← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 80

Sashe 67

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mik'ewa tayi Kamar an tsikareta ta d'auko wayarta da taji Yana ta ringing ganin lambar da Yesmeen ta kirata dashi ne yasa ta dauka cikin ihun kuka ta fara magana tana "Allah ya isa tsakanin mu dake Yesmeen,duk tsawon lokacin nan kinsan dama abinda yake damun Umma baki tab'a fadawa kowa ba,ko bazaki fada wa kowa ba ai ya Kamata ki fadamin ko dan umma ba mahaifiyar ki bace, shi yasa Kika barta duk tsawon lokacin nan a kwance Muka rasa sanin wane irin cuta ne yake damunta, tun kafin ku bar garin nan Yesmeen kinsan Abba ya cutar da umma a madadin ki fada da wuri,mu ceto umma amma kikayi shiru Yesmeen wallahi idan Abba ya Kara cutar da Umma bazan tab'a yafe Miki ba wallahi kinfi abba mugunta har kuka koma Abuja su Saifullahi sun dade kafin su tafi baki fada musu ba yesmeen kece ma kika kashe umma ba Abba ba,kina tunanin da ace yau mahaifiyar ki na raye naga abinda zai cutar da ita bazan taimaka Mata ta hanyar fadawa mutane su Kai Mata agaji ba"

"Ya isa haka Nusrah ki barni nayi miki magana Mana ki saurareni mana, Abba ya wuce duk Inda kike tunani yanzu ba lokacin da zaki Tsaya ganin laifina bane,ki kirawo Gwaggo ki fada mata halin da ake ciki,mama bakinta daya da Abba wallahi itama so take ta kashe umma sau uku tana gwada saka wa umma guba a abinci,idan kika fada Mata wallahi ba abinda zatayi akai kiyi sauri ki kira Gwaggo Nusrah"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Yesmeen Allah ya tsine Miki albarka duk kinsan wanan masifar baki fadamin ba sai da na tura mama wajen Umma idan har wani abu ya samu umma wallahi bazan yafe miki ba muguwa azzaluma"

Nusrah da jikinta ke balain rawa ta kashe wayar tana jin numfashinta na neman d'aukewa.

Hannunta rawa kawai yake ta nemo lambar Saifullahi na waje da yake yawan kiranta dashi,sai da ta Masa miscall uku a na hudu ya dauka,tana Jin muryarsa ta saka ihu tana "Saifullahi Abba ya kashe umma, Ashe Abba kudinsa bana halal bane ashe Abba shine silar jefa umma a halin da take ciki"

"Bangane ba Aunty Nusrah mai ke faruwa ne kimin bayani yadda Zan gane"

Nusrah labarin da Yesmeen ta bata duk ta kwashe ta fada masa ta Kara da "wanan wane irin balai ne, akan kudi Abba ya kassara rayuwar Umma,ga itama yayarta itama farautar ranta take mai umma ta musu da zafi haka Yesmeen ta cucemu wallahi idan har mama ko Abba Suka cutar da ita bazan tab'a yafe Mata ba Saifullahi yanzu mai abin yi banida lafiya ya za'ayi mu ceto umma bana so mijina yasan halin da ake ciki"

"Zan kiraki yanzu Ina zuwa"

Kiit taji Saifullahi ya kashe wayar a daidai lokacin da Yaya Abu ta turo k'ofar ta shigo ta zuba mata ido tana kallonta ta kasa yarda wai yayar mahaifiyar ta ke san kashe ta"

Yaya Abu kuwa jakar hannunta ta fara k'ok'arin ajiyewa tana "Nusrah wai kuka kike har yanzu ki daina kuka haka wallahi karyar Yesmeen ne sata tayi wa mahaifinku shine ta yanke ta kala Masa sharri,naje har tashan ba motar Abuja gobe asubanci zanyi karki damu wallahi babanku bazai iya cutar da Sajeeda ba,Yesmeen Yar iskar yarinya ce sharri kawai take yiwa babanku wallahi ki daina dagawa kanki hankali"

"Hakane Mama Abba bazai iya cutar da ita ba sai dai idan Yan uwanta"

Yaya Abu da ido ta bata a lokacin da ta yi hanyar waje bayan ta dauki jaririyar ta sai ta kasa gane Inda maganar ta ya dosa.

