Sashe 14
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta ga k'ofar d'akin ta a rufe yake ta tabbatar da mafarki take tabi ta hada gumi,ta kalli hannun ta da ta rik'e wasikar da ta rubutawa Sajeeda,ta dago ta kalli agogo taga karfe Sha biyu na dare ta mik'e tsaye da sauri dan har ga Allah so take ta gudu ta bar gidan,dan rayuwarta a cikin hatsari take tunda har Kabiru ya fara mata Barazana akan zai kasheta idan bata gudu ba watarana zai kasheta din.
Jakar da ta zuba kayan ta ta d'auko bayan ta ajiye takardar a karkarshin pillo a hankali ta fara karewa dakin kallo hawaye na zubo mata hakika Sajeeda ta rik'e ta tamkar Yar cikin ta bata tab'a barin ta tayi maraici ba duk da dangin mahaifinta sun watsar da ita,mahaifinta ma gani take ya manta da Yana da ita dan bai tab'a Neman ta ba.
A yanzu bata san hannun wa zata fada ba
Tafi minti talatin a tsaye tana zubar da hawaye tana tunanin halin da ta tsinci kanta a ciki tayi matukar nadamar leka Kabiru,dan da bata leka shi ba da duk haka bata faru ba.
A hankali ta murda k'ofar d'akin ta fita palo kirjinta na dukan uku uku fitilar palon ma a kashe take ko Ina shiru sai karar fanka.
Cikin Sand'a ta nufi k'ofar fita daga palon ta murda a hankali ta fice tare da rufo k'ofar duk abinda take yi jikin ta rawa kawai yake.
Taku uku tayi taji motsin bud'e k'ofa.
Cikin zafin nama ta shige cikin fulawowi dake kewaye da jikin bangon runtse idon ta tayi da k'arfi dan ji tayi abu ya soketa a baya ta d'auke numfashin ta a lokacin da Kabiru ya fito Yana dube dube.
Ganin bai ga kowa ba yasa yayi bayan gidan dan ya duba lafiyar karen sa kasan dan Kamar motsi yaji
Yana yin bayan gidan Yesmeen ta fito daga fulawowi ta shige cikin gidan da gudu ta bud'e kofar ta ta shige tana sauke ajiyar zuciya dan ta balain tsorata ta d'auka Kabiru zai ganta.
Ba haka taso ba taso ta gudu a yau dan ta balain tsorata da Kabiru amma ko bata gudu yau ba sai ta gudu gobe.
Tana Jin motsin sa a bayan gidan sai da ya jima kafin ya koma ciki.
Sajeeda
A firgice ta tashi daga baccin da take ta hau kalle kalle,ganin Kabiru a gefen ta yasa ta hau tashin sa tana cigaba da kallon bakin k'ofar jikinta na rawa Karen da Kabiru ya kawo cikin gidan tayi mafarki ya shigo Yana kokawa da ita Yana jan zanin ta tana ja
Kabiru bude idonsa yayi yana "Sajeeda zan bar Miki d'akin nan na koma dakina kawai dan bakya barina nayi bacci na gaji"
Kuka Sajeeda ta fashe dashi tana "Kabiru dan girman Allah ka fitar da Karen nan da ga gidanan rabon da nayi bacci cikin dadin rai har na manta tun muna tsohon gida rabona da samun bacci Mai nustuwa kullum sai nayi mafarki da Karen nan na gaji Wallahi na gaji Kabiru idan har ba za ka fitar da Karen nan daga gidanan ba wlh zan bar gidanan kullum cikin fargaba nake dare yayi ban da mugayen mafarkai da nake fama dasu.
Ido Kabiru ya zuba mata cikin mamaki dan ya d'auka aikin da shugaba yayi a kanta zai saka duk abinda ta gani bazata iya magana ba.
