← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 80

Sashe 52

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nifa Banga kiranki a wayata ba akan me zan ki d'aukar wayarki"?

Gwaggo na k'ok'arin magana Yesmeen ta fito daga d'akinta cikin lalube kanta a sama tana "Gwaggo kece kika zo"?

Murmushin Gwaggo ta saki zuciyarta fal da tausayin Yesmeen da ke matashiyar budurwa amma kaddara rashin gani ya fada mata,ta karasa wajen Yesmeen dake laluben iska,ta tarota tana "Nice Yesmeen yanzu nan nazo"

Baba yalwa kuwa sallati ta saki dan dama tana da labarin makantar Yesmeen ganin tana laluben yasa ta saki sallati tana "dama da gaske ne yarinya nan bata gani innalillah wa Inna ilaihi rajiun wai Mai ya jawo Mata rashin ganin"?

"Allah masani baba Allah shi ya barwa kansa sani,Sajeeda dai taga jarrabawa sai dai muyi addua Allah ya bata ikon cinye wanan jarrabawa dan autan ta ma baya magana dare daya aka wayi gari baya magana,ita Kuma Yesmeen ta daina gani, Sajeeda Kuma bansan wane irin cuta ke damunta ba ance kwaro ne ya cijeta sai kin ma ganta,wai tana Ina ne?

Yaya Abu dake Jin kamar tayi bindiga dan bacin rai,da hannu ta nuno d'akin Sajeeda tana ga d'akin ta can yanzu ma zan shiga wajenta ne na bata abincin karyawa kuka shigo bari na zubo muku abincin"

Daga haka ta koma kitchen din da sauri,ta zubar da shayin da ta hadawa Sajeeda cikin zink zuwan Gwaggo ya matukar b'ata mata rai da yanzu ta samu ta bawa Sajeeda shayin nan,ko mai itama babba yalwar tazo nema oho.

Taja siririn tsaki,ta fara hada wani shayin tana Addu'a Allah yasa a yau zasu juya ko gobe kafin su tafi ya zama dole ta dage wajen kula da Sajeeda har dasu Gwaggo ta hadawa shayi ta jera a faranti ta fito tayi d'akin Sajeedan.

Sajeeda

Duk maganar da suke Ina jiyo su daga daki,Allah Allah nake na ga mahaifiyata sai motsa bakina nake naga ko zan iya magana sai dai duk a banza na kasa magana,bazan so mahaifiyata tazo ta tafi batare da na fada mata halin da nake ciki ba,bansan taya Zan sanar da Yesmeen ta fadawa Gwaggo halin da muke ciki ba,da zan samu da Yesmeen ta nunawa Gwaggo tana gani,da zan samu da Yesmeen ta fadawa Gwaggo duk abinda ke faruwa,nasan ko ban iya magana ba Gwaggo tafiya zata yi dani, suna shigowa na fara hawaye ganin babba yalwa a bayanta yasa naji wani irin farinciki,ba damar magana bansan yadda zan nuna musu jin dadin ganin su ba,sai na fara buga kaina da bango Ina gurnani hawaye na zubo min.

Gwaggo ta saki hannun Yesmeen dan har da ita suka shigo ta iso wajena da sauri ta rikeni,tana "Sajeeda zaki jiwa kanki ciwo ki bari wani abu kike so a yi Miki?wajen ma da kike kwance a jike yake"

Ni kuwa kallon yesmeen da kanta ke sama kawai nake Ina gurnani,Wanda ni magana nake akan ta fadawa Gwaggo abinda ke faruwa,duk gurnanin da nake Yesmeen Taki sauko da kanta,mai yasa Yesmeen itama zata min haka,Yaya Abu dai bata d'akin ballantana nace shi yasa taki nuna musu tana gani,haka nayita hawaye da Ina iya motsa hannuna ne ma da sai na nuno Yesmeen din kila Gwaggo ta gano magana nake so da ita.