Kabiru

A zub'e yake a gaban shugaba ya jike jagab da gumi,jikinsa rawa kawai yake da yaji maganar da ke fitowa a bakin shugabansu da ya Sha bakakken Kaya da wani murtukekken Kare a cinyarsa,Yama kasa d'aga Kiran da ake masa,

Cikin wani irin murya shugaban yace "ka daga wayar ka dan banaso hankalin ka ya rabu gida biyu"

Kabiru wayar ya d'auko daga gaban Aljihunsa,ganin Saifullah ke kiransa yasa yaji gabansa ya Fadi.

A hankali ya Kai wayar kunnensa bayan ya daga wayar.

Cikin wani Irin murya yaji Saifullahi na "Abba Ina Umma take"

Kabiru Bai San lokacin da ya mik'e tsaye ba kirjinsa kamar ya fado,murya a kakarye ya daure yace "Lafiya kuwa Saifullahi Ummanka na gida Mana Mai ya faru"?

"Abba Kai mugune azzalumi, asirinka ya tonu,wallahi Kar Wani abu ya samu umma har na dawo idan har wani Abu ya samu umma Abba da hannuna Zan kashe ka,idan har zaka iya cutar da umma wallahi nima Zan iya kasheka karka yarda wani Abu ya samu umma na fada maka"

Daga haka yaji ya kashe wayar Kabiru ya zube kasa tare da sakin ihu.

Saifullahi kuwa Yana kashe wayar ya Nemo lambar Gwaggo dan a yanzu ba mai taimakawa Sajeeda sama da ita.

Kabiru

Mai ya rage min babu shugaba,yarana sun gano sirrina yau dana shi yake cewa zai kasheni, ribar Mai na samu a shiga kungiyar nan na Shiga uku shugaba yanzu ya zanyi"...
ALBISHIRINKU 🥳🥳 ALBISHIRINKU 🥳🥳🥳🥳 MANYAN MATA
Takunce dai A&Z COLLECTION takara zuwa muku da kayanta masu sauki da inganganci👌👌

Muna da supplement nau,i kala kala

Sannan akwai sabulu Mai suna HALFCAST SOAP hmmm hajiyata duk yadda za,ai karki Bari abaki labarinshi Dan sabulune dayake aiki cikin kwana uku kacal 👌zakiga yadda kalarki zata koma kiyi haske me kyau bana bleeching ba haka Zaki dinga sheki kina haskawa acikin jama,a 🔥🔥🔥
Koda kindaina amfani dashi ba,abunda fuskarki zatai saboda natural ne Wanda sukai bleeching yabata musu jiki dafuska Kuma kunemeshi Yana dawo dakalar fata baidaya bacan Baki nan fariba 😄
Akwai cream gamasu San suhada set Wai ai hajiyata saikin zama taurariya acikin taurari mudin kika mallakeshi💃💃💃
Kira ko WhatsApp 09037870422

Karku manta muna da supplement kala kala

Na matsi
Na gyaran breast
Na hips
Na slimming
Na fari
Na gashi
Dasauransu

Haka zalika muna :

HADIN MAI JEGO
HADIN UWARGIDA
HADIN AMARYA

Kuma duka afarashi me rahusa kedai kawai kituntubeni 👇👇
09037870422

Muna garin kano muna tura Kaya ko,Ina cikin aminci 🤝

Sai Allah yakawoku

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 87*

"Ka taimaka kayi min aiki shugaba idan asirina ya tonu tun yanzu ribar mai naci a Shiga kungiyar nan,da na kassara rayuwar matata dan na samu kudi,yarana suji Dadi,sai gashi tun baaje koina ba asirina ya tonu"

Ihun kuka kawai Kabiru ke yi yana ya Shiga uku,shugaba kuwa kamar ba dashi Kabiru yake ba.