Ya za'ayi ya barta ta bar gidan bayan yazo dab da cimma burinsa
Dole yasan dabarar da zai mata nan da kwana uku yasan ya samu cikar burin sa tashi yayi ya zauna Yana "Ya isa Sajeeda tsaya ki saurareni"
Sajeeda tsagaita kukan da take tayi Kabiru ya fara magana Yana "Ki kwantar da hankalin ki zan maida karen wajen Wanda ya bani amma baya gari sai ranar alhamis zai dawo na Miki alkawari Yana dawowa zan maida karen akwai barayi sosai a unguwar nan shi ya sa na karbo Karen dan na san idan barayi najin haushinsa zasu ji tsoron shigowa amma tunda kin saka tsoro a ranki ran alhamis zan maida Karen shikenan"?
Gyada Kai Sajeeda tayi Kabiru ya saki murmushi Yana ta koma ta kwanta.
Sajeeda tashi tayi tana bari tayi sallah raka'a biyu.
Kamar kullum dai tana raka'a biyu bacci ya kwasheta akan sallaya.
Kabiru kuwa na ganin haka ya fito daga d'akin yayi waje.
Yesmeen tuni ta ajiye batun guduwa a gefe dan sau uku tana mafarkin idan zata gudu sai Sajeeda tazo tayi ta rokonta Bata san Mai yasa take yawan mafarkin ba.
Yau har suka gama karyawa bata ga Sajeeda ta fito daga daki ba taga dai Kabiru ya fita ganin har Sha daya Sajeeda bata fito daga d'akin ba yasa ta nufi d'akin Sajeedan dan ta dubata.
Koda ta tura k'ofar d'akin Sajeedan a kwance ta ganta tana ta mutsu mutsu tana girgiza ita kadai idon ta a rufe ta hada gumi,.
Da sauri ta Isa bakin gadon ta fara girgiza ta tana "Umma umma ki tashi"
Sai dai bata bude idon ta ba ta cigaba girgiza hakan kuwa ya Kara dagawa Sajeeda hankali tayi waje da sauri taga ko su Saifullahi na nan"
Ganin su Saifullahi basa nan da ta duba dakinsu yasa tayi d'akin ta dan ta d'auko wayarta ta Kira Kabiru ta fada Masa halin da Sajeeda ke ciki.
Jikinta rawa kawai yake a lokacin da ta d'auko wayarta akan gado ta d'auko wayar kenan kamar ance ta kalli windon dakinta taga Karen a kwance Yana girgiza Kuma a ringingine Yana wani gurnani
Sakin baki tayi tana kallon Karen dan bata tab'a ganin Kare a kwance kamar mutum ba sai wanan,kamar an mitsineta tayi d'akin Sajeeda da gudu,Koda ta Shiga girgiza da mutsu mutsun ta cigaba da yi ta Kara fitowa da gudu tayi dakin ta ta tsaya a bakin windo shima mutsu mutsun taga Karen nayi,sai ta fara k'ok'arin ta hada tunanin ta waje daya tunanin daya darsan mata a zuciya yasa tayi waje da gudu zuciyarta cike da tsoro da fargaba tayi bayan gidan ta tsaya nesa da wajen da Karen yake har lokacin Yana ta girgiza dube dube ta fara yi idon ta ya sauka akan wani katon dutse bata tsaya bata lokaci ba ta d'auki dutsen ta jefa wa Karen ya kuwa mirgina ya fara haushi Yayo kanta ta kwasa da gudu ta koma ciki tare da rufo k'ofar
Jikinta karkarwa kawai yake dan saura kiris ya kawowa kafarta Cafka.
D'akin Sajeeda ta koma ta kuwa ganta a zaune tana sauke ajiyar zuciya ta bi ta hada gumi yesmeen kuwa tuni ta daskare a tsaye dan a yanzu abinda take zargi ya tabbata.
Sajeeda kawai take kallo zanin da ke jikinta ma a yau tayi mafarkin ta dashi
Ganin Sajeeda ta kallota yasa ta nufi wajenta tana "Sannu umma na shigo na duba ki ne da naga har sha daya baki fito ba"
Sajeeda bata iya ce Mata komai ba dan gabanta zugi kawai yake mata.