Babba yalwa sallati kawai take a lokacin da tayi tozali dani, tama kasa karrasawa wajen da nake kwance sai cewa take "Hauwa dama haka Sajeedan ta dawo innalillahi wa Inna ilaihi rajiun wane irin cuta ne wanan taya zaa barta a gida baa je an nema Mata maganin gargajiya ba?ai bana Jin wanan larurar tata ta asibiti ce?yanzu kenan ko tashi bata iya yi sai dai tayi Kashi ko fitsari a kwance"?

"Haka ta dawo babba shi yasa na kasa samun kwanciyar hankali wanan ruwan da kike gani daga gabanta yake fitowa mai wari ba fitsari tayi a kwance ba ban taba ganin larura irin na Sajeeda ba shi yasa nacewa mijinta ya bari mu gwada maganin gargajiya yak'i"

Ido babba yalwa ta zaro sai a lokacin ta matso kusa da wajen da nake kwance tana

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu a jikin Sajeeda warin nan ke fitowa? Hauwa har kika barta tun lokacin da kika zo baki tafi da ita ba
Aikuwa dole mu tafi da ita aje a jarraba maganin hausa bana Jin ma larurarta na asibiti ne,"

Abinda nagani kenan mijinta ya hana

"Aikuwa dole ya bari mu tafi da ita sannu Sajeeda Allah ya tashi kafadunki ya baki lafiya"

Murmushi kawai nake Ina godewa Allah a zuciyata da ya aikomin da su a daidai lokacin da rayuwata take cikin hatsari yayata take Neman rabani da numfashina"

"Ina shi kabirun yake ne dan gwara yazo indai ya bamu izini a yanzu zamu juya mu tafi"

Cewar Gwaggo babba yalwa na k'ok'arin magana Yaya Abu ta shigo d'akin da farantin abinci,so nake kawai su Gwaggo su gane so take ta kasheni,hakane yasa na fara gurnani Ina buga kaina da bango

Gwaggo ta rikeni tana "Sajeeda ai sai ki jiwa kanki ciwo wani Abu kike so"?

Gurnani na cigaba da yi

Yaya Abu ta ajiye farantin abinci tana "haka take yi idan taga abinci ko tana san wani abun ku muje daga d'akina ku ci abincin kafin ku gama na gama bata abinci na kintsa ta"

Ina Jin Mai tace na fara buga kaina Ina gurnani nasan so take su Gwaggo su bata waje ta kasheni,sai Gwaggo ta girgiza kanta ta hau share hawayen da take ta hanasu zubowa saboda tausayina tana "Bazan iya cin komai ba sai dai ki Kai babba taci abincin ki kawo abincin na bawa Sajeedan"

"Kuje kuci abincin nan Gwaggo rashin cin abinci zai saka Sajeeda ta samu lafiya ne ku tafi daki kafin mijinta ya sauko bai dace ma ya sauko yazo ya sameku anan ba,haba Gwaggo"

Gwaggo na k'ok'arin magana babba yalwa ta daga Mata hannu tana "Muje daga d'akin kafin mijin nata ya sauko"

Babba yalwa tayi hanyar waje Gwaggo ta bita a baya duk da gurnani da nake dan Kar su fita su barni da ita.

Suna fita ta kalli Yesmeen dake tsaye tana "uwarki kika tsaya yi bazaki fita ki bani waje ba shegiya ai wallahi sai su Gwaggo sun tafi dake"

Yesmeen lalubar hanyar tayi tafita waje dan tasan Sajeeda bazata tab'a yarda taci abincin hannun Yaya Abu ba,ba karamin dadi taji da ganin su Gwaggo fadar Kuma zasu tafi da Sajeeda ya mutukar faranta mata,dan da haka zasu samu su gudu,dan itama bin su zata yi Wanan karyar makantar ma ya dameta,ta fara gajiya makarantar da bata zuwa duk yafi daga mata hankali.

Sajeeda

Duk yadda Yaya Abu taso na Sha shayin k'in Sha nayi,dankalin ma naki ci,dan nasan idonta ya rufe da san ta kasheni,ganin su Gwaggo bazai saka ta fasa ba.

