Sashe 38
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai kawai na iya gyada masa,Ina ganin ba wacce Zan fadawa halin da nake ciki sama da Nusrah Ina ganin ba wacce Zan fara fadawa cutar da Kabiru yamin sama da Nusrah,duk da Yesmeen ta rokeni Kar na fadawa kowa amma dole na fadawa Nusrah saboda tasan yau idan na Fadi na mutu Abban ta ne ya kasheni shi yayi ajalina ko a yanzu banji bazan nunawa Kabiru nasan halin da yake ciki ba.
Muryar Nusrah da naji da sallama ta wayar Saifullahi yasa na mik'a hannuna da naga kamar sirrancewa yake
Ya Mik'o min wayar na karba Ina tazo gida yanzu nan inasan ganin ta Ina Jin yadda ta rude tana tambaya ta ya taji muryata haka
Saifullahi yace "ke dai kizo Mana ai kema kina jin muryarta kinsan bata da Lafiya"
Ya kashe wayar Yana mun sannu
Na koma na kwanta Ina tambayarsa su Annur,da nake Jin mugun tausayinsa a raina Abban Nusrah akan duniya ya cutar dani ya cutar da dan cikinsa ya kurmance,a yanzu abubuwa suka ringa dawo min kaina Wanda banda na saka yardar Abban Nusrah a raina yaci ace na gano halin daya jefa kansa a ciki,wai duk Ina zaune ban taba sanin abinda ke faruwa ba,Abban Nusrah ya cuceni,Yesmeen itama ta cuceni dan da ta fada min da tuni na bar masa gidan na kwashe yayana.
Saifullahi haka ya zauna a gefena Yana jeramin sannu har Fahad shi ma ya shigo d'akin,duk Ina ganin tausayina a idon yarana basu san halin Nan da nake ciki mahaifun su ne ya jefani a ciki ba Ina tsoron ma ya yi wani abun ya Kara fadawa kan yayana banda Allah nasan Yesmeen da nasan Kabiru ya Dade da cin galaba akan ta,dan ma duk abinda zai faru tana gani a mafarki Kamar yadda babarta ke ganin komai a mafarki kafin ta rasu.
Idona a rufe naji shigowar Yaya abu da plate din abinci tana "Ki tashi kici abinci Sajeeda ni na rasa me yake damunki kike wanan kwanciya da kukan anya ba wani matsala ne dake ba iya makantar Yesmeen ke damunki"?
"Bata da lafiya ne Mama Kuma dole umma ta shiga damuwar halin da Yesmeen ke ciki,tashi daya ta wayi gari bata gani,Kamar yadda Annur ya wayi gari ya daina iya magana abunan na bani mamaki"
"Ai ba abun mamaki bane saifullahi Allah yakan jarrabci bawan sa dan ya gwada imanin sa,kunga Abban ku Allah ya Masa arziki a yanzu sai Kuma ya jarrabce shi ta hanyar tab'a yayan dan yaga ko zai iya jurewa in Sha Allah aka cigaba da neman magani zaa Dace watarana ki daina saka damuwa a ranki"
Ina murna nazo naci arziki ke Kuma kina langwabe wa
Ni dai gabana da naji ya fara min kaikaiyi kawai nake sosawa ta cikin bargo saboda Kar su Saifullahi su ga yadda nake susa ko a yanzu ma ji na nake a jike nasani ruwan nan mai wari ke zubo min.
Shigowar Nusrah d'akin yasa na bud'e idona bata yi wata wata ba ta fado kaina tana "Umma Mai ya Same ki haka Kinga yadda kika dawo"??
Yaya Abu ce tayi magana da bata iya gaisuwa ba, Nusrah zubewa ta a kasa ta hau bawa yaya abu hakuri akan bata lura ita bane.
Ganin hankalin Nusrah ya tashi sosai har tana na tashi muje asibiti yasa na daure na Mik'e zaune Ina k'ok'arin boye halin da nake ciki,abincin da Yaya abu ta kawo min na dauka duk da nasan ba iya ci Zan ba haka. Na fara tusawa ita kuwa tayi waje tana ko nifa Ina ganin ta fita na kalli su Saifullahi Ina su bamu waje magana Zan Yi da Nusrah.
Nusrah gadon ta hau sosai ta zauna gabad'aya hankalin ta na kaina,ni kuwa Ina ganin ba kowa na rushe da kuka,Nusrah hankali a tashe ta ruko hannuna tana "Umma dan Allah mai ke faruwa ne ya naganki haka kamar mara lafiya"?
"Nusrah Abban ku ya kasheni Da raina"
Nusrah Abbanku ya gama Dani....
" Umma mai Abban namu ya miki ?wani abu yayi"?
Ina k'ok'arin magana na jiyo muryar Abban Nusrah a palo yana magana dasu Saifullahi dake mi shi bayanin rashin lafiyata na rufe ido na da sauri da naji ya nufo dakina a duniya idan da wanda na mugun tsana Abban Nusrah ne,Nusrah kuