← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 80

Sashe 61

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har fada sai da suka so suyi dashi akan zuwa d'auko Sajeeda sai babba yalwa ce ta mata magana akan ta bar zancen zuwa dauko Sajeeda tasan Kabiru na iya k'ok'arin sa wajen nema mata magani abinda zata yi kawai ta ringa yiwa Sajeeda Addu'a dan bakin uwa nada tasiri akan yayanta,da wanan shawarar ta zage wajen yiwa Sajeeda Addu'a ba dare ba rana,daga lokacin Kuma da ta fara Addu'a sai ta cigaba da ganin Sajeeda a mafarkin, Wanda tuni ta gano Sajeeda na tsananin bukatar taimakon ta dan ko da Rana ta kwanta sai tayi mafarki da ita, Babansu Sajeeda haka zai yi ta mata fada akan dan ta saka Sajeeda a ranta da yawa ne shi yasa take yawan mafarki da ita,a babu yadda Gwaggo za tayi ta hakura da zuwa dauko Sajeedan ta cigaba da mata Addu'a, azumi da sadaka kuwa cikin yin sa take,dan a yaranta Sajeeda itace mafi soyuwa a gareta ta rasa wane irin cuta ne ya d'auke mata magana ya shanye Mata jiki yake fito mata da ruwa ta gabanta,
musamman taje babban asibti ta tambayi likita ko da akwai kwaron da idan ya ciji mutum yake d'auke Masa magana har ya shanye masa jiki,ta lissafa Masa yadda jikin Sajeedan yake, likita yace gaskiya bai tab'a ji ba,sai dai idan wani cutar ne na daban zata iya kawo Sajeedan a dubata,Koda ta dawo daga asibitin haka ta baje tunani tana yi akan gaskiyar kwaron da Kabiru yace ya ciji Sajeeda gashi Sajeeda bata da bakin da zata Fadi abinda ya sameta,Bata San Mai yasa take Jin akwai wani boyayyen lamari game da rashin lafiyar Sajeeda ba,daga yadda take gurnani tana buga kanta da alamar akwai abinda take so ta fada mata amma bata da bakin yi Mata magana,mai ya samu Sajeeda haka?anya ba wani Abu mijinta ke b'oyewa ba shi yasa ya dage akan bai yarda su daukota ba, menene dalilinsa nakin yarda su taho da Sajeeda da ba wani Abu za ta iya Masa ba,a iya saninta akwai jinya da larurar da idan ya samu mutum dole sai an maida mutum gida an nema masa magani,yanzu idan fa ta rasa Sajeeda Kabiru wata zai samo ya shimfida sabon rayuwa da ita,Sajeeda fa ba mai maye mata gurbinta,har ace tana raye a matsayin ta na uwa amma yarta na Abuja a kwance a haka zata zauna watarana sai dai a Aiko mata da ta rasu,Abu da tasani bazata tab'a iya kula da Sajeeda ba,ta Kuma san saboda abin duniya Abu ke zaune a gidan, bazata zauna ta biyewa Babansu Sajeeda Taki dauko Sajeeda ba,a matsayin ta na uwa tasan da akwai matsala dole ta taimakawa Sajeeda dan bata da kowa sama da ita da mijinta idan mijinta yayi iya nashi k'ok'arin ya barta itama tayi nata k'ok'arin.

Da wanan shawarar da ta yanke ta Kara tunkurar Babansu Sajeeda da maganar zuwa d'auko Sajeeda inda a ranar babba yalwa na gidan,Babansu Sajeeda ya ringa fadan kullum sai sun yi waya da Kabiru yace Sajeeda tana samun sauki shi bai ga amfanin zuwan da Gwaggo za tayi ba, Gwaggo kuwa ta rushe da kuka akan sai taje sai dai duk abinda zai faru ya faru,

Babansu Sajeeda ya zuciyo ya hau fadan idan ita ke zaman kanta sai taje ya gani,babba yalwa ganin abin na Neman zame musu fada har Gwaggo na sai dai idan ya saketa ita dai sai taje ba zata zauna a Aiko mata da yarta ta rasu ba.

Babba yalwa tacewa Gwaggo abin ba sai ya kai ga haka ba abinda za'ayi bari a Kira Yaya Asmau taje ta dubo Sajeeda idan har jikinta ba sauki,da gaskiyar Gwaggo dole a dauko Sajeeda.

