Sashe 15
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
So nake ma na Kira Abban ku nace masa zanje asibiti bana Jin dadin jikina zanje likita ya dubani"
"Sannu umma ki daure ki sha kunun Kinga da zafin sa"
Dak'yar Sajeeda ta sha kunun kamar wacce aka yiwa duka haka take jin jikinta.
Daga sallahr asuba ta koma bacci,a cikin baccin ta taji Kamar ana zungura mata abu a gabanta ta rasa wane irin masifa ne wanan"
Wajen biyar na yamma su Saifullahi suka shigo gidan a guje suna ihun murna
Sajeeda dake can daki ta fito da sauri
Yesmeen dake kitchen itama ta fito daga kitchen din tana kallon su
Faisal ne ya fara magana cikin murna Yana "Abba ya siyo sabuwar mota dalelliya yana waje yanzu zai shigo"
"Umma ke Kinga kyaun motar"?
Cewar Saifullahi Yana washe baki
Sajeeda
Da ido kawai nake bin su dan ban ji digon farin ciki a zuciyata na siyan motar da suka ce Abban su yayi ba,ni a yanzu ma tsoron yadda Abban su ke kashe kudi yake dan naji Wai Yana shirye shirye tura Saifullahi kasar waje yayi karatu,a kasa da wata hudu Abban Nusrah yayi irin wanan kudin,anya kudin nan nasa na halal ne kuwa.
Bakin sa a washe ya shigo palon Yana kada mukulli ya nufo wajen da nake tsaye Yana "Sajeeda na Miki sabuwar amarya fito waje kiganta"
So nake na mishi tambayoyi amma na kasa Kamar wacce aka likewa baki haka nabi bayansa,na ga dalaleliyar motar a tsakar gidan,bansan kudin motar ba amma nasan masu kudi ke hawa irin motar nan Wanda ya isa ya tadda Kai"
Yake kawai nake Ina Masa Allah ya sanya alheri cikin murmushi ya Miko mun mukulin Yana "Ke na siyawa Sajeeda babban burina dama na samu kudi kiji Dadi na faranta miki ba kaina na siyawa ba ke na siyawa"
Sakin baki nayi ina kallon sa ya gyada min kai "Ni Kuma Abban Nusrah baka siyawa kanka ba sai ni"?
"Kin cancanci na siya Miki Sajeeda"
Girgiza kaina nayi na maida Masa mukullin Ina "bazan karba ba Abban Nusrah dan duk Wanda ya tambayeni Ina na samu motar Nan bansan mai zance Masa ba"
Take ya hade rai ya hau masifa kamar zai kawo min duka Wai so nake nace sata yakeyi bata hanyar halal yake samun kudinsa ba"
Nidai shiru nayi bance Masa komai ba.
Sai gashi a ranar yayi fushi yak'i kwana a dakina duk hakurin da na bashi yaki ya saurareni.
Washegari ma ko ta kan Sajeeda bai bi ba yana tashi ya Shiga kitchen ya dafa abinci dayaji namomi ya zuba a plate din da yake kaiwa Kare abinci dan da kansa yake hadawa Karen abincin da yake ci.
Zuciyarsa cike take da farinciki dan a yau zai samu cikar burinsa dan idan komai ya tafar Masa yadda yake so ya zama multi millionaire
Har ya d'auki abincin zai yi waje ya ajiye saboda fitsarin daya mugun matsar sa.
Sai ya nufi bandaki dan yayi fitsarin.
Yesmeen dake labe tana lekansa da tun jiya take Addu'a Allah ya bata saa da nassara.
Ganin ya ajiye abincin yasa ta fito da balain sauri hannunta dauke da shinkafar beran da ta Nemo tun a jiya.
Tana zuwa ta juye shinkafar beran gabanta na mugun faduwa.
Ta fito daga kitchen kenan taci Karo da Kabiru cikin mugun faduwar gaba ta ja da baya ya shige yana watsa Mata mumunan kallo tayi waje da gudu.
Ya d'auki abincin yayi bayan gida.
Yana zuwa ya tsugunna a gaban Karen ya ajiye abincin a gabansa.
Da sauri Karen ya fara cin abincin Yana kada jelarsa.
Kabiru kuwa sai shafa Masa baya yake Yana tunanin yadda zaiyi a Daren yau dan abinda akace yayi wanan da zaiyi yafi kowane wuya da hatsari
Ganin Karen ya daina cin abincin ya sa ya daina shafa shi yaraf Karen ya zub'e a kasa bakinsa na fitar da kumfaa hankali a tashe Kabiru ya mik'e tsaye Yana kallon Karen tun Karen na motsi har sai da ya daina.
Hankalinsa a mugun tashe ya girgiza Karen
Yaga ko motsi baya yi babu ma alamar rai a jikinsa wani irin ja da baya yi cikin azabar tashin hankali ko baa fada Masa ba Karen dai mutuwa yayi.
Wani irin ihuuu ya saka yana "Yesmeen kin kashenii.............
Hmmm
Yanzu aka fara labari ku biya 500 zuwa acct dinan 2029764071 ko katin mtn zuwa lambar Nan 08033719070 ku turo da shaidar biya ta layin Nan 08033719070 ko wanan layin 08064484400
Mutanen Niger ku tuntubi lambar Nan
+227 96 82 89 84 Dan kuyi payment ku more karatu..
MG'S SKINCARE
Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?
Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,
Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,
Ga product din kamar hka,
Sabulu 4k
Mg's beauty kit 14k
Herbal whitening soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Glow oil
Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k
Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,
Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Team glow😍
*RUFAFFEN SIRRI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*Page 10*
A haukace Kabiru ya ringa girgia Karen Yana kuka wiwi,shi kadai yasan wahalar da ya sha kafin a iya hada masa abinda zaiyi ya samu cikar burin sa,sai a yau da zai samu cikar burin sa Yesmeen ta kashe masa arzikin sa.
Ya dauki abincin ya kurawa plate din ido, zuciyarsa kamar tayi bindiga saboda bakin ciki,ba Mai Masa aika aikan nan sai Yesmeen ba wacce ta saka masa ido sai ita daga fita yayi fitsari shine ta Shiga kitchen taje ta masa wanan aika aikan.
Shikenan duk burikan sa da wahalar da ya Sha ya tashi a banza, Yesmeen ta jawo mai Asara
A wani irin haukace yayi cikin gidan jikinsa na wani irin rawa ba abinda zai hana ya raba Yesmeen da ranta a yau.
Bugun da yayi wa k'ofar palon yasa Sajeeeda mik'ewa a tsorace tana "Abban Nusrah lafiya"?
Ko kallon ta bai yi ba yayi hanyar d'akin yesmen
Yesmeen kuwa tunda taga yayi waje ta shige d'akin ta ta kulle wani irin tsoro ne ya shigeta a lokacin da Suka hadu a k'ofar kitchen sai taji ta fara nadamar ma zuba shinkafar beran dan tasan indai Karen ya mutu atake dole Kabiru ya zargeta tunda yaci karo da ita a lokacin da take fitowa daga kitchen, kirjinta kamar ya fado saboda fargaba ta tsaya a window tana kallonsu.
A lokacin da Karen ya zub'e a kasa taji Kabiru ya Kira sunanta bandaki tayi a guje dan tasan yau kashinta ya bushe kuka kawai take a jiya tayi mafarkin Karen na ta cizon Sajeeda har sai da Sajeeda ta daina motsi,sau biyu tana mafarki a jere hakane yasa ko da ta tashi,sai taji gabadaya ta kasa samun nutsuwa zuciyarta tayi ta rayya mata da ta zuba wa Karen maganin b'era dan daga mafarkin da take tasan karen su Kabiru ke so ya cutar da Sajeeda,bazata iya zuba ido tana kallo ba, dole tayi wani Abu.
Bugun da Kabiru ya fara yiwa kofarta yasa ta saki ihu dan ba k'aramin bugu yake yiwa k'ofar ba ta tuna yadda ya ringa rantsuwar zai kasheta idan ta Kara masa shishigi.
Sajeeda kuwa hankalin ta ba karamin tashi yayi ba da ta ga yadda Kabiru ke k'ok'arin balle k'ofar d'akin Yesmeen Yana rantsuwar sai ya kasheta.
Cikin tashin hankali ta fara magana tana "Abban Nusrah Mai Yesmeen din ta maka haka dan girman Allah kayi hakuri karka manta marainiya ce ka rufa min asiri mai ta maka haka dan Allah"
Cikin jajjayen idonsa ya kalli Sajeeda Yana "Kinsan Allah yarinya nan sai na kasheta sai dai duk abinda zai faru ya faru"
ido Sajeeda ta zaro cikin tashin hankali tana " A hayyacin ka kake kuwa Kabiru Mai ta maka da zaka kasheta innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"
Tace cikin ihu a daidai lokacin da ya buga k'ofar da balain k'arfi ya balle,ya shige yana hucci kamar wani zaki bai yi wata wata ba ya fara buga k'ofar bandakin da karfinsa.
Sajeeda ta saki ihu Kamar yadda Yesmeen dake cikin bandakin ke zunduma ihu tana azo a taimaka mata.
Sajeeda kuwa ganin da gaske idon Kabiru ya rufe idan har ta bar shi ya shiga bandakin shaidan na iya cin galaba a kansa ya kashe mata Yesmeen.
Jan kabirun ta farayi da karfinta tana rokon sa shi kuwa iya karfinsa yake tura k'ofar dan ya balla kofar ita kuwa Sajeeda ta Kankame shi duk yadda yaso ya tureta ya kasa dan ba karamin kankama ta masa tana ihu ba.
Kabiru ya runtse idonsa jikinsa na cigaba da rawa hawaye sai zubo masa yake na asarar da Yesmeen ta jawo Masa yanzu duk mafarkin sa na yin kudi ya tafi a banza dan dak'yar idan shugaban zai Kara sauraransa dan Yana ta basu wahala a duk abinda aka ce yayi bai yi ba Sajeeda da zai samu komai yazo masa cikin sauki,ta bijire masa hanyar da ya rage Masa Yesmeen ta ruguje masa Anya Yesmeen dinan mutum ce kuwa"?ko dai tasan dalilin daya saka ya kawo Karen cikin gidan.
Hucci kawai yake Sajeeda kuwa har lokacin tana Kankame dashi tana bashi hakuri kamar yadda yesmeen dake bandakin ke aukin bashi hakuri tana sharrin shaidan ne ya yafe mata.
Baya Jin kwarin jikin sa saboda irin bugun da yayi wa k'ofar d'akin nata murya can kasa da tunanin daya darsar Masa na idan har ya dage zai yiwa Yesmeen wani abu,asirinsa na iya tonuwa a gaban Sajeeda dan Yesmeen na iya fadar wani Abu ko shi zuciya tasa ya Fadi wani abu asirin sa ya tonu.