← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 80

Sashe 4

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ga Allah naji Dadi rumgume da juna muka yi Bacci.

3am

Kabiru a hankali ya leka fuskar Sajeeda yaga tayi nisa a bacci.
Ya zare jikinsa daga nata ya sauko a hankali sabida Kar ya tasheta daga bacci.

Gefen gadon ya duba a hankali ya d'auko pant din ta ya kudundune a hannun sa cikin sanda ya fice daga d'akin yayi waje.

Yana zuwa yayi bayan gida ya d'auko tukunyar kasar da ya shigo dashi da ba Wanda yasan ya shigo dashi,ya saka pant din a ciki ya fara surutan da aka ce yayi a hankali Yana waige waige duk da Yana da tabbacin ba Mai ganin sa dan a sharrudan ance Kar ya sake ya yarda a gan shi.

Yesmeen.

Bata da nauyin bacci ko kad'an ko ya taji motsi sai ta farka.
Motsin k'ofa yasa ta bude idonta.

Kafin taji Kamar takun tafiya a ta Bayan dakinta Inda ta mik'e zaune tare da dafe kirjinta cike da tsoro.

A hankali ta Mike ta leka ta window..........

MG'S SKINCARE

Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4k

Mg's beauty kit 14k
Herbal whitening soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Glow oil

Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glow😍

*RUFAFFEN SIRRI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Page 3*

Ba abinda take iya hangowa sabida duhu,amma dai kamar mutum take hango wa tunanin ta kila barawone ya shigo gidan hakane yasa tayi sauri ta bar jikin window ta nufi k'ofar d'akin cikin sand'a ta bud'e a hankali dan so take ta je k'ofar d'akin Umman ta sanar musu,tana fitowa Kabiru ya shigo shi ma cikin sand'a,ganin Yesmeen yasa gabansa mugun faduwa dan daga shi sai gajeran wando,itama jikinta ne ya dau rawa cikin rawar baki tace "Abba motsi naji a bayan dakina Ina tunanin barawone ya shigo shine na fito na fada muku"

Sai a lokacin Kabiru ya dan saki ajiyar zuciya dan duk tunanin sa ta gan shi

"Ki koma nima motsin naji shi yasa na fito ba kowa Ina ga b'eraye ne"

Da sauri ta juya ta koma ciki ta rufe kofar ta ta saka sakata ta kulle ta Kara gyara labulen window ko da ta kwanta sai ta kasa komawa bacci dan zuciyar ta cike take da tsoro tunda Nusrah tayi aure take jin tsoron kwana ita kadai.

Kabiru kuwa Yana shiga d'akin yayi sauri ya kwanta a gefen Sajeeda yayi rigingine Yana kallon ceiling sai murmushi yake shi kadai dan a yau kawai da ya rabawa yayan sa kudi ya sauke hakkin da ya Kamata ace shi yake saukewa ba Sajeeda ba sai yaji wani irin farin ciki da ya dade bai ji irin sa ba,yana bakin ciki yaga yaran sun tsallake shi idan suna zaune sun tafi wajen Sajeeda suna Yar murya ta basu kudi har Kuma suka girman kallon babu suke masa dan sau tari zai ji suna mun san Abba bashi da kudi,abun na matukar Kona masa rai zai iya cewa tunda yaran Suka dai girma ba Wanda ya tab'a tunkarar sa yace Abba ina san kaza kayi min kaza duk wajen Sajeeda suke zuwa,Wanda yasan sabida bashi dashi shi yasa basa tunkarar sa abin arzikin da zai ce yayi shine a lokacin Auren Nusrah ya dan tab'a abin arziki,amma komai dai Sajeeda ke yi Kuma bata tab'a nuna gajiyawarta ko damuwa ba dan macece ita Mai zafin nema,a yau da yaga ya Sanya yayansa farin ciki yaji ya Kara kwadaituwa da ya samu kudin.

Abu daya ke damun sa a cikin dokokin da aka shimfida masa,na kin sallah na tsawon sati daya,yaso ya nuna bazai iya ba Rabiu ya dage Masa.

Haka yayi ta sake sake har aka Kira sallah Asuba Sajeeda ta mik'e zaune cikin hamma da adduar tashi daga bacci,shi kuwa yayi saurin rufe idon sa kamar
Bacci yake.

Sai da ta sauka daga gadon ta hau neman pant din ta dan zani kawai ta rufe jikinta dashi.

Ganin ta duduba wajen da ta kwanta bata gani ba sai tayi tunanin ko wajen da Kabiru ke kwance ya danne,hakane yasa ta hau tashin sa akan ya tashi yayi wanka Kar ya makara sallah asuba.

Kabiru kuwa kamar mai baccin ya mike Yana mitsitsika ido,ya mik'e tsaye ta janye bargon ta hau duduba Inda ya kwanta bata gani ba sai gashi har zanin gadon ta cire,Kabiru kuwa ya San mai take nema Sarai hakane yasa ya shareta ya shige bandaki yayi wanka ya fito ko alwala bai yi ba ya nufi wajen kayan sa.