Mik'ewa tayi tana "Bari na shiga bandaki Ina zuwa"
Tana shigewa Yesmeen ta fito jikinta na rawa dan boye tashin hankali da take ciki tayi dama tunda aka kawo Karen nan tasan da akwai manufar da ya saka Kabiru ya kawo karen, Yanzu Kabiru ya rasa wa zai cutar sai Sajeeda mai ta masa haka da ta cancanci irin wanan zaluncin daga wajensa a iya sanin ta da zaman da tayi a gidan,Sajeeda kullum k'ok'ari take ta kyautata masa amma sakayar sa zai yiwa Sajeeda kenan,kuka kawai take na tsananin tausayin Sajeeda bata san Mai ma'anar abinda ta gani ba bata san wane cutarwa Karen zai yiwa Sajeeda ba,ta riga da tasan sirrin Kabiru a yau Allah ya haska mata abinda Kabiru ke nufi da kawo Kare cikin gidan zata yi iya k'ok'arin ta dan ta taimakawa Sajeeda Koda kuwa nata rayuwar zai zama a cikin hatsari.
Sake sake kawai take a zuciyarta
Motsin Sajeeda da taji a palon yasa ta goge hawayen ta ta fita waje.
Ta tarar da Sajeeda a zaune tayi fayau da ita kamar mara lafiya.
Kitchen ta shige ta d'auko flask din da ta zuba Mata kunnun gyada da Kofi ta Kai Mata palon ta fara k'ok'arin zubawa Sajeedan sai Sajeeda ta daga Mata hannu tana "Bazan iya sha ba yesmeen bana Jin dadi bani da lafiya bansan Mai yake damuna ba ba daidai nake ba"
Sajeeda ta karashe kwalla na zubo Mata
Yesmeen kuwa ta zuba mata ido itama idonta ya ciciko da kwallan tausayin Sajeeda kila ma jininta ake zukewa.
Cikin rawar murya Yesmeen ta fara magana tana "Umma Allah ya baki lafiya Wai me yake damun ki haka"?
Sajeeda share hawayen daya zubo mata tayi tana "Bansani ba Yesmeen idan har Zan kwanta sai nayi mugun mafarki da Karen da Abban ku ya kawo na rasa dalili jikina ba kwari Ina Jin ciwo a jikina bansan Wanda Zan fadawa ya gane Mai nake ji ba,na fadawa Abban ku yace ran Alhamis zai fitar da Karen Kinga jibi kenan rabona da bacci mai Dadi har na manta har tsoron rufe idona nake yi"
"Umma daga mafarkin nan da kike yi da Karen nan da Abba ya kawo Zaki san ba kalau ba kinsan wasu karnukan fa mayune Dan Allah umma ki dage da Addu'a ki daina ma bacci,idan za ki yi Addu'ar ki fito Palo kiyi saboda kiyi a nutse"
"Ina yi Yesmeen sai dai Ina fara yi bacci zai daukeni ni gidanan gabadaya nake so ma mu bari nidai haduwar Abbanku da wanan abokin nasa bai zame min alheri ba dan sai da suka hadu nayi bankwana da kwanciyar hankali Ina ta so na nusar da Abban ku ya kasa gane kiga fa daga zuwa gidanan Annur dina ya kurmance wallahi banga alheri a tarayyar Abban ku da abokin nan nasa ba na dai cewa Abban ku ya maida Karen nan Inda ya d'auko yace jibi zai maida Karen"
"Umma ki dai cigaba da Addu'a kafin kiyi bacci kiringa karatun Qur'ani"
Kiringa kwanciya da alwala ni tunda na fara mugayen mafarkai na dage da Addu'a na rage mafarkin dan biyun dare nayi nake tashi nayi ta Addu'a"
"Zan saita alarm a wayata in sha Allahu zan ringa tashi biyun daren