← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 80

Sashe 6

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwancen da nake naji motsin bud'e k'ofar dakina hakane yasa na bud'e idona sai naga abokin Abban Nusrah ya shigo da Jan zani daure a kugun sa hannun sa rik'e da tukunyar kasa,sai na Mik'e da sauri cikin tsananin tsoro na fara kwallawa Abban Nusrah Kira akan ya tashi,dan ba iya abokin nasa ne ya shigo ba har da wasu a bayan sa suma da tukunyar kasa a hannun su,ihu nake iya karfina na kasa d'auke idona daga kansu na Kai hannu na dan na tashi Abban Nusrah sai na ji baya gefe na har suka zagaye gadon da na ke kwance na cigaba da ihu Abokin Abban Nusrah ya fusgoni da k'arfi ya Kai hannun sa wajen zani na, na saka ihu!"

A daidai lokacin da naji an rik'e ni ana girgiza ni na bud'e ido na da sauri tare da mik'ewa zaune kirjina na dukan uku uku a lokacin da na farka na ga ashe mafarki nake duk na jike da gumi,na Kankame Abban Nusrah da ya rik'e ni gam yana "lafiyarki kuwa"?

"Mafarki nayi Abban Nusrah innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Na cigaba da sallati Ina kallon k'ofar dakin mu dake rufe dan sai nake ganin kamar ba mafarki nake ba

"Kiyi Addu'a ki koma ki kwanta"

"Abban Nusrah mafarkin abokin ka nayi"

"Gwara da ki ka ce mafarki ba gaske ba ki koma bacci dan Allah"

Ya fara k'ok'arin cire ni daga jikin sa na Kara Kankame shi mu ka kwanta ahaka.

Mafarkin da nayi na nan daram a idona,ko kad'an ban runtsa ba dan gani nake ko Yaya na rufe ido zan ga sun shigo bansan Mai yasa nayi mafarki da abokin Abban Nusrah ba,Mai ma'anar wanan mafarkin da nayi.

Idona biyu har aka Kira sallah Asuba na tashi na daura alwala Abban Nusrah kuwa sai sakin munshari yake,a yanzu baya sallah akan lokaci sai nayi ta tashin sa kafin ya tafi massallaci.

Duk tashin da na masa bai tashi ba da na dame shi ma tsawa ya daka min hakane yasa na rabu dashi nayi Sallah ta ina ta mamakin canjin da nake gani a tare dashi,sai Kuma na tuna wai abokinsa yace zamu bar gidanan take naji wani irin tsoro da fargaba ya rufeni da na tuna mafarkin da nayi dashi,jikina na gaya min mutumin nan baa a banza zai taimake mu ba bansan mai yasa jinina bai d'auke shi ba ko dan na saka shi a raina shi ya sa nayi irin wanan mafarkin dashi.

Har na fito Muka hada abincin karyawa da Yesmeen zuciyata cike take da tunani har sai da Yesmeen tayi ta tambaya ta mai ke damuna nace mata ba komai.

Karfe tara da rabi su Saifullahi suka shigo dan su karya fuskar su a washe,Annur kuwa ya zauna a gefe na bayan duk sun gaisheni yace "Umma nifa yanzu kullum sai nayi mafarki Abba yayi kudi"

Da sauri na daga masa hannu Ina "ka ringa mana Addu'ar idan alheri ne kudin Allah ya tabbatar mana"

"Ai yama tabbatar in Sha Allah yaro babban ka ya zama Mai kudi,Umman ka ke so mu cigaba da zama a talauce ba cigaba"

Naji maganar Abban Nusrah a baya na na waiga Ina kallon sa a daidai lokacin da ya iso gefena ya zauna fuskar sa d'auke da murmushi Yana amsa gaisuwar da suke Masa.

Ya janyo faranti ya fara zuba dankali yana cigaba da magana "Saifullahi Kai da Faisal yanzu idan muka gama karyawa zamu je ku rakani gidan da abokina ya bar min kyauta nasan zaku ga kwana biyu na dan samu kudi,wani aminina ne tun muna primary Allah ya hada ni dashi Mai kudine sosai hakane yasa yace zai taimaka min yanzu haka jiya nida mahaifiyar ku mun je jiya ta masa godiya ba iya kyautar gida kawai yace zai min ba har aiki zai bani a companyn sa zaa ringa biyana miliyan daya duk wata"

Ihu Suka saka gabad'aya suka hau murna har da tsalle Yesmeen itama sai murna take

"Abba yanzu kana nufin sabon gida zamu koma Wanda yafi wanan"?

Saifullahi yace cikin tsananin murna da farinciki

"Sabon gida zamu koma ai zamuje kuga gidan daga nan ma sai muje ku masa godiya"

Murna kawai suke Yesmeen kuwa jiki na rawa ta d'auko wayarta ta Kira Nusrah ta hau labarta mata naji itama ta saki ihu ta cikin waya tana zata zo gidan.

Nidai da ido kawai na ringa bin su banji Ina murna ba na rasa dalili hakika cigaba ne yazo mana Wanda ban tab'a tunani ko mafarkin sa ba amma na rasa mai yasa naji a madadin naji ni cikin Farin ciki nake Jin akasin haka har ga Allah bana san mu bar gidanan abokin Abban Nusrah sam bai kwanta min ba Ina addua Allah yasa tarayyar su ya zame Mana alheri.

