← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 80

Sashe 13

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abban Nusrah Dubu dari naga fa kana miko min Abban Nusrah Ina kake samun kudi haka,a kasa da wata uku kayi irin wanan kudin"

"Sajeeda idan har bayanin da na Miki na samun kudina bai gamsar da ke ba kisa a ranki sata nakeyi tunda ke dama baki tab'a kyautata min zato ba kullum sai dai ki munana min,Ina ga ai na fada miki duk karshen wata zan ringa d'aukar al bashi miliyan daya toh jiya albashi nayi idan kin ga dama ki yarda idan baki ga dama ba karki yarda wanan matsalar ki ne daga yau karki sake min tambayar daga Ina nake samo kudina ni ba yaron ki bane da Zaki saka ni a gaba kina min tambayoyi kamar danki.

ke a rayuwar ki rayuwata ta baya ta kanikanci ne yake burgeki na dauko dari biyu ko dari da hamsin na baki, toh ni da wanan rayuwar da kike min fata har abada arziki da budi yanzu na fara gani,idan Zaki saki jiki ki mori niimar da Allah ya Mana toh,idan bazaki saki jiki ba wanan matsalar ki ce.

Daga haka ya mik'e tsaye ya fara kwalawa Yesmeen Kira

Da sauri Yesmeen dake daki ta fito har tana tuntube

Tana isowa ta zub'e akan gwiwarta kamar dai yadda ta saba cikin girmamawa.

Ya d'auko kudin ya mik'a mata

Yesmeen hannunta ta hau rawa tana zuba addua a zuciyarta dan yanzu duk abinda zai fito daga hannun Kabiru tasan ba na halak bane.

Daurewa tayi ta karba

Kabiru cikin hade rai ya fara magana Yana "Kije kasuwa ki Karo Mana kayan amfanin gida dan Naga alamar babar ki bata san zuwa"

"Kamar dame dame zaa siyo"?

Kabiru shiru yayi Kamar mai nazari sai can kuma ya karbi kudin Yana "jeki Sako hijabin ki sai muje kasuwar idan na gama Miki siyayyan sai ki kawo kayan gida ni na wuce wajen aiki"

Sai a lokacin Sajeeda tayi magana tana "Bance bazan je ba Abban Nusrah ka kawo na siyo kayan"

"Bazan bayar ba"

"Allah ya baka hakuri tunda kace da kan ka za ka siyo mai zai hana ka tafi da su Saifullahi Yesmeen Ina ga ko karyawa bata yi ba"

"Da ita Zan tafi idan zaki hana Kuma sai naji"

Sajeeda bata Kara cewa komai ba taja bakin ta tayi shiru.

Yesmeen kuwa ta mik'e hankalin ta a tashe tayi cikin d'akin ta tana zuwa ta zub'e a kasa ta daga hannu tana "Ya Allah ka kareni daga sharrin Abba Allah ka dubi marainiyar ka da idon Rahama kar ka bashi ikon cutar dani"

Ta mik'e ta saka hijabin ta tayi waje gabanta sai faduwa yake bata san Mai yasa take Jin fitar da zasu yi a tare Kabiru Yana da wani manufa a zuciyarsa.

Koda ta fito Kabiru har yayi waje Yana jiran ta.

Jiki a mace ta fita waje bayan Sajeeda ta Mata adduar dawowa lafiya

Tana zuwa ta haye machine din Kabiru dan har lokacin Kabiru bai siyi mota ba saboda gudun zargin mutane.

Sai da suka fara tafiya Kabiru ya fara magana yana "Ba kya Jin magana ko?sai kinyi abinda Zaki tona min asiri ko"?

Jiki na rawa Yesmeen ta hau grigiza kai tana "Ba abinda nace Abba wlh ba abinda nayi"

Kabiru girgiza kan sa yayi bai Kara magana ba dan Yesmeen ta zame Masa karfen kafa,Yesmeen na neman zame masa barazana ga cikar burin sa ya rasa yadda zai yi da ita kullum zuciyarsa cike take da fargaba duk da ya fesa Mata maganin mantuwa ko da ta gan shi amma sai yake jin kafin ya cimma burin sa zata iya aikata mishi komai.

Gashi bai fi saura kwana hudu ya samu cikar burin nasa ba ko a yanzu so yake ya tsoratar da ita yadda ko da mutuwa ma yayi bata Isa fallasa sirrin sa ba.

Bai zame da ita ko Ina ba sai gidan gonan Rabiu a bushen da yake Jin Zuciyarsa da tsanar da yayi wa yesmeen,ba dan gudun zargi ba tsaf zai shaketa ta mutu a binne ta.

Yana tsayar da machine din ya sauko.

Yesmeen da taji kirjinta kamar ya faso saboda tsoro dan ba kasuwan suka zo ba kamar ma daji ya kawota.

Tsawan daya daka mata yasa ta sauko daga machine din a gigice ta zub'e a kasa tare da fasa ihu tana ruko kafarsa a gigice tana "Abba na hada da girman Allah karka kasheni dan darajar da Allah yayi wa Annabi karka cutar dani"

"Rufe min baki kafin na yanka ki ni zaki Tarawa jama'a"

Da sauri Yesmeen ta rufe bakin ta jikinta na wani irin rawa

Kabiru ya fusgo hannun ta ya tura gate din Suka shige Yesmeen ta turje ta fara Neman ihu dan bilhakki da gaskiya zuciyar ta ta bata kasheta zai yi Kabiru kuwa ganin yadda take zunduma ihu yasa ya kwasheta da Marin da sai da ta ga taurari na gilma mata kafin ta dawo daidai.

