← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 80

Sashe 40

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya fara magana wani irin Abu naji ya tsaya min a zuciya,wutar kiyayarsa ruruwa kawai yake a raina ji nake kamar na samo wuka nayi ta yanyanka shi yanzu alwashin da nake Sha ma bazai ci kudin nan ba yadda yake san yaga ya kasheni sai dai mu tafi tare bana Masa fatan Rahamar Allah daga Rana irin ta yau har zuwa karshen numfashina addu'oi masifa da balai Zan ta Masa,tunda har dani zai yi kudi,ba abinda zai hana naso ganin bayan sa.

Ganin Yana k'ok'arin barin palon Yana ta sheka rantsuwa yasa na fara magana cikin bacin rai Ina Jin ruwanan na zubo min Mai doyi

"Wallahi ba inda zata je Abban Nusrah idan har ka dage ka gaji da rukonta sai ka sallameni nima na tafi,haka kawai ba abinda ta maka zaka koreta,baka tashi korarta ba sai da ta daina gani,mai zaka cewa mahaifinta ya makantar Mata da ido,a haka na d'auko ta,har yanzu baka ji a jikinka mutane zasu fara zargin akwai wani abu dake faruwa a gidan ka ba kasa da wata biyar ka Zama hamshakin mai kudi,Dan cikin ka ya kurmance yanzu itama Yesmeen ta makance kila nan gaba ma mutuwa za'ayi,duk wani abu na faruwa da dalili banda na gidanan,Koda kaddara Allah ya Aiko akan ce ga dalili kafin aukuwar kaddarar amma na gidanmu daban ne Annur daga kwanciya bacci ya tashi ya daina magana Yesmeen daga kunna fitila ta daina gani,sai nayi magana ace ba haka ba idan har ka shirya korar Yesmeen ka dawo mata da ganin ta sai ta bar gidanan"

"Yaya Abu Kinga yadda ta juya zancen nan ko,banda Sajeeda bata da ilimi bata san yadda Allah ke juye lamarin sa dare daya ba,a cikin awa daya idan Allah ya so azurta bawan sa a yanzu Allah zaiyi silar da zai yi arziki,yanzu Mai ya hada kurmancewar Annur da makancewar Yesmeen da arzikin da Allah yamin yanzu ace matata ke min wanan zargin idan wani taji yana so ya zargeni ita ba mai hanawa bane,wanan wane irin abu ne,yanzu ba abin zargi a wajen ki sai ni kenan Shekara ashirin da uku muna tare ace baki san halina ba?baki San abinda zan yi da Wanda bazan iya ba mai kike nufi duk da kalmomin nan da kikayi da mutane zasu fara zargina"?

Kallona kawai yake Yana hucci cikin bacin rai

Yaya Abu kuwa ta fara bashi hakuri tana "Hakuri zaka yi Kabiru Sajeeda halin ta sai ita na rasa wacce iri ce ita idan har dan ance zaa Mai da Yesmeen take wanan maganganun sai kayi hakuri ka barta kana kallo ma ni da nake yayarta yadda ta hayyaya ko min kamar zata kawo min duka,yanzu da mutane na nan kaga sai su dauka ni muguwa ce Allah dai ya kyauta

"Kuna dai kallon irin abinda take min toh wallahi na fara gajiya Sajeeda bata San darajar miji ba duk maganar daya fito a bakin ta fadamin kawai take ni kuwa na gaji bazan dauka ba"

"Ya bazaka gaji dani ba tunda ka Gama Dani ya bazaka gaji ba tunda kayi kudi dani,ai a yanzu bani da wani amfani a wajen ka tunda har ka sadu da kare kazo ka sadu dani,bani da abin mora yanzu dole ka gaji dani"

Abinda naso Fadi kenan sai na juye da

"Tunda bansan darajar miji ba ya zaayi kenan"?

