← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 80

Sashe 59

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaine dai ka shigo kake san kasheta Kabiru taya Zan kashe kanwata,Kai mai ya kawo ka d'akin ta a haka yanzu a halin da Sajeeda take ciki har zaka iya nemanta? innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu so kake ka karasata saboda ka samu kayi Aure,ai ba sai ka kasheta ba Kabiru zaka iya sakinta mu tattara mu bar maka gidan,har ace a halin da Sajeeda take ciki na a kwantar a tayar zaka iya nemanta toh ta Ina ma zaka nemeta a halin nan da take ciki idan ba kasheta kake so kayi ba"

Kabiru da ransa ya fara b'aci ya daka Mata wani irin tsawan wargaza masa shiri da take Shirin yi gashi duk alamomin rashin gaskiya ya bayyana a fuskarta shi ba yaro bane da zata raina Masa hankali danne pillon take so tayi a fuskar Sajeeda ya shigo

"Laifine dan nazo wajen matata ko da nemanta nayi haramune karki wani wayance Abu dan da zuciya daya muke zaune dake a gidanan ban taba kawowa zaki iya aikata haka ba,Kiri Kiri naga kina san danne kanta da pillo har mai kanwarki ta miki haka da kike so ki kasheta ?dama haka kike?yanzu da ban shigo ba kasheta zakiyi kenan Mai ta Miki"?

"Ni zaka yiwa sharri Wai taya Zan kashe Sajeeda gurnanin ta na jiyo Ina daga daki shine na shigo dan na dubata,ganin bata dora kanta a pillow ba yasa na daga kanta dan na dora Mata pillon sai naji an ja kafata ta kasan gado hakane yasa na saki pillon a kan fuskarta dan zaka ji ma nayi ihu lokacin da ka shigo wallahi ba kasheta na shigo nayi ba karka manta fa kanwata ce uwar mu daya uban mu daya akan me Zan kasheta"?

Sajeeda

Wani irin kuka ne ya kwace min da naga Abban Nusrah yayi shiru alamar karyar da ta tsara Masa yayi tasiri a zuciyarsa na fara girgiza kaina Ina nuna ta da hannu Ina "Mai na miki Yaya Abu da kike San kasheni?Mai na Miki da na cancanci haka daga wajenki?iya sanina ban taba miki komai ba,yanzu akan duniya kika zabi ki kasheni?mai na Miki kike so kiga kin rabani da numfashina"?

Duk cikin gurnani nake magana Ina nuna ta da hannuna da naga kabiru ya zubawa ido cikin mamaki Yana kallo da alama bai tab'a tunanin zan iya motsa hannuna ba kirjina ciwo kawai yake min Ina kallon makiyana guda biyu Abban Nusrah shi ma shigowa yayi dan ya nemeni ta baya dan a tub'e yake daga shi sai gajeran wando,mijina uban yayana shi ya jefani a halin nan haka bai ishe sa ba sai ya Kara nemana ta baya,ya karasani daya gefen Kuma yayata da muke uwa daya uba daya da ita,ita takeso ta kasheni wai dan ta aure shi,akan ta gan shi da kudin da bata San da ya ya same shi ba kuka kawai nake Ina cigaba da nuna Yaya Abu da hannu

Yaya Abu da hankalin ta ya Kara tashi da yadda taga Sajeeda na gurnani tana nunata da hannu ta matsa kusa da ita da sauri dan gani take tunda ta iya motsa hannunta kila ma bakinta ya budu tayi magana ta tona mata asiri

Ta ruko hannun Sajeeda tana "Ya Isa haka Sajeeda dole kiyi kuka saboda Kinga mijin ki na neman yimin sharri daga nazo na taimaka miki,amma ba komai tunda kora da hali yake min goben nan zan tattara na bar gidan kafin wani Abu ya Sameki ace nice ni nasan wani ne ya shigo dan ya cutar dake tunda na ji an rik'e min kafa ta kasan gadonki"

Fusge hannuna nayi daga rukon da tayi min Ina cigaba da gurnani, Abban Nusrah ya matso kusa da gadon ya ruko hannuna yana "Sajeeda Alhamdulillah kin fara iya motsa hannunki alamar kin fara samun sauki da kina da baki da kin fada min gaskiyar abinda Abu ta shigo yi miki dan daga yadda kike gurnani ni nasan bata da gaskiya bansan mai kika Mata take so ta kasheki ba"

"Wai ya zaka ce Ina so na kashe Sajeeda ne?akan me zan kasheta,ka fito kace ka gaji da zamana a gidanka ba sai ka hada damin sharri ba dan wani ne ya shigo yake san cutar da ita ka Kuma leka kasan gadon kagani dan wallahi an ja kafata bari na leka kagani"

Kabiru kallonta kawai yake a lokacin da ta fara k'ok'arin tsugunnawa dan ta leka kasan gadon.

Yesmeen hankalinta idan yayi Dubu sai da ya tashi da taji abinda Yaya Abu tace d'auke numfashinta tayi ta cire hannunta dake cikin ledar da ta nannade jikinta dashi a hankali,ta mik'a hannun Yaya Abu na lekawa ta kwasheta da mari, Yaya Abu ta saki ihu tayi waje da balain gudu.

Kabiru kuwa ya mik'e tsaye da sauri ya ja da baya Yana kallon kasan gadon dan yaji karar saukar Marin.

Tabbas da mutum a kasan gadon dan kamar motsi ma yake ji a kasan gadon.

Har lokacin ihu Abu ke tsallawa tana Aljanine a kasan gadon

Kabiru kuwa da shi ma jikinsa ya fara rawa ya fara neman abunda zai haska kasan gadon da kuma sandar da zai bugawa koma waye ganin bai ga komai a d'akin ba yasa yayi kasa da murya Yana "Sajeeda da gaskiya Abu akwai mutum a kasan gadon nan bari na dauko wayata na haska na d'auko sanda ta watakila barawone Ina zuwa"?

