← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 80

Sashe 33

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Asmau tace tana Kai hannu wajen fuskar Yesmeen ta ringa juya hannun Kamar zata tsone mata Ido Amma Yesmeen ko motsawa bata yi ba ta ringa kallon sama, likita ya mik'a wa Yaya Asmau takarda akan ga magungunan dai a siya mata.

Haka Yaya Asmau ta ruko hannun Yesmeen suka fito daga office din Suka nufi d'akin da aka kwantar da Sajeeda.

Suna Shiga suka ga Sajeeda a zaune duk da ruwa a jikinta kuka kawai take sharba Yaya Abu na masifar tayi shiru ita fa ba yarinya bace Mai haka zata cika asibitin da kuka,

Kabiru kuwa shiru kawai yayi dan tana farfadowa ta fara kuka.

Sajeeda kuwa Yesmeen data ga tana kallon sama hannun ta na lalube sun shigo d'akin yasa ta Kara rushewa da wani kukan tana "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha "Yaya Asmau mai likita yace ya samu idon yesmeen dan Allah karki ce min dagaske ne Yesmeen ta daina gani"

Yaya Asmau na k'ok'arin magana Yaya Abu ta Kara dakawa Sajeeda tsawa tana "Wai ke Mai hakane Sajeeda ke fa ba yarinya bace ke idan kina irin wanan kukan Mai kikeso ita Yesmeen din tayi"?

"Ki barni Yaya Abu dole nayi kuka dan tunda Abban Nusrah ya hadu da wanan abokin nasa ya shigo rayuwar mu da Sunan taimako nake ganin masifa kala kala,wlh rabona da kwanciyar hankali tun kafin Abban Nusrah ya had'u da abokin nan nasa,tunda kuwa suka hadu,daga wanan sai wanan,daga komawar mu gidan daya bamu Annur ya kurmance,nima kaina ba lafiya ce dani ba,Wai yanzu tashi daya Yesmeen ta wayi gari tace bata gani,sai nayi magana Abban Nusrah yace ba haka ba wlh bazan iya cigaba da zama a gidanan ba idan har Abban Nusrah bazai maida Masa dukiyar sa ba wlh gida Zan koma,ko shekara daya bamu yi ba masifar yau daban na gobe daban"

"Ikon Allah Sajeeda a hayyacin ki kike kuwa,Mai ya hada kurmancewar Annur da makancewar Yesmeen da abokin mijinki, Mai laifin Wanda ya taimakawa mijinki ya tsamo shi daga talauci dan ya dandana arziki kina nufin kin fi karfin Allah ya jarrabce ki"?

"Haka nake fama da ita Yaya Abu ban taba sanin Sajeeda makiyata bace sai yanzu,tunda ta bud'e ido taga Allah ya amsa adduata na samu mai taimaka min ta dorawa kanta masifa Bata tab'a zaton alheri kullum sai sharri da zargin abokina take,
ta dage bata hanyar halal abokina ke samun kudi ba, Bayan abokina Yana da balain kudi,shikenan duk wani Mai kudi ba ta hanyar halal yake neman kudinsa ba,yanzu sai ace dangote ma ba ta hanyar halal yake samun kudinsa ba,Sajeeda burinta taga na Kare rayuwata a talauci Ina yawo gida gida Ina gyara Allah ya kawo min wanan bawan Allah dan ya taimaka min Sajeeda tace ba haka ba tsabar masifa ko tuntub'e tayi sai tace tana zargin ba ta hanyar halal abokina ke samun kudi ba"

"Nasan mai nake cewa Abban Nusrah Kar idonka ya rufe da San kudi ka kasa gane abinda nake so na nuna maka,Mai ya kurmantar mun da yaro har gobe ba Wanda yasan dalili,yanzu ma Yesmeen ta makance bata gani,Kai Kuma kasan halin da nake ciki ban da mugayen mafarkai da nake fama dashi Abban Nusrah mai yasa tun a baya duk wanan masifun basu sameni ba sai yanzu?

"Saboda a yanzu Allah yaga damar jarrabtarki yau naga masifa a wajen yarinya nan,Sajeeda iya sanina Baa miki baki ba,idan Allah zai maka arziki haka kawai kake wayar gari kaga kayi kudi,?naga dole sai da sila silar arzikin Kabiru ta hannun abokin sa ne idan Zaki tsarkaka zuciyar ki ki kwantar da hankalin ki ki tsarkake zuciyar ki"

Ta kalli Asmau tana "Wai Mai likita yace ya samu idon nata ne"?