Tsaki tayi ta dire kofin shayin ta hau masifa akan Kar na Sha din kwana biyu bata San iskanci da na tsiro dashi ba, haka ta jani a kasa ta kaini bandaki ta kwakwara min ruwan sanyi tunda na fara larurar nan ko Yaya ruwan sanyi ya taba jikina haka Zan ta Jin kaikaiyi Ina gurnani dan ba hannun da zan sosa jikina Kamar zan zauce haka nake ji dan ko bacci bana yi Kuma Yaya Abu tasan da haka,amma haka ta kwara min ruwan sanyi ta kwara min a gabana ta cire zanin gadon ta shimfida wani kayana ma duk sun min yawa haka ta d'auko wani doguwar Riga ta saka min,sai yatsuna fuska take tana magana kasa kasa dan duk abinan da take yi saboda su Gwaggo ne ni kuwa kuka kawai nake Ina cije lebbena dan wani irin azababen kaikaiyi nake ji a ko'ina na jikina gashi ba damar susa.

Tana gama fesa Air freshner tayi waje.

Tana fita da minti goma na fara Jin maganar ita da Abban Nusrah a palo bayan ta gaishe shi ta sanar Masa da zuwan su Gwaggo

Sai naji yace "Su Gwaggo Kuma da sassafen nan"

"Eee wai Sajeeda suka zo dubawa Gwaggo duk tabi ta dagawa kanta hankali'

"Jiya fa munyi waya da ita nace mata kar ta damu dan yanzu ma na gano wani likita da yace min akwai wani acan kasar waje idan har aka kaita zaa samu magani a wajen sa,yanzu Shirin da nayi na zuwa wajen likitar ne ai da Gwaggo ta daina dagawa kanta hankali' bari na duba Sajeeda sai na je mu gaisa da Gwaggon"

Turo k'ofar d'akina yayi na zuba Masa ido,kudin haram ya zauna wa Abban Nusrah yayi wani irin kib'a Kamar bashi ba, murmushi ya sakar min ya zauna a gefen gadon yana "Sannu Sajeeda ya jikin naki"?
Kiga Gwaggo da Dora wa kanta wahala da sassafe nan tazo nafa ce mata Kar ta damu Zaki samu sauki dan an samo likitan da ya San Kan larurarki kasar waje zan Kai ki,kinsan Sajeeda ba abinda bazan miki dan na faranta Miki Rai ba,bari naje wajen su Gwaggo mu gaisa sai na dawo akwai maganar da zan miki"

Daga haka ya mik'e yayi waje na bishi da ido Ina mamakin halinsa duk abinan fa ya d'auka bansan komai ba rashin maganar nan nawa na matukar damuna, istigari na fara yi a zuciyata dan zuciyata a kuntace take nasan Ina fara istigifari zan ji sanyi a zuciyata, nasan yanzu da wuya ya iya hana Gwaggo tafiya dani, ko yak'i yarda babba yalwa ba bari zatayi ba da kunya ya kalli kakata yace bazai barsu. Su tafi dani ba.

Gwaggo

Sai da ta fito daga d'akin Sajeedan hankalinta ya dawo jikinta ta fara karewa gidan kallo,jiki a mace suka karasa d'akin da Yaya Abu take Kamar tunanin da takeyi irinsa baba yalwa keyi dan suna Shiga d'akin babba yalwa tace "Wai wane irin aiki mijin Sajeeda ya samu haka yayi irin wanan kudin"?ba Sanaar gyare gyare yake bane"?

"Babba nima kaina ya kulle bansan ya akayi Kabiru yayi kudi lokaci daya haka ba Kinga katon gidan daya Gina wancan shekarar ma ai bashi da komai"

Babba yalwa bata kara magana ba zuciyarta ya hau mata sake sake Kamar yadda na Gwaggo ke mata.
Chapter 52 · 0% Book details