Yaran ko ta kaina basu Kara bi ba suka yi waje duuu dan Abban Nusrah ma cewa yayi duk suzo su tafi suga gidan.

Basu dawo gidan ba sai wajen laasar bakin su Kamar gonar auduga sai labarta mun kyaun gidan suke da haduwar sa ,suka d'auko Dubu hamsin suka bani akan abokin Abban su ne ya basu kyauta,sai fadar kirkin shi suke suna murna wai Abban su ya zama Mai kudi nidai ban iya ce komai ba sai dai sake sake a zuciya dan ban samu fuskar ma da zanyi wata magana ba.

Sai da muka zo kwanciya Naga na kasa jurewa dan Abban Nusrah cemin yayi a gobe goben nan zamu tashi mu bar gidan Kuma baza mu dau komai ba dan akwai komai a gidan

Duk da nasan magana ta zata b'ata masa rai haka na daure na fara magana Ina "Abban Nusrah daga haduwar ka da abokin nan naka ina ga ko sati ba'ayi ba har a cikin Yan kwanakin nan ya maka irin wanan alherin har dasu kyautar gida Abban Nusrah Kar idon mu ya rufe ya Kamata muyi bincike a kansa kafin mu koma gidan da ya bamu,ya Kamata mu tabbatar da irin sana'ar da yake yi saboda mu samu kwanciyar hankali wlh zuciyata bata dauki wanan abokin naka ba tsoro nake ji Kar ya zama bata hanyar halak yake samun kudin sa ba Abban Nusrah"

"Ya isa haka Sajeeda na fada miki Mai kudine Yana harkar Mai Kuma babban dan kasuwane bansan sau nawa kike so na fada Miki ba, ya za'ayi cigaba ya zo mana har gida ki tsaya kina wani kananan zance an gaya Miki banyi bincike akan sa ba Mai kudine na fada miki dan haka idan Zaki saki jikinki mu ci arziki toh idan bazaki saki ba wanan matsalar ki ce"

Yaja dogon tsaki ya kwanta tare da juya min baya

"Allah ya baka hakuri Abban Nusrah ai bansan kayi bincike akan sa ba Allah yasa mu koma gidan a saa"
"Ameen"

Kawai yace ya Kara Jan bargon saman kansa.

Wlh a ranar sai naji na kasa bacci kallon dakina dana kwashe shekaru a ciki kawai nake sau uku Abban Nusrah na farkawa ya leka fuskata idan yaga idona biyu sai ya koma ya kwanta yaja tsaki ana hud'u da ya leka fuskata muka hada ido sai ya Kara Jan tsaki Yana "Wai me kike yi baki yi bacci ba"?

"Bana Jin baccin ne Abban Nusrah Ina ta jimamin yadda zamu tashi mu bar gidanan Mai tarin tarihi"

Tsaki yaja Ya juya min baya ya hau magana kasa kasa ban ji Mai yake cewa ba.

Tun bai zama mai kudin ba ya canja hali Abban Nusrah ya zama wani iri sai na tsinci Kaina da Addu'ar ina ma abokin Abban Nusrah yace ya fasa ba mu gidan.

Ana Kiran sallah asuba na tashi nayi alwala duk tashin da na masa akan yayi sallah bai tashi ba har yanzu mamaki yake bani,dan Ina Jin karar bude gidan wanda nasan su Saifullahi ne suka tafi massallaci.

Koda na iddar barin dakin nayi dan wani zazzabi zazzabi naji Yana Neman rufeni na kwanta a dogon kujerar dake Palo.

Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani,Kamar dai mafarkin da nayi jiya haka na sake mafarki da abokin Abban Nusrah ihu kawai nake a mafarki dan Jana kawai ya ringayi Abban Nusrah na tsaye Yana kallona bai motsa ba girgizani da aka yi da k'arfi ana ummaa!!

Yasa na bud'e idona da sauri na Mik'e zaune Ina waige waige
"Umma lafiya kuwa"?

Yesmeen ta kara rikeni

Na dafe kirjina da hannu biyu Ina sallati a raina ya zaayi nayi mafarki iri daya sau biyu

Sai da na dan samu nutsuwa na mik'e na nufi dakina.

A zaune na tarar dashi a gefen gado na zauna a gefensa Ina "Abban Nusrah wlh yau na sake mafarki da abokin ka sau biyu kenan Ina mugun mafarki dashi Abban Nusrah bana jin mutumin nan akwai alheri a tare dashi dan Allah ka Kara bincike a kansa.

"Tunda kin ringa kin dasa mugun nufi a zuciyarki ai dole kiyi ta kananan mafarki ban taba ganin matar da take bakin ciki da ci gaban mijinta ba sai ke,wato kin fi so mu cigaba da zama a gidan haya kinfi so kiga na cigaba da yawo a machine da karfuna Ina bin mutane Ina musu gyara kinfi so yarana su cigaba da zuwa suna neman abu a wajen ki ni Kuma na cigaba da zama hoto,Sajeeda baki isa ba sabida wani banzan tunanin ki bazan k'i karbar arzikin da Allah ya nufa zan samu ba idan Kin ga ke ba za ki iya ba za ki iya cigaba da zama a gidan nan amma ni da yara na a yau za mu bar gidan nan ba fashi"

Ya fice daga d'akin a fusace.

A takaice Ina ji Ina ga ni muka bar gidan ba dan raina na so ba yara na kuwa murna kawai su ke.
Chapter 6 · 0% Book details