← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 80

Sashe 64

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba kunya ba tsoron Allah Suka ajiye Yaya Asmau wajen da ba yawaitar mutane

Suka ja motar a guje kafin su isa gidan.

Kabiru haka ya ringa hararo yadda zaici uban Yesmeen kafin ya kasheta dan duk ita ta ja masa wanan masifar,dan Koda wasa bai tab'a tunanin akwai Wanda ke shiga dakinsa da ga ajiye kayan tsafin su ba yesmeen ta cutar dashi.

Yana isowa gidan Rabiu yayi zamansa a mota Kabiru yayi cikin gidan da sauri tare da nufar wajen k'ofar Yesmeen Yana zuwa bakin k'ofar ya ganta a bud'e hankali a balain tashe ya fada d'akin Yana "Shikenan ta gudu wallahi ta gudu ta tona min asiri"

"Ya nufi k'ofar bandakin Yana tura k'ofar yaga wayam ba kowa ya saki wani irin ihu Yana "ta kasheni wallahi ta gudu Rabiu"

Ya fito daga d'akin Yesmeen a haukace ya hau sama dan ya duba Sajeeda........

Labarin Nan fa da tsayi wallahi na gaji masu so na saka ra'ayin su bazan iya ba yadda labarin yake haka Zan rubuta na Kuma yanke da yawa ma ahaka.....

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

ALBISHIRINKU 🥳🥳 ALBISHIRINKU 🥳🥳🥳🥳 MANYAN MATA
Takunce dai A&Z COLLECTION takara zuwa muku da kayanta masu sauki da inganganci👌👌

Muna da supplement nau,i kala kala

Sannan akwai sabulu Mai suna HALFCAST SOAP hmmm hajiyata duk yadda za,ai karki Bari abaki labarinshi Dan sabulune dayake aiki cikin kwana uku kacal 👌zakiga yadda kalarki zata koma kiyi haske me kyau bana bleeching ba haka Zaki dinga sheki kina haskawa acikin jama,a 🔥🔥🔥
Koda kindaina amfani dashi ba,abunda fuskarki zatai saboda natural ne Wanda sukai bleeching yabata musu jiki dafuska Kuma kunemeshi Yana dawo dakalar fata baidaya bacan Baki nan fariba 😄
Akwai cream gamasu San suhada set Wai ai hajiyata saikin zama taurariya acikin taurari mudin kika mallakeshi💃💃💃
Kira ko WhatsApp 09037870422

Karku manta muna da supplement kala kala

Na matsi
Na gyaran breast
Na hips
Na slimming
Na fari
Na gashi
Dasauransu

Haka zalika muna :

HADIN MAI JEGO
HADIN UWARGIDA
HADIN AMARYA

Kuma duka afarashi me rahusa kedai kawai kituntubeni 👇👇
09037870422

Muna garin kano muna tura Kaya ko,Ina cikin aminci 🤝

Sai Allah yakawoku

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 85*

Yesmeen

Kuka da Addu'a kawai ta ringayi a bandaki,tana Jin motsin Kabiru dake bude k'ofa Yana rufewa,tasan indai ta bud'e k'ofar ta fito sunanta matacciya abinda ya bata mamaki tasan wani ya shigo d'akin amma Bata San koma waye ba,dan da sauri aka koma, ta dauka Wanda ya shigo zai kawo mata agaji sai dai shiru take ji,haka tayi ta kasa kunne tana Jin motsin sa,a lokacin da ta ji karar bud'e gate da tashin motarsa hannuwa ta daga sama ta hau yiwa Allah godiya dan a yau zata bar gidan bazata sake tayi Wasa da wanan damar ba,Sajeeda kawai take ji batasan yadda zasu gudu ba.

Duk da tashin motarsa da taji,kin fitowa tayi daga bandakin dan gani take kamar tarko ya danna mata dan ta fito daga bandakin,jin bata Kara Jin motsi ba yasa ta murza mukullin a hankali ta fara leko da kanta a hankali ganin babu kowa yasa ta fito daga bandakin da balain Sauri,tana zuwa bakin kofa taga a kulle da alama Kuma ta waje aka kulle k'ofar, tuni ta zub'e a kasa ta hau rizgar kuka,dan bata san ta hanyar da zata fita daga d'akin ba,ta mik'e da sauri ta hau duba windows din d'akin,nan ma ba hanya dan duk da bugular a jiki,ko kanta ma bazai iya fita ba,haka ta koma bakin kofa ta ringa jijjigawa wai ko zata samu k'ofar ta bud'e,gashi ba waya a hannun ta ballantana ta Kira wani,idan zata shekara tana bugu mai gadi bazai tab'a jiyota ba,

Tuna kila zata iya samun extra mukulli a drawers din d'akin yasa ta mik'ewa a zabure ta hau hargitsa d'akin.

Ta kusa minti talatin tana duba d'akin kafin ta samu wasu mukulai a saman drawer d'akin,jiki na rawa ta dauki mukulayen ta hau gwada bud'ewa,har ta fara karaya dan duk bana k'ofar bane,tana gwada na kusan karshe taga k'ofar ta bud'u,ta saki wani irin ajiyar zuciya tana yiwa Allah godiya, hijabinta kawai ta saka tana fitowa ta haye sama da sauri dan maigadi zata roka ya taimaka mata ya dauko Mata sajeedan dan ji take bazata iya tafiya ta barta ba.

