Sashe 65
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaskiya ban yarda dake ba dan duk yaran gidanan na sansu bansankii ba sanan matar gidan da safe suka yi tafiya da yaran wacce matar gidan kike nufi"?
Yesmeen tasan idan ta tsaya yi masa bayani zai cigaba da bata Mata lokacine har Kabiru ya dawo ya rutsa ta a gidan.
Tayi waje da sauri dan ta Nemo mai motar tazo su d'auki Sajeeda.
Sai dai ko da ta fito sai ta rasa hanyar da zata bi dan lokacin da Suka dawo bata wani yi kalle kalle ba tunda a matsayin bata gani Suka taho,gashi layin shiru ba yawaitar mutane sai manyan gidaje, gudu ta ringayi kad'an kadan tana bin layin da ta ga a mike.
Horn din da taji da zata Sha kwana yasa ta sunkuya da sauri kamar tana gyara takalmin ta a daidai lokacin da motar ya wuceta a guje,tabi motar da kallo ganin motar ta tsaya a k'ofar gidan yasa ta gwallo ido dan Kabiru ma ta hango a gaban motar,
Hannunta dafe da kirjinta da taji kamar ya fado saboda tsoro ta mike da sauri,ta sa gudu,haka kawai dabarar sunkuya ya fado mata bawai dan tasan Kabirun bane dan tabbas da bata sunkuya ba ba abinda zai hana ya ganta.
Gudu take da iya karfinta har ta fara hango titi,a madadin tayi titi sai ta yanki wani layi dan tasan zasu iya biyota.
Ko kad'an bata san Kan garin ballantana tasan Inda take jefa kafarta ba, duk kwanar da ta gani fadawa kawai take,tana share hawayen tausayin Sajeeda da bata samu ta d'auko ta ba.
Sai da ta tabbatar da tayi nisa ta samu wani k'ofar gida ta zauna tana maida numfashi,bata jima da zama ba taga an bud'e gate din gidan ta dago da sauri taga wani ne ya fito daga gidan zai Kai Kabiru a shekaru,hannun sa rik'e da carbi dan an fara kiraye kirayen sallah magriba,
Ganin Yana kallonta yasa tayi saurin gaishe shi ya amsa cikin faraaa Yana "Yarinya daga Ina"?
"B'ata nayi babba dan Allah ka taimaka min da kudin mota da tasha Zan tafi katsina da Yar uwata nazo munzo wani gida sai muka fito akan zamu tafi sai wasu Suka biyo mu,shine nabi ta wata hanyar tunda zu nake bulayin nemanta ban ganta ba"
"Allah sarki,wajen wa kuka zo anan din"?
"Aikatau aka kawo mu daga katsina shine wayanda muke yiwa aikin suka ce zasu yi tafiya Suka sallame mu"
"Allah sarki Ina ga b'ata garine suka biyoku abinda za'ayi kizo mu Shiga ciki yanzu dare yayi bazai yu kina mace ki dau hanyar katsina ba gobe da safe idan Allah ya kaimu sai ki shirya a Kai ki Tasha kila itama Yar uwar taki ta gaji da nemanki ta tafi ita kadai"
Yesmeen zubewa tayi a kasa ta hau yi Masa godiya yace ta biyo shi abaya.
Ta mik'e tabi bayansa koda Suka Shiga wata ta gani a palon za ta kai Yaya Abu a shekaru,tana sanye da hijabi da carbi a hannunta.
Sallamar da mutumin yayi ta amsa tana kallon yesmeen din dake biye dashi a baya.
Yesmeen kuwa ta zub'e a kasa ta hau gaisheta itama cikin faraa ta hau amsawa mijin ya hau yi mata bayanin da Yesmeen ta Masa,itama ta ringa zuba Allah sarki tana ba komai ta kwana din gobe sai a Kai Yesmeen Tasha.
Daga haka ta hau kwallawa wata Aisha Kira,Yesmeen kanta a kasa har Aisha ta karaso matar ta mata bayanin ta Kai Yesmeen daki,ta samu tayi sallah a zuba mata abinci idan ma wanka take so tayi a nuna Mata bandaki.
Yesmeen ta hau yi Mata godiya
Ta mik'e tabi bayan Yarinyar da zasuyi kusan saa daya.
Suna Shiga d'akin yarinya ta nuna mata bandaki ta shige dan burinta kawai ta samu ta rama sallolin dake kanta dan ko azahar batayi ba tana sallah Rabin hankalin ta na wajen Sajeeda tasan yanzu Kabiru ya haukace da nemanta.
Sai da ta rama sallolinta ta hau yiwa Sajeeda Addu'a akan Allah ya kareta daga sharrin Kabiru,dole tasan yadda zatayi a kaiwa Sajeeda a gaji kafin ya Kara cutar da ita dan har yanzu ta kasa gane Mai yaje nema a d'akin jiya daddare.
Abincin ma da aka kawo mata kasa ci tayi dan ji tayi Sam bazata iya cin abincin ba.
Tunanin da ya fado mata yasa tayi saurin kallon wacce aka kira da Aisha dake ta latsa wayarta ta ma shareta kamar batasan da zamanta a d'akin ba.
Tayi gyaran murya tana "Aunty dan Allah ki taimaka min da Aron waya inaso na Kira Yar uwata"
Aisha karamar wayar dake gefenta ta dauka ta mika mata batare da tace mata komai ba ta tashi tayi waje.
Yesmeen kuwa jiki na rawa ta hau shigar da lambar Nusrah dan ba lambar Wanda ta rik'e a kanta sai lambar Nusrah da Sajeeda.
Safa da marwa kawai take dan burinta Nusrah ta dauki wayar ta fada Mata halin da ake ciki.
Tana Jin an dauka ta saki ajiyar zuciya tana "Nusrah Yesmeen ce kina jina"?
"Yesmeen kece ko mafarki nake yi"?
"Nice Nusrah ke kadai ce"?
"Aaa nida Mama ne a daki tana yiwa jaririya wanka"
Yesmeen kasa tayi da murya tana "kibar d'akin Nusrah magana Zan Miki Mai mahimmanci kiyi sauri"
Nusrah mik'ewa tayi daga Kan gadon,tayi waje Yaya Abu dake yiwa jaririya wanka ta bita da Ido
"Yesmeen ya akayi ba bar d'akin a Ina Kika samu waya taya akayi Kika kirani"?
"Nusrah Umma tana cikin hatsari kiyi sauri ki kira Gwaggo taje ta d'auketa dan ni guduwa nayi Abba ne yake san kasheni"?
"Kamarya Yesmeen bangane maganganun ki ba"
"Nusrah bamu da lokacin da zan ringa Miki bayani kiyi saurin Kiran Gwaggo Abba shi ya jefa umma a halin da take ciki,nasan bazaki gane ba, Abba kungiya ya Shiga dan yayi kudi,toh da umma yayi kudin shiyasa take ta rashin lafiya labarin nada tsayi Abba ya San nasan sirrinsa shi yasa nayi karyar makanta,saboda Kar ya cutar dani, Nusrah Dan Allah banida lambar Gwaggo kiyi sauri ki kirata yanzu saboda gobe da safe taje ta d'auko umma Kar Abba ya sake cutar da ita"?
"Yesmeen a hayyacinki kike kuwa kinsan Mai kike cewa kuwa Abban mu fa naji kina ya Shiga kungiya yayi kudi da umma innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Kamarya Wai kimin bayani bangane ba"
Yesmeen da sauri da sauri ta hau bawa Nusrah labari.
Nusrah kuwa jikinta ya dauki wani irin kyarma ta saki ihu tana "Abba ya cucemu Yesmeen ga mama nan ita zan gayawa yanzu nan"
"Aaa Nusrah karki"!!!
Kit taji Nusrah ta kashe wayar Yesmeen hankali a tashe ta hau Kiran wayar Nusrah Amma bata dauka ba.
Bazata so Nusrah ta fadawa Yaya Abu ba.
Nusrah kuwa dakinta ta koma tana kuka wiwi tana zuba sallati dan shakka babu ta yarda da maganar Yesmeen.
Yaya Abu kuwa yadda ta shigo yasa ta ajiye jaririyar akan gado ta tarota tana "Wai waye ya kiraki a waya ne lafiya"
"Mama Abba ya cucemu Abba ashe kungiya ya Shiga dan yayi kudi,Ashe Abba ba kudin Allah da Annabi ne dashi ba da umma yayi kudi,?
Yaya Abu yamutsa fuska tayi tana "Kamarya bangane ba"?
Tiryan tiryan Nusrah ta kwashe komai ta fada mata ta Kara da "Mama ki taimaka ki tafi daddaren nan Kar ya cutar da umma innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"?
Yaya Abu Zama tayi a gefen gadon tana "yanzu Yesmeen ce duk ta fada miki haka ke kin yarda Abban ku kungiya ya Shiga ba sharrin yarinya nan bane? toh bar kuka haka kinsan me za'ayi yanzu nan zanje nabi motar dare naje na dauko Sajeeda karki sake ki fadawa kowa wanan maganar dan idan har Kika furta maganar nan Kamar kin tonawa Abban ku asirine kinji Mai nace ko"
Nusrah Kai ta hau gyadawa tana "Mama ki ceto mana umma kiyi sauri Kar ya cutar da ita.
Yaya Abu mayafinta kawai ta yafa ta dauki Jakarta tana "karki fadawa kowa maganar Nan Nusrah"
Daga haka tayi waje da sauri tana yin nisa da gidan ta d'auko wayarta ta hau Kiran wayar Kabiru
Ko kad'an tak'i yarda a zuciyarta da kungiya ya Shiga dan yayi kudi, karyar Yesmeen ne kawai,Ashe duk tsawon lokacin nan Yesmeen na gani,anya ba ita ta Shiga d'akin Sajeeda ta shige kasan gado ta gaura mata Mari ba,
Kabiru
Yana tura k'ofar d'akin Sajeeda ya hangota a kwance Kamar matacciya da sauri ya karasa wajenta,ta dagota yaga tana numfashi kad'an kadan,ya saketa da sauri ya sauka kasa Yana Jin kamar kirjinsa ya faso saboda tashin hankali Yana fita waje yayi wajen motarsa hankali a tashe ya ruko hannun Rabiu dake jingine a mota Yana "Yesmeen ta gudu Rabiu shikenan asirina ya tonu ta fallasa sirrina ga Sajeeda can kamar a sume ta fada mata na Shiga uku Rabiu yanzu ya zanyi"
"Wai kana nufin guduwa tayi"?
"Ta gudu wallahi ban ganta ba da dukan alamu ta fadawa Sajeeda dan gata can Kamar ta suma,nasan idan ba fada mata tayi ba va abinda zai sumar da ita watakila ba iya Sajeeda zata bankadawa sirrina ba kila ta fadawa wasu na Shiga uku Rabiu asirina ya tonu tun ban mori arzikina ba"
"Yanzu abinda za'ayi ka d'auko Sajeeda mu tafi kungiya sai mu saka shugaba ya duba Mana inda Yesmeen din take idan har ta fadawa wani zai fada Mana sai asan abin Yi"
Kabiru a haukace ya koma cikin gidan kafa ba takalmi ya haye sama ya sabo Sajeeda a kafadarsa ya sauko da balain sauri ya sakata a Bayan motarsa jikinsa sai rawa yake.
Wani irin gudu yake falfalawa.
Yana ya Shiga uku,kiran Yaya Abu daya shigo wayarsa dake gaban motar yasa ya saki ihu Yana "shikenan itama ta fada Mata Rabiu ga yayar Sajeeda na kirana".
"Ka dauka kila wani abun zata fada maka"?
Hannunsa rawa kawai yake ya daga wayar abinda Yaya Abu tace Masa yasa ya taka wani irin birkiii.......