya kasheta ba Kar abin yamin yawa"

"Bakada hankali Kabiru ga abinda zakayi nan cikin sauki asirinka ya rufu idan ta warke fa idan Suka dage da Addu'a ka nemeta ta bayan Ina jiye maka wallahi idan baka Yi aikin da aka baka ba,Ina jiye maka abinda zai biyo baya,daga lokacin da kayi rantsuwa zaka Shiga kasan ba fita,ka Kuma Sha jini akan bazaka tsallake duk sharuddan da aka kafa ma,har da Kare ka kwanta kaje makabarta ka kwana sai da kazo wajen da zaka ringa kananan abubuwa zaka nemi ka karaya ka nemeta nace yanzu bamu da lokaci"
Chapter 62 · 0% Book details