Sashe 19
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hamza kanin su Saifullahi ya fado d'akin Yana "Abba umma tana Kiran ka"
Kabiru wani irin kallo ya watsawa Yesmeen Ya kasa gane Kan Yesmeen daga yadda take rawar jiki da alama ta gane akwai abinda ya saka a fitilar d'akin ta ya Rasa wacce irin yarinya ce ita ya juyo zai fito daga dakin kenan Hamza ya Kai hannun sa wajen fitilar Yana "Aunty Yesmeen d'akin ki duhu"
A lokaci guda Kabiru da Yesmeen Suka isa wajensa,Yesmeen ta tunkuda hannunsa Kabiru cikin ihun tashin hankali yace 'karka kunna fitilar nan Hamza"
Saura kiris ya
ya sume saboda tashin hankali a gaban idon sa Hamza ke neman makancewa bayan Annur ya kurmance,cikin borin kunya ya dakawa Hamza tsawa Yana ya fita,Hamza ya fice daga dakin da gudu ,Kabiru bai yi wata wata ba yayi Kan Yesmeen ya rufe ta da mugun duka Yana "kin zame min masifa Yesmeen dole ki bar gidan nan kafin ki jawo min wani tashin hankali"
Dak'yar Yesmeen ta kwace daga bugun da yake mata tayi bandakin ta ta rufo k'ofar tana ihun kuka
Daga abinda ya faru ta Kara tabbatar da zargin da take yiwa Kabiru nasan cutar da ita tunda har ya gigice daya ga Hamza na neman kunna fitilar d'akin, anya zata zauna a gidanan Kabiru ya samu nassara a kanta, zaman ta ma a gidan bai zo yayi amfani ba tunda bai fasa cutar da Sajeeda da take k'ok'arin taga ta taimakawa ba,dole tasan nayi kafin Kabiru ya kai ga shigowa d'akin ta ya caka mata wuka haka taci kukan ta a bandaki ta daura alwala ta fito.
Kabiru kuwa yana fitowa daga d'akin Yesmeen yayi hanyar waje har lokacin kirjinsa bai bar bugawa ba da abinda ya so ya faru anya bazai ma cire abinda ya saka a fitilar d'akin Yesmeen ba Yana tsoro a cikin yayansa wani yaje ya kunna fitilar d'akin ya makance.
Jiki na rawa ya d'auko wayarsa daga Aljihu ya Nemo lambar Rabiu
Yana d'auka ya fara magana Yana "Rabiu na gaji da yarinya nan Rabiu yarinya nan ta zame min masifa ta riga da tasan sirrina kullum bibiye take dani,kasan jiya ma daddare Ina san nayi aikin da aka saka ni na karshe sai gashi tana buga k'ofa,ni nasan duk yadda akayi yarinya nan ta gani jiya, karfi da yaji tana neman hanani rawar gaban hantsi ,indai zan ganta da Sajeeda a waje daya sai nayi ta tsarguwa Ina Jin kamar zata fada Mata bansan Mai yasa shugaba yace ba yanzu ake bukatar jininta ba, wallahi ba ni da burin da ya wuce na kau da ita,kasan yanzu saura kiris dana ya Kunna fitilar d'akinta,duk wani abu da akace na mata sai ta tsallake,yarinya nan bana Jin ita kadai ce tasan akwai abinda na saka a fitilar d'akin ta dan k'in kunnawa tayi da yarona yaje kunna fitilar har da tunkude shi alamar tasan akwai wani abu Ina tsoron yarinya nan ta tona sirrina dole mu dau mataki"
"Toh yanzu ya kake so ayi"?
"So nake a b'atar da ita kawai tunda shugaba yace baza'a kasheta ba,kasheta zai zame min tashin hankali a b'atar da ita kawai na samu kwanciyar hankali.
Na samu kudin nan a yanzu ya Kamata na more wa rayuwata amma yarinya nan a gidanan bazan samu kwanciyar hankali da zan ci kudina cikin nutsuwa ba,tunda tasan sirrina ni ba kace akwai wayanda ke siyan mutane ba"?
Dariya Rabiu ya saka Yana "Siyar da ita zaka yi"
"Eee siyar da ita zanyi ko na basu ma kyauta bana kaunar ganin yarinya nan,a rayuwa ba wacce na tsana sama da ita, indai tana gidanan asirina zai yi saurin tonuwa,a halin da Sajeeda take ciki yanzu bana san na bata k'ofar da zata zargeni,shi yasa ban fito da kiyayyar yarinya nan fili ba,amma indai da yadda za'a batar min da ita dan Allah ka taimaka min na mori arzikin nan cikin kwanciyar hankali.
"Toh shikenan ka bari gobe idan mun hadu a kungiya duk sai ka fadawa shugaba abinda kake so ayi maka ba lailai sai da jinin Yesmeen zaka yi amfani nan gaba ba zaka iya nemo wani gwara a b'atar da ita tunda ta zame maka barazana"
"Dan Allah a taimaka min"
"Karka damu Abokina zaa san abinda za'ayi"
Kabiru sai a lokacin ya samu kwanciyar hankali suka dan tab'a hira suka yi sallama
Murmushi Kabiru kawai yake yana hararo yadda zai more rayuwarsa idan ya kau da Yesmeen.
Koda ya koma ciki d'akin yaran ya fara zuwa ya zuba musu warning akan Kar Wanda ya Kara Shiga d'akin yesmen duk Wanda ya Kara Shiga sai ya ci mutuncinsa dan yana tsoron wani a cikin su yayi gangancin da Hamza yaso yi yau dole ma gobe ya cire abin tunda Yesmeen ta san da abu a fiitlar.
Sajeeda
Har muka je asibitin muka dawo da lodin magungunan da aka bamu ban ji wani sauki a jikina ba,a yanzu ma kasana nake Jin Yana d'aukar dumi shi kadai tsawon rayuwata ban taba Jin haka ba bansan Mai ya jawo min haka ba,Ina ta so na tuna abinda ya jawo min wanan dumi da leman da nake fama dashi na kasa tunawa,na San dai ba daidai nake ba kafin Abban Nusrah ya samu nutsuwa dani,da Kuma ya samu nutsuwa dani naji jikina ya Kara canjawa bansani ba ko rashin lafiya ne ya jawo min haka.
Duk yadda naso na daure na dauki jikina kasawa nayi,haka na kwanta a daki, har Abban Nusrah ya shigo ya zauna a gefena ya ruko hannuna Yana tambaya ta jikina
Hawaye na zubo min na fada masa yadda nake Jin jikina duk da magangunan dana sha.
Cikin tausayawa ya hau min sannu ya kara b'allo min maganguna na sha ya zauna a gefena ya hau shafani Kamar wata yarinya,a ranar har daki ya d'auko abincina ya kawo min naci,inaso na fita na duba yarana amma bana san tashi dan sallah ma dak'yar nakeyi saboda Ina tsayawa Zan ji jiri na dibana.
Koda na tambaye shi Yesmeen tunda na dawo banga ta leko ba sai cemin yayi maganin mura ta sha ta Dade da bacci.
Shi ya ringa ja na da hira Yana ta bani labaran yadda yake samun kudi, Wai ana masa alheri a wajen aikin sa Yana tunanin ma zai fara gini A Abuja"
Ni dai Jin sa kawai nake dan ni kadai nasan me nake ji a jikina a yanzu ma kaikaiyi nake ji sama sama sai naji kamar abu ya zubo.
A haka na kwanta ni ba bacci ba ni ba Ido biyu ba,wajen uku dai bacci ya daukeni sai na hau mafarki
Abban Nusrah ya Kai mu wani gidan bene wai gidansa ne nazo shiga na fada wani Rami dake gaban gidan,sai na hau ihu Ina mikawa Abban Nusrah hannu akan ya taimaka min na fito,a madadin ya taimaka min sai ya hau watso min kasa.
Ihu nake da iya karfina amma ba mai jina sai da ya kusa gama rufeni da kasa na farka a gigice Ina sallati nabi na hada zufa,a hankali na kalli wajen da Abban Nusrah ke kwance naga baccin sa kawai yake har da munshari,a hankali na Kara tuno mafarkin da nayi Ina wane irin mafarki ne wanan
Jina da nayi a jike kamar wacce tayi fitsarin kwance yasa na Kai hannu na shafa wajen da nake kwancen naji a jike,cikin mamaki na fara k'ok'arin mik'ewa tsaye Dan kamar dai fitsarin nayi,yadda naga zanin jikina a jike.
Koda na cire zanin na Kai hannu jikina na shafa ruwan na Kai hancina dan na shinshina naji ko dai fitsarin nayi kasan zuciyata kuwa sallati kawai nake ko da na Kai hannu hancina wani irin wari naji nayi saurin cire hannuna hankalina a balain tashe "Wanan ruwan daga ina"?
Na tambayi kaina Ina cire wandon jikina gabad'aya na Kara Kai wandon hancina naji wani irin wari Kamar gurbatacen kwai ya daki hancina na wurgar da wandon jikina na d'aukar rawa mai ke Shirin faruwa dani haka?wane irin ruwa ne wanan yake fitowa a jikina.
Kuka na rushe dashi daya saka Abban Nusrah tashi a firgice Yana "Sajeedaa lafiya Mai ya faru"?
"Abban Nusrah na Shiga uku na lalace kaga ruwa mai doyi ke fita a jikina innalillahi wa Inna ilaihi rajiun
Na Kara rushewa da ihun kuka
Ya taso daga kwancen da yake ya zagayo wajen da nake tsaye Yana "wane irin ruwa Kuma Sajeeda"?
"Farkawa nayi daga bacci najini a jike,kaga wajen da na kwanta Abban Nusrah kaga zanina mai ke Shirin faruwa dani Abban Nusrah tunda jiya nake Jin wani iri a jikina Abban Nusrah,tun jiya da ka kusanceni ban Kara jina daidai ba"
"Bangane baki Kara jinki daidai ba Mai kike nufi?watakila infection ne dake ki kwantar da hankalin ki gobe da safe sai mu koma asibiti kije bandakin ki gyara jikinki"
"A Ina zan samo infection Abban Nusrah idan ba kai ne ka saka min infection ba a ina zan samo"
"Ta Ina Zan saka miki nima ki daina kukan nan kije bandaki ki gyara jikin ki gobe idan muka je asibiti sai muji Mai ya kawo Miki farin ruwan"
Kuka kawai nake da iya karfina
Gwara kowane rashin lafiya da wanan masifar dake neman Samuna,Taya ruwa zai ringa zubo min Mai wari, tunda nake a rayuwa ko discharge ban taba ba,amma dare daya na tashi ruwa na zubomin mai wari,nan ko maganin Mata indai na matsi ne bana amfani dashi saboda tsoro.
Idan har ba Abban Nusrah ne ya kwaso wani abun yazo ya saka min ba Kuma iya sanina ba maneman Mata bane sai dai idan Wanan tsinanne abokin nasa ne zai dora shi a hanya mara kyau.
Baccin da ban koma ba kenan na Shiga bandaki na wanke jikina da ruwan dumi da Dettol na samo sabon pant na saka,wanan tashin hankalin da na tsinci Kaina a ciki ya d'auke min tunanin mafarkin da nayi.
Sai da nayi Sallah Asuba bacci ya daukeni.
Yesmeen