Da wanan shawarar aka nemo Yaya Asmau da itama take ta san zuwa duba Sajeedan dan tana ranta,ana fada mata ta amince akan zata je,ana sauran kwana biyu da zata taho Abujan.

Gwaggo ta bazama nemo magungunan gargajiya tunda take bata tab'a zuwa wajen wani mallami ba sai gashi tayi asubancin zuwa wajen wani shahararen mallami da ya kware a warkar da mutane masu laruran Aljannu da karya sihiri,haka Gwaggo ta hau zayyana masa larurar Sajeeda yace mata bazai iya ganewa ba sai an kawota ya ganta,ya ya tofa addu'oi a ruwan zamzam akan a Kai wa Sajeedan,kafin a bata a daura mata alwala idan ta Sha a shafe mata jikinta, abinda Kuma yafi a kawota ya ganta.

Gwaggo haka ta kaiwa Asmau ta mata bayani ta hada da rokon tana zuwa taga alamar Sajeeda jikinta ba sauki ta kirata a waya zata zo su taho da ita dan bazata iya ba.

Gwaggo har da kukanta ta d'auko kudi akan ta Kara na mota

Yaya Asmau taki karba kasancewar bata san gidan da suka koma a Abuja ba sai ta hau Kiran Kabirun dan ya kwatanta mata sai dai har ta karaci kiransa bai dauka ba,har Yaya Abu ma da ta kirata bata dauka ba,sai lambar Nusrah ta kira Nusrah ta Mata kwatance dan indai ta sauka a tasha duk wanda ta samu ta fadawa sunan unguwa da lambar gidan zai Kai ta har k'ofar gida.

Da asubar fari ta d'auko hanya bayan Gwaggo ta rakata har Tasha tana rokon ta tana isa gidan ta mata waya.

Koda ta iso bata Sha wahalar samun abun hawa ba tana fada Masa unguwar da lambar gidan yace ta hau su tafi.

Tafiyar mintuna Suka iso katafaren gidan,Yaya Asmau taki yarda gidan kabirun aka kawota dan gidan ya wuce tunaninta saboda haduwarsa sai da ta tambayi mai gadi ya tabbatar mata da gidan ne ta Shiga ciki.

Koda ta shiga haka ya ringa kwankwasa k'ofar palon da taga an rufe tafi minti goma a tsaye ganin baa bud'e ba yasa ta koma wajen mai gadi tana tambyarsa da Anya suna nan.

Yace mata ba kowa amma Kabiru na nan bai fita ba

Da haka ta sake komawa ta gwada tura k'ofar taji ta bud'u.

Tana Shiga ta fara Jin ihun Yesmeen tana "Abba ya saka kayansa a tsirara yake"

Cak ta tsaya tsakiyar palon ta hau kalle kalle dan ta gano d'akin da take jiyo muryar Yesmeen cikin ihu, tuni jikinta ya dauki rawa ta fara bin bango tana nufar d'akin da take jiyo muryar Yesmeen din,tuni taji kanta ya kwance ta kasa hada tunanin ta balle ta gane Mai ke faruwa kirjinta wani irin dokawa yake da taji Yesmeen na "Abba karka tabani Abba nifa yarka ce karka lalata min rayuwa Ummaaa kizo kiga Abba zai lalata min rayuwa"?

A bakin k'ofar ta tsaya jikinta na d'aukar wani irin rawa tana so ta tuna waye ma Abban da zai lalatawa Yesmeen rayuwa sam ta kasa kawo Kabiru ji tayi ta kasa ma motsawa saboda tana fargabar ta Shiga d'akin taga abinda yafi karfinta tuna Yesmeen ba gani take ba kila shi yasa wani azzalumin ke san rabata da mutuncinta,yasa ta yanke shiga d'akin duk da bata da tabbacin ko k'ofar a bud'e take, hannunta na karkarwa ta tura k'ofar a hankali ta zura kanta.