Yayi hanyar waje da sauri,Yesmeen kuwa ta fito daga kasan gadon da ledar a nannade a jikinta ta shige zif din Sajeeda cikin zafin nama tana hada wani irin gumi,k'yarma kawai take saboda tsoro.

Kabiru na fita ya ci Karo da yaya Abu da ta dafe kumatunta tana cigaba da ihun "ka leka kagani Kabiru wallahi akwai mutum ko aljan a kasan gadon,motsin da najiyo daga d'akina yasa ni fitowa dan na dubata wallahi ka leka kagani"

"Shhhh to ki bar ihu mana haka Ina zuwa"

Ya haye sama da sauri ba jimawa ya sauko da wayarsa da ya Kunna tocilan daya hannun sa rik'e da sandar labule yayi d'akin Sajeedan a hankali Yaya Abu da jinta bai dawo sosai ba tabi bayansa itama.

Nesa da gadon ya tsugunna ya hau haska gadon sai dai bai ga alamar komai ba.

Yaya Abu kuwa ta gwallo ido tana "baka ga komai ba"?

Kabiru bai kulata ba ya cigaba da haskawa ganin bai ga komai ba yasa ya mik'e tsaye ya ajiye wayarsa a gaban mudubi da sandar hannun sa ya nufi Kan gadon ya d'auki Sajeeda da har lokacin take kuka ya ajiyeta a Kan 2 Seater dake cikin d'akin ya daga katifar sama.

Yaya Abu dake bakin kofa ta saki ihu tana "Wallahi Aljanine ya rike min kafa ya taska min mari innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Kabiru kuwa shi kansa sai da kansa ya daure da mamaki dan tabbas yaji karar Marin da aka yiwa Yaya Abu ta kasan gadon ya Kuma ji motsi amma sai gashi ba kowa a kasan gadon.

Yadda yaga Yaya Abu na cigaba da ihu a tsorace har su Annur dake d'akin su sai da suka fito yasa yacewa Yaya abu "Dan Allah ki bar ihun nan haka Kinga dai ba kowa a kasan gadon kila Aljanine ya ga zaki yi ba daidai ba ya cafo kafarki ya waska Miki mari, daga yau Sajeeda bazata Kara kwana a d'akin nan ba sama zan maidata dan Kamar zamanta a d'akin nan hatsarine"

Daga haka ya saki gadon ya nufi wajen Sajeeda da ta zaro ido tana gurnani

Yaya Abu da ta mugun tsorota dan ta gama yarda Aljanine ya ja kafarta ya waska mata mari ta shige dakinta da sauri ta kulle ta zauna a gefen gado jikinta na wani irin rawa ta yarda yadda Nuratu ke da Aljannu Sajeeda ma na dashi,dan tunda ta kuduri niyyar kashe Sajeeda ta daina cin abincinta idan har ba Aljannun ta ne suka fada mata ta saka magani a abincin ba ba yadda za'ayi tak'i ci,yau da ta so amfani da pillo Kuma Aljanin ya ruko mata kafa, tsoronta ma kar Aljanin ya biyota daki ya kasheta tunda ya b'ace daga kasan gadon.

Wani irin zabura tayi ta nufi kofarta ta bude tana kalle kalle,har zata doshi d'akin Yesmeen ta fasa dan dakin Yesmeen ma ya mata nisa nasu Annur ne a gefenta.

Ta fada dakinsu da sauri ta rufo k'ofar duk suna zaune da Alama basu koma bacci ba ta haye gadonsu ta kudunduna ta rufe idonta,tabbas Sajeeda nada Aljannu babu tantama da alama burin da taci na auren Kabiru ba zai tab'a yuwa ba dan dak'yar Aljannun ta su barta ta zauna lafiya idan ta ma samu nassarar kashe Sajeedan yanzu ma sajeedar tsoron ta take ji,a kwancen da take ta tafi tunanin suna Yara lokacin da ta addabi Nuratu mahaifiyar Yesmeen da Sajeeda,ranar da ta Zo ta hada musu sharri a kan su suka cinye abincin Babansu mahaifiyar su ta zane su,a ranar Nuratu Aljanunta suka tashi ta shaketa da bango har gobe da tabon a wuyanta shi yasa Sam basa shiri da Nuratu har kowa ya Kama gabansa har Kuma suka manyanta bata manta shakar ba dan farcenta ta soka mata a wuya,kila irinsa ne da Sajeeda, tsoro ne ya Kara rufeta,ta cije lebbenta tana hararo Asarar da zatayi na rasa arzikin da ta ciwa buri,tuna yadda taga Kabiru dazu da yaje d'akin Sajeeda ya saka ta mik'ewa zaune,mamakin yadda Kabiru zai nemi Sajeeda da gabanta ke fidda ruwa kawai take,da yanzu bata je d'akin ba haka zai nemi Sajeeda kila shi ma ya kwaso cutar yazo ya zuba mata idan da ta samu nassarar kau da Sajeedar, tuni taji tsigar jikinta na tashi har yawu na taruwa a bakinta dole Kabiru yaso Kara Aure,idan har shaawa na iya sawa ya nemi Sajeeda da Babu abin mora a jikinta,haka tayi ta juye juye tana tunanin kila ma Yana can Yana neman Sajeeda tunda ya haye da ita sama,zata san yadda zata yagi rabonta kawai amma bazata tab'a iya auren Kabiru ba Koda Sajeeda ta mutu sai dai idan roba zai ringa sawa.
Chapter 59 · 0% Book details