Na jefa masa tambayar Ina ciza lebbena dan takaicin maganar daya fito a bakina

"Aure zan Kara Sajeeda idan na Kara Aure watakila ki shiga hankalin ki"

Daga haka ya juya a fusace yayi d'akin sa na bi shi da kallo hawaye na zuraro min inama Yesmeen ta fadamin da wuri kafin Kabiru ya cutar dani,dama sai da na ayyana haka a raina kila ya zabi yayi kudi dani ne Saboda ya kau dani yayi aurensa yaji dadin rayuwarsa,ni Dana Sha wahala dashi a madadin ma idan gajiya yayi dani ya sauwake min cikin ruwan sanyi na tafi da lafiya ta shine ya zabi ya cutar dani,yadda nake Jin kasana nasan Abu ne mawuyaci na dawo yadda nake,duk a tunaninsa bansan sirrinsa ba,yau ban da Ina tsoron jefa Yesmeen a cikin masifa da a yau Kabiru ya gane kuransa dan sai na Tara Masa jama'a,Amma a yanzu nasan mai Zan yi Dan idan har na bar maganar a cikina zuciyata na iya fashewa dan bakin ciki.

A haka naja kafata na shige daki Ina jiyo muryar Yaya Abu na idan bana so ayimin kishiyar sai na Shiga hankalina da itace a d'aular da nake ciki da an sha mamaki dama idan Dadi yayi wa mutum yawa sai yace Dadi kasheni.

Ban juya ma na kalleta ba har shige d'akina Nusrah ta biyoni bana Jin zan iya Mata wani magana yanzu dan Ni kadai nasan mai nake ji ga ciwon zuciya ga na jiki.

Haka ta karaci zamanta ta gama koke kokenta akan makancewar Yesmeen tayi kasa da murya akan na taimaka na fada mata abinda nace Zan fada mata dan idan ta koma gida ba lailai ta samu nutsuwa ba haka za tayi ta tunani

Ce mata nayi Kar ta damu zamu yi waya ba wani abu bane,bana jin a yadda na ganta a cikin damuwa akwai abinda zan iya gaya Mata haka ta zauna a d'akin tayi ta zuba min Sannu kafin ta tafi gidan ta ma sai da ta Mana abincin dare sai tausayina take tana yanzu wa zai na tayani aikace aikacen gidan tunda Yesmeen bata gani,

Murmushi kawai na Mata nace kar ta damu su Saifullahi zasu ringa tayani tunda duk sun iya ji nake kamar na fada mata Yesmeen na gani yadda naga ta damu sai Kuma na fasa Ina tunanin mata magana ko ta waya ne ya zama dole na tashi tsaye na nemi mai taimaka min da Addu'a na kubuta daga hannun wanan azzalumin mutumin.

Yesmeen

Tunda Yaya Abu ta d'auko ta daga d'akin Sajeeda taji gabad'aya ta kasa samun nutsuwa,tayi nadamar tona sirrin ga Sajeeda yafi a kirga, dan tasan ba lailai ta iya dannewa ba zata iya tarar Kabiru da maganar.

Kuka kawai take tana tunanin abin da ya Kamata tayi,idan har Sajeeda ta tari Kabiru da zancen yasan itace ta fada mata,dole ta gudu kafin ya dawo gidan,dan tasan Sajeeda tace bazata fada masa bane kawai saboda ta zauna.

Da wanan tunanin ta fara tunanin yadda zata gudu batare da kowa ya ganta ba.

Tana kwance Yaya Asmau ta shige bandaki

Yaya Abu Kuma ta tashi tana bari taje kitchen ta d'auko Madara.

Tana ganin ta fita daga d'akin ta mik'e da sauri ta fice daga d'akin da gudu ta bar gidan Koda ta fara tafiya haka zuciyarta tayi ta Mata sake sake tana tunanin Anya gudun ta shine mafita a gareta,?Anya idan ta gudu bata tonawa kanta asiri asan tana gani ba?