Ya mik'e tsaye da karensa ya na k'ok'arin nufar wani k'ofa da ya Sha Jan kyalle

Rabiu kuwa yayi saurin dira a gabansa ya zub'e a kasa dan yafi Kabiru sanin komai game da kungiya idan shugaba ya bawa banza ajiyar ka ka Kade har ganyenka idan har shugaba yayi shigar bakakken kaya da Wanan Karen a cinyarsa toh ka Shiga uku ka lalace

"kayi hakuri shugaba yayi kuskure yayi ba daidai ba a taimaka ayi Masa afuwa Kar a yi Masa hukunci mai tsauri a taimaka shugaba duk abinda kace yayi zai yi dan asirinsa ya rufu a taimaka"

"Ka kawo Mana lusari mai bakin jini,da rashin nassara,kungiya bata tab'a haduwa da mai kawo Masa matsala ba sama da wanan abokin naka,a kaida duk Wanda ya san sirrinmu sai ya mutu,a kai'da duk Wanda ya ganmu da idonsa sai an kawo Mana shi munyi amfani da jinin sa,daga ranar da aka fara saka shi aiki bai tab'a nassara ba,kungiya ta cigaba da daga Masa kafa,yasan bazai iya ba mai yasa ya shiga tun farko,ya dauka nan wajen Wasa ne, wanan bashi ne dan nasa ba"?

Duk maganar da shugaban ke yi bai juyo ba dan baya ya bawa Rabiu da Kabiru da ya mik'e jikinsa na balain rawa,da wani abu kamar kibiya ya nuna katon mudubin daya rufe bango daya na d'akin,take sai ga Saifullahi ya bayyana Yana ta safa da marwa a wani daki da wayar a hannun sa,

Shugaba ya cigaba da magana yana "Zan iya dakatar dashi zan iya saka wayarsa ta d'auke bazai Kira mahaifiyar matarsa ba,amma bazan yi ba dan Sam bai cancanci Zama a kungiyar nan ba har yanzu da sauran Imani a tare dashi,har yanzu Yana da birbishin tausayi a kirjinsa.

Kabiru a guje yaje ya kwanta a gaban shugaban ya rike kafarsa Yana "ka taimaka min kasa wayarsa ya d'auke na tuba bazaa Kara samun kuskure daga wajena ba duk abinda kaci nayi, zanyi idan har asirina zai rufu ka taimaka min Kar ya Kira bana so asirina ya tonu,inaso a mantar da Nusrah da Saifullahi inaso itama yayar matata a shafe komai a kanta nayi alkawari koma menene zanyi"

"Ka zama shaida zan bashi dama na karshe idan har ya sabawa umarnin mu baiyi duk abinda za'a Umarce shi da yayi ba duk abinda ya biyo baya shi ya jawowa kansa"

Kabiru da sauri ya fara gyada kansa Yana kallon Saifullahi ta mudubi da ya Kara wayar a kunnensa, hankali a tashe yace zai Kira ka taimaka min

Shugaban a hankali ya taka ya isa gaban mudubin,ya daki mudubin kad'an,sai ga wayar Saifullahi ta watse a kasa,

Kabiru da ya rik'e zuciyarsa ya hau sauke ajiyar zuciya
Da yaga Saifullahi ya sunkuya ya d'auko wayar ya hau daddanawa da alama wayar d'aukewa tayi.

Shugaba ya Kara nuna mudubin da kibiya sai ga Nusrah ta bayyana itama da wayarta a hannu Yana dan buga mudubin wayar ta itama ta Fadi kasa

Sai a lokacin ya juyo yana "anjima zanyi aikin da zan rufe musu baki bazasu tab'a iya fadawa kowa ba,a yanzu Kuma wayarsu ta tashi daga aiki kenan.
Chapter 67 · 0% Book details