Tana zuwa ta tura k'ofar d'akin ta hango Sajeeda na kife a kasa sai numfarfashi take Yesmeen da gudu ta karasa wajenta ta dagata tana hada ido da Yesmeen ta hau hawaye so take tayi gurnani magana amma ta kasa Saboda jikinta duk a mace saboda rashin kwari makogaranta wani irin zafi yake saboda gurnanin da ta ringa yi da jiyo ihun Yesmeen,ji tayi numfashi ma wahala yake Mata,hannun ta da take iya dagawa ta hau shafa Yesmeen tana gurnani kasa kasa

"Yesmeen Mai ya miki Allah yasa Bai cutar dake ba,bani da kafa Yesmeen Ina Jin ihunki ba dama na taimaka miki"

Yesmeen da tsananin tausayin yadda ta shigo taga Sajeeda a kife yasa ta Kara rushewa da kuka tasan gurnanin da take magana take amma bazata iya gane mai take cewa ba, tuna bata da lokacin zama Kabiru na iya dawowa ya rutsa su yasa ta jinginar da Sajeeda a jikin gado tana "Umma guduwa zamu yi bamu da lokaci Abba idan har na sake ya dawo nasan sai ya kasheni,har d'akina yazo zai min fyade umma yau ya gane Ina gani,ya rantse sai ya kasheni bari na Nemo abin hawa yanzu nan na dawo kinsan bazan iya d'aukar ki ba Umma"

Yesmeen duk da sauri take magana tana k'ok'arin mik'ewa taji Sajeeda ta ruko hannunta da sauri jikinta sai rawa yake

Yesmeen ta koma ta tsugunna Sajeeda ta hau jijjiga Mata kai tana gurnanin magana "Ki tafi ke kadai Yesmeen mutuwa Zan yi kirjina ciwo yakemin zuciyata zafi take min ba amfanin rayuwata tawa ta riga da ta Kare kimin alkawari Zaki tonawa Kabiru asiri idan Kika gudu,Yesmeen Allah ya Miki albarka ya cigaba da kareki zan je na hadu da Yar uwata mahaifiyar ki,ki gudu kawai Yesmeen karki bari ya dawo ya Sameki"

Yesmeen da ba gane Mai Sajeeda ke cewa tayi ba ta dafa ta tana "Umma kinsan bansan Mai kike cewa ba bari na Kira Mana Mai motan ko Mai gadi ya sauko dake mu buya a wani wajen"

Sajeeda girgiza Mata Kai ta hau yi tana grigiza Mata hannu

Yesmeen kuwa tayi waje da sauri,Sajeeda ta bita da ido hawaye na cigaba da gudu a fuskarta, numfashinta k'ok'arin daukewa kawai yake tana Jin wani irin nauyi a kirjinta sallati kawai take tana adduar dacewa da Rahamar Allah dan ji take mutuwa kawai za tayi dan daga lokacin da taji ihun Yesmeen taji abu ya soketa a kirji,tasan Kabiru lalatawa Yesmeen rayuwa kawai yake so yayi,a yanzu bata san matsayin da zata ajiye shi ba Dan ya wuce duk Inda take tunani, ihun Yesmeen yasa ta fara k'ok'arin sauka daga gadon Amma ta kasa har sai da ta motsa jikinta da karfi,ta fado daga Kan gadon gurnani kawai take da iya karfinta tana Jin kamar makoshinta na tsagewa sai Addu'a take akan Allah ya hankado wani ya taimakawa yesmeen, tuna Kabiru kila dan Neman biyan bukatarsa yake san neman Yesmeen kila ma ya cutar da ita kamar yadda ya cuceta yasa taji kirjinta na wani irin nauyi da suya har numfashinta na d'aukewa a wanan halin taga Yesmeen ta Fado dakin.

Yesmeen

A guje tayi gate Mai gadi da bai tab'a ganin ta ba dan bai tab'a ganin ta fito ba ya mik'e tsaye Yana kallonta har ta iso wajensa tana hakki

Sai dai Yesmeen tuni taji jikinta yayi sanyi da irin kallon da Mai gadi ke mata da alama bazata samu kansa cikin sauki ba.

"Baiwar Allah daga Ina lafiya dan Ina zaune a gate dinan banga lokacin da Kika Shiga ba"?

"Ni Yar gidan ce baka tab'a ganina bane dan ba fitowa nake ba,dan Allah matar gidan ce ba lafiya so nake ka taimaka min ka samo min abun hawa na Kai ta asibiti"

Wani irin kallo Mai gadin ya hau yi mata dan ji yayi Sam Bai yarda da Yesmeen ba dan bai tab'a ganin ta ba,ko matar gidan da take fada dazu suka yi tafiya da Yara dan duk tunanin sa Yaya Abu ce matar Kabiru tunda har rakosa wajen motar take wani zubin,bai Kuma tab'a ganin Yesmeen da Sajeeda ba

"Dan Allah ka taimaka min idan bazaka Kira Mai mota ba ka taimaka min mu sauko da ita sai na kai ta asibitin dak'yar take numfashi Kar tazo ta mutu dan Allah"
Chapter 64 · 0% Book details