Ganin mutum a zigidir ya bata baya yasa taji wani irin mummunan faduwar gaba Kabiru na jiyowa ta zaro ido tayi baya da sauri tare da zubewa a kasa dan kafafunta wani irin rawa Suka dauka ta hau Jan "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Kabiru

Yaya Asmau da yaga ta shigo ta koma da sauri yasa yaji numfashinsa na neman d'aukewa hankali a balain tashe yayi wajen da gajeran wandonsa yake ya fara sakawa da sauri Yana "na Shiga uku asirina ya tonu"

Yesmeen kuwa hamdala kawai take tana Daga kwance bama tasan wacce ta shigo ba amma tasan yau asirin Kabiru ya tonu,ta mik'e tsaye cikin zafin nama ta fada bandaki ta kulle kanta.

Kabiru kuwa da jikinsa ke wani irin rawa ya fara tunanin yadda akayi Yaya Asmua ta shigo d'akin bayan ya kulle k'ofar, wani irin zufa ke keto Masa jikinsa na rawa yayi hanyar waje Yana tsoron Yaya Asmau taje ta tona Masa asiri,sai da yaje bakin kofa yaga Ashe murza mukulin yayi bai kullu ba,yaya Asmau har lokacin sallati take Tama kasa tashi fitowar Kabiru daga d'akin kamar zai fado kanta yasa ta fara ja da baya tana "Dama haka kake Kabiru marainiyar Allah zaka lalatawa rayuwa"

Girgiza Kai Kabiru ya fara yi Yana "Wallahi sharrin shaidan ne ban Kai ga tab'a ta ba ki rufamin asiri"

Yaya Asmau da ta
Samu ta mike dak'yar saboda rawar da jikinta keyi itama girgiza kanta ta fara yi tana "a yau Zan tafi da Sajeeda da Yesmeen Kabiru Kai dabba ne Yar cikinka zaka nema wallahi sai na tona maka asiri Ina Sajeeda take, Sajeedaaa"

Yaya Asmau ta hau kwallawa Sajeeda Kira

Kabiru hankali a tashe ya fara cewa "karki min haka Yaya Asmau ki rufamin asiri"

Gurnanin Sajeeda Yaya Asmau ta fara jiyowa daga sama da k'arfi

Yaya Asmau da jikinta ke rawa tayi wajen mattattakalar bene dan tasan Sajeeda ke wanan gurnani.

Tana Hawa taji an buga Mata Abu akai.....

Wallahi karfe Tara da rabi aka kawomin wayar da Zan bari sai gobe nace Bari dai na muku

ASSALAMUALAIKUM AUNTY ZEE MOM MUJAHID TAKUCE

INGATACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA DUK WANI ABINDA YA TOSHE MAKI HANYAR SADARWA SHIN NI IMA NE BAKIDA SHI ZAFI KIKEJI YAYIN MUAMALA
RASHIN NI IMA BAKI JIN SHA AWA NE? RIKICEWAR AL ADA ?FITAR FARIN RUWA MAI WARI BUDEWAR GABA TALEWA MALEWA KURAJEN CIKIN FARJI KURAJEN JIKI DAUKEWAR AL ADA RASHIN HAIHUWA
BANGAREN MAZA RASHIN KUZARI
KANKANCEWAR GABAN NAMIJI SAURIN KAWOWA RASHIN JIN SHA AWA JIN ZAFI YAYIN MU ALA DA MATANKA HMMM KEDAI KISHA KEDA MIJINKI ZAKITASHI MAN ALBARKA KODA YAUSHE KADA KIYI SANYA KICE KIN GWADA MAGUNGUNA KIYI HAKURI KI GWADA WANNAN KANKAT NE BI IZINILLAH

GAME DA MASU NEMAN HAIHUWA KIYI KOKARI KU GWADA ANGWADA ANDACE INA KATSINA INA AIKA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH KUDIN MAGANIN KO WANI GALLON 4K KUMA KEDA MIJINKI ANA SO KOWA YASHA GALLON DAN GIRMAN ALLAH IDAN BAKI SHIRYA BA KARKI BIYO NI YAN FLASHING KUYI HAKURI DAN ALLAH SAI NAJIKU DIN INKUN SHIRYA🤪KUKIRA KAI TSAYE 08162859027

ALBISHIRINKU 🥳🥳 ALBISHIRINKU 🥳🥳🥳🥳 MANYAN MATA
Takunce dai A&Z COLLECTION takara zuwa muku da kayanta masu sauki da inganganci👌👌

Muna da supplement nau,i kala kala
Chapter 61 · 0% Book details