Sajeeda kuwa cikin mamakin rashin ganin wandon ta tace "Abban Nusrah kaga ban ga pant dina ba sai dubawa nake"

"Toh tsayawa Neman pant zakiyi ko Kuma wanka zaki Shiga sabida kar ki makara sallah asuba,kin wani daddage da nema kamar baki da wani"

"Ba haka bane Abban Nusrah kasan yesmeen na shigowa d'akin tayi gyara Kar nazo taga pant akan gado Ko a wani wajen kaga da kunya ko"

""Umm ni dai na tafi massallaci sai ki dage da nema"

Yayi waje.

Sajeeda Kuma ta shige bandaki dan tayi wanka ta yanke idan ta iddar da Sallah sai ta gyara d'akin ko zata gani.

Kabiru kuwa yana fita ya labe daga waje Yana kallon lokacin da su Saifullahi suka fito daga gidan suka nufi massallacin.

Sai Kuma yaji kirjin sa ya masa nauyi Mai bambanci Arne da musulmi sallah ce fa, yanzu haka zai yi sati kenan ba saka goshin sa a kasa ba? tuna irin kudin da zai yi yasa ya ture tunanin a ransa dan a wanan yanayin da yake ciki kudi kawai shi ne burin sa dan Rabiu yace masa Rabin masu kudin garin nan duk ta haka suka yi kudin su.

Sai da ya ga yaran sun dawo sun shige ciki shima ya fito daga lungun da ya b'uya ya Shiga gidan.

Koda ya Shiga daki Sajeeda ya Tarar ta daddage da neman pant da hijabin da tayi sallah a jikinta har zanin gadon ta canza sabida Neman da take shi kuwa ya hade rai dan ko da wasa baya so ya bata fuskaar da zata ishe shi da maganar pant din ta.

"Abban Nusrah kaga har daga katitar nan nayi wlh Babu pant ba dalilin sa"

"Mtsss kina da matsala wlh Tom mai Kika daddage kina nema daya ne dake"?

"Aa ba dayane dani ba Ina ta mamakin yanda zan kwana da abu a gefena yanzu na duba ko sama ko kasa bangani ba"

"Baki da abin yi ne Sajeeda ki cigaba da nema idan Kuma ba barawone ya shigo ya rasa mai zai dauka sai wandon ki"

Kabiru yace tare da Jan siririn tsaki,ya kwanta Yana zai koma bacci karfe goma ta tashe shi daga bacci zai je wajen abokinsa da ya bashi kyautar kudi yace masa yaje Yana san ganin sa.

Da toh ta bishi ta fito daga dakin tana tunanin kila wani wajen ma pant din yayi ta tsaya wahalar da kanta.

Tare suka yi abincin karyawa da Yesmeen dake bata labari taji motsi jiya a bayan windonta,ko baccin arziki bata yi ba

Dariya Sajeeda ta saka mata ta ringa ce mata matsoraciya yanzu haka b'eraye ne.

Sajeeda

Tare muka ci abinci da Abban Nusrah da yazo fita ya bani Dubu biyar Wai nayi cefane har ga Allah daga jiya zuwa yau bansan kalar Farin ciki da Addu'ar da nayi wa Abban Nusrah ba, hakika ya kyautata wa nida yarana,dan ko da Abban su ya fita suka shigo hirar kyautar da aka musu kawai suke Annur kuwa ya hau cewa "Nayi mafarki Abba ya Zama mugun Mai kudi Wai ya gina wani gidan bene duk muna ta murna amma ban ga umma a gidan ba"

Murmushi na saki Ina "idan baka gani a gidan ba wata Abban ku ya auro kenan,a lailai auta kyautar da aka ma ya maka dadi irin wanan mafarki haka.

Tare muka yi aikin abincin da aka kawo min da Yesmeen dan Kamar na mayar nima na dan huta tunda na samu Yan canji,dan daidaikun Rana ne baa kawo min aikatau Kuma har ya zame min jiki.

Da yamma Ina d'aki sai ga Abban Nusrah ya shigo gidan da sallama fuskar sa Kamar gonar auduga ba kowa a gidan sai ni kadai dan duka yaran sun tafi islamiya.

Nima ganin fuskarsa a washe yasa nima na washe bakina Ina "Abban Nusrah Mai muka samu ne naga fuskar ka d'auke da Annuri haka"

Zama yayi a gefena Yana "Sajeeda Ina ga mun kusa zama masu kudi"

"Allah Abban Nusrah abokin naka ya nemo ma aikin ne"?

"Daga wajen sa nake yanzu haka ai yanzu ma zama bai Kama ki ba tashi Zaki yi mu tafi ki tayani yi masa godiya Kinga yau ma kudin daya bani kyauta Sajeeda"

Gwalo ido nayi a lokacin daya bud'e ledar dake hannun sa wrapper Dubu Dubu ne guda biyar,mik'ewa nayi na dafe kirjina Ina "Abban Nusrah duka wanan kudin ya baka aikin me yake yi haka"?

"Ke kinsan kudin sa kuwa wanan ai ba komai ne ma a wajen sa ke baki ga alkawarukan da yamin ba a ciki kuwa har da kyautar gida yace bazai manta alherin da na masa muna Yara ba"
Chapter 4 · 0% Book details