Watakila Sajeeda zata iya daurewa taki fada Masa,tana nan awani lungu taga wucewar Nusrah a Napep,ba jimawa ta ga shi ma kabirun ya dawo a mota,tuni tunanin ta ya bata akan gudun kamar tonawa kanta Asiri zatayi hakane yasa ta fara tunanin hanyar da zata bi ta koma gida da bazasu zargi komai ba,tana nan tana sake sake ta hango fitowar su Saifullahi suna dube dube kafin su juyo wajen da take tsaye sai ta fara bin bango tana kallon sama,har Suka karaso wajenta.

Daga maganganun da da Sajeeda tayi da suka dawo tasan bazata fada ba, sai a lokacin ta dan samu nutsuwa sai dai har ga Allah taso Sajeeda ta yarda a maida ta wajen dangin mahaifin ta dan kullum cikin fargaba da zulumi take,yanzu haka zatayi ta tunanin kila ya gano ta tona masa asiri.

Kabiru

Koda ya Shiga daki ji yayi hankalin sa ya tashi da maganganun Sajeeda sai yake ganin kamar k'ok'ari take ta gano sirrin sa,so kawai yake dare yayi karfe daya ya kirawo shugaban nasu ko a yanzu kasa hakuri yayi sai da ya Kira Rabiu duk ya bashi labarin abinda ke faruwa.

Sai daya gama bashi ya kyalkyale da dariya Yana "Wai wanan yarinya da take daga ma hankali haka nawa take Mai zai Hana ka kau da ita kawai ka huta,idan ba Aljanna bace ita taya zata gane wani Abu da har zata maka karyar makanta, abokina idan har kasan yarinya nan ta zame maka kaya a wuya ka kau da ita kawai ka huta"?

"Taya Zan kau da ita batare da an Zargeni ba ni fa yanzu tsoron Sajeeda nake wallahi yadda take magana Kamar tasan wani Abu"

"Ba dai Yesmeen din yanzu ta nuna bata gani ba,ba sai ka jira shugaba ba da kanka zaka gano tana gani ko bata gani.

"Tayaya Zan gano kasan Allah idan har yarinya nan karya tamin bata gani wallahi wallahi sai na kasheta"?

Rabiu dariya ya saka ya hau fada Masa abinda zaiyi da zai gano Yesmeen ko bata gani.

Da wanan tunanin Kabiru ya samu kwanciyar hankali sosai yaji dadin shawarar da Rabiu ya bashi ranar a d'akin sa ya kwana dan so yake ya nunawa Sajeeda fushi yake da ita,Dole ma yasa a Kara masa aiki a kanta yadda duk abinda zai yi bazata iya Buda baki ta Masa magana ba.

Washegari karfe bakwai ya fito Palo ya zauna sai da ya ga fitar su Annur Yan makaranta ya nufi d'akin Yesmeen

Da sallama ya shiga d'akin su Yaya Abu na kwance da Yesmeen na can karshen gado a kwance shigowar sa yasa Suka mik'e zaune dan ba bacci suke ba Hira suke,sai da suka gaisa Yaya Asmau ta fara magana tana "gobe Zan tafi idan Allah ya kaimu wlh Abban yaran nan ya Kira akan na dawo ita dai Abu tace anan zan barta"

"Aikuwa anan zaki barni dan ba abinda zai maidani can sai dai idan kanina bayasan zamana"

"Kai haba Yaya Abu wallahi ki Sha zamanki ni nafiso ma ki zauna kici arziki kema"

Tuni Yaya Abu ta hau washe baki

Kabiru kuwa yace "toh tunda gobe zaki koma mai zai hana ki shirya ki tafi kasuwa Yaya Abu ta raka ki ki siyo kayan tsaraba ai bakya tafi haka ba komai ba"

Tuni suka washe baki su biyu Suka hau godiya da Addu'a

Kabiru cikin tsananin murna ya tashi ya fito daga d'akin
Chapter 40 · 0% Book details