"Yace bai ga komai ba sau biyu ya duba idon yace ba abinda ya samu idon ta idan dai bata gani toh matsalar bata asibiti bace ba dan ko Ina zamu Kai ta a dubata zaa ga idonta kalau yake"

"Kinji ko Yaya Abu Wai Mai yasa bazaki fahimceni bane haka kawai Yesmeen zata daina gani ki duba lamarin nan"

Kabiru a fusace ya fara magana Yana "Yaya abu na gaji da halin Sajeeda ki Mata gargadi,Kar ta Kara danganta koma me ya faru da abokina Ni musulmi ne na yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka,kurmancewar Annur da Yesmeen daga Allah ne na karbi wanan jarrabta da hannu biyu idan bazata iya ba sai tasan nayi"

Daga haka Kabiru ya fice daga d'akin Yaya Abu ta hau bashi hakuri Yana fita ta rufe Sajeeda da fada tana "wlh bansan Baki da hankali ba sai yau wato kinfi san rayuwar talauci akan na arziki toh wlh ki gagauta cire wanan tunanin a ranki ki mori arziki mu mora Asmau kiji min masifa a wajen Sajeeda"

Sajeeda kuka kawai take dan ba Mai fahimtar ta dama tasan Yaya Abu bazata tab'a ganewa ba har gwara ma Yaya Asmau a yanzu ta fara ma zargin kabirun dole ta fara saka mishi ido,ya fara abubuwan da take dasa zargi akansa.

Yesmeen dake tsaye idonta a sama kawai take kallo ta kasa yarda Wai Yesmeen ta makance kenan Wanda hakan na nufin bazata sake gani ba,ta rushe da wani sabon kukan,Yaya Abu taja tsaki tana Jin kamar ta rufe Sajeedan da duka ita Kam da itace ko sata Kabirun ke yi ba abinda ya shafeta indai zai kawo Mata kudi.

Sajeeda kuwa kafin a sallame su daga asibitin sai da ta Kara ganin gynecologist ya duba ta duk test din da aka mata infection Mai k'arfi aka gano mata,da Dr ya rubuta mata magunguna masu shegen tsada akan ta ringa amfani dashi duk bayan sati biyu ta ringa dawowa asibiti ana dubata.

Har suka dawo gida zuciyarta a jagule take ita infection,Yesmeen makanta,Annur kurma abin ya mata yawa.
A yanzu makantar Yesmeen da tausayinta yafi nukurkusar zuciyarta gani take bata rike amanar da Nuratu ta bata ba.

Kabiru

Koda ya bar asibiti wajen Rabiu ya wuce cikin tsananin farinciki dan ya Masa albisihir din makantar Yesmeen dan dama tunda ba makancewar Allah da Annabi bane ba yadda za'ayi likita ya gano abinda ya makantar da ita.

A gidan Rabiu yaci abincin dare cikin farinciki Rabiu na kwadaita masa auren Yar shilla ya more rayuwar sa,neman Mata ma yakeso ya fara yi Amma abinda bai tab'a yi ba sai yaji ya kasa amsa tayin Rabiun.

Koda ya isa gida bai ko kalli d'akin Sajeeda ba Dan so yake ya nuna mata fushi yake yi da ita ko zata shiga hankalin ta dadin da yaji,Yaya Abu zata taimaka Masa wajen yi Mata magana dan yasan ita tana San abun duniya.

Sajeeda kuwa wani irin zazzabi da ciwon Kai ne ya saukar Mata saboda tsabar kukan da ta sha,da hannun ta ta bawa Yesmeen abinci tana kukan yadda za'ayi budurwa kamar Yesmeen ta makance lokaci daya,Koda ta tashi d'akin ta ta Kai Yesmeen dan ta kwanta dan gani take kulawarta kawai Yesmeen ke bukata,idan Kabiru ya dawo ga roke shi ya koma d'akin sa dan ko ta bar Yesmeen a d'akin ta ba lailai su Yaya Abu su iya kula da ita ba tsawa kawai zasu yi ta daka mata.

Koda suka kwanta da zazzabi da ciwon kan nata haka ta zubawa Yesmeen ido tana kuka.

Har karfe dayan dare bata ji alamar Kabiru zai shigo ba hakane yasa ta kulle k'ofar ta dan tasan dakinsa ya tafi.

Ta zauna a gefen Yesmeen ta gyara Mata rufin bargon hawaye na zubo mata tace "Ya Allah ka dubi marainiyar ka da idon Rahama ka bud'e Mata idonta ta ringa gani"

Yesmeen da rufe idonta kawai tayi ta bud'e idon ta a hankali dan ji tayi bazata iya jurewa ba,Kar jinin Sajeeda ya hau saboda damuwar makantar da tayi.

Sajeeda kuwa ta Dan ja baya da sauri data ga ita Yesmeen ke kallo ba sama ba.

Yesmeen ta mik'e a hankali idonta cikin na Sajeeda tana "Umma Ina gani"........

MG'S SKINCARE

Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4k

Mg's beauty kit 14k
Herbal whitening soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Glow oil

Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glow😍
Assalamu alaikum iyayen yara. Ko kuna da labarin shahararriyar mai saida kayan yara a garin Katsina wato BEEMYS_KIDS🤔 To tana nan tana saida kayan yara tun daga kan su riguna, wanduna, takalma, da duk wasu kayan kyale-kyali na yara da kuka sani daga sabuwar haihuwa (newborn) har matasan yara wato toddlers. Kayan ta akwai sauki dai-dai da yanayin rayuwa duba da yadda ta canja abun sai dai hamdala. Tana kawo kaya daga China, Turkey da Bangladesh. Ku hanzarta iyayen yara masu alfarma a dama daku wannan sallar kar ayi babu ku. Muna maraba da masu sayen daya ko sari duk a farashin da bazai gagari aljihu ba. Nagode🥰🥰🥰
https://wa.me/message/FMUET45HVY52N1
Chapter 33 · 0% Book details