Kabiru ya tsugunna a gabanta ya daga rigar sa sama ya d'auko wuka.

Yesmeen ta zaro ido.

Cikin wani irin murya kabiru yace "Yesmeen kin takura min kina min barazana kasheki Zan yi kawai na huta"

"Abba Dan Allah karka kasheni na rantse da Allah ban taba fadawa kowa ba,tunda ka min gargadi ban Kara leko ka ba"

"Karya kike yi na gano take taken ki so kike ki tona min asiri so kike ki fallasa sirrina"

"Wallahi Abba ba Wanda na gaya wa Kuma bazan tab'a fada wa kowa ba ka yarda dani"

"Wallahi Yesmeen duk ranar da na kamaki kin Shiga abinda bai shafe ki ba kinsan Allah sai kasheki dan duk duniya ba wacce na tsana sama dake a larura nake zaune dake ki nisance ni Yesmeen wanan shine gargadi na karshe da zan miki domin duk takun da kike Ina sane komai kike Yi Ina kallon ki"

"Ba Wanda zan fadawa Abba in Sha Allah na yarda ka kasheni idan har na fadawa kowa"

Kabiru ido ya zuba mata daya ga yadda jikinta ke rawa dan ba karamin tsorata tayi ba.

Mik'e wa yayi ya maida wukar ya daka mata tsawa akan ta tashi su tafi.

Da sauri ta fice waje ya bita ya tada machine suka tafi kasuwar dan dama Sajeeda yaso ta tafi kasuwar ya tsorota ta a gidan amma ta tsaya Masa tambayoyi Koda ya gama siyan duk abinda zai siya.

Sai da ya saka Yesmeen ta wanke fuskarta yaga ba Wanda zai gane tayi kuka ya loda kayan da ya siya mota ya biya kudin Yesmeen ta tafi gida.

Yesmeen sai da ta isa gidan hankalin ta ya dan kwanta bata tab'a tsorata kamar yadda Kabiru ya tsorata ta ba,Sajeeda kuwa sai tambayoyi take mata akan Mai ya sameta ta ganta a firgice haka.

Yesmeen tace ba komai gajiya kawai ta kwaso.

Saboda Kar Sajeeda ta zargi wani abu ta dan saki jikinta ta tayata ayyukan gidan taci abincin

Ana kiraye kirayen sallah magriba ta shige daki tacewa Sajeeda a gajiye take bacci take ji tana sallah zata kwanta.

Ko da ta shiga d'akin jakar makarantar ta ta d'auko ta d'auko paper da biro ta hau rubutawa Sajeeda wasika tana kuka,dan ta yanke a ranta guduwa zata yi bazata iya cigaba da zama a gidan da rabon da ta samu bacci mai kyau a gidan ba har ta manta,jininta da zaa auna zaa ga yayi mugun Hawa saboda fargabar da take fama dashi,kalar tsanar da take hango Kabiru na mata wata rana zai iya kashe ta din"

Kafin a Kai ga haka gwara ta tsira da ranta ta gudu ta bar gidan ta Shiga duniya bazaa rasa na Allah da zasu taimaka mata ba,dan bazata je wajen dangin mahaifiyar ta ko mahaifinta ba ballantana a Nemo ta.

Tana rubuta wasikar tana kuka har sai da ta gama ta ninke takardar ta kwanta lamo tana jiran dare yayi ta fice daga gidan.

A kwancen da take kuka kawai take tana tunanin Ina zata dosa ya Sajeeda zata ji idan ta ga wasikar.

Tana nan a kwance bacci ya fara k'ok'arin sace ta sai k'ok'ari take ta hana kanta baccin har sai da baccin ya saceta ta k'arfi.

Mafarki

Shigowar Sajeeda d'akin ta da Sunan ta da ta Kira yasa ta bud'e idonta.

Ganin Sajeeda a tsaye ta kura Mata ido hawaye na zubo Mata yasa ta mik'e zaune da sauri tana Umma

"Kar ki tafi ki barni Yesmeen,Mai na miki da Zaki tafi ki taimaka min karki tafi Yesmeen".........

2nd to the last free pages

Biya 500 ta wanan acct din 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko katin mtn ta wanan lambar 08033719070 sai a turo da shaidar biya ta layin nan 08033719070 ko wanan layin 08068484400

Mutanen Niger Kuma ku tuntubi wanan lambar
+227 96 82 89 84 karku yarda a Baku labari dan rufaffen sirri labarine mai Abubuwan ban mamaki da alajabi akwai Kuma darusa Mai yawa

MG'S SKINCARE

Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4k

Mg's beauty kit 14k
Herbal whitening soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Glow oil

Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glow😍

*RUFAFFEN SIRRI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Page 9*

"Yesmeen
Kar ki tafi ki barni Yesmeen"

Sajeeda ke ta maimaitawa a mafarkin ta har sai da ta tashi a firgice bakin ta d'auke da sallati.

Dan sai taga kamar a gaske ba mafarki ba.
Chapter 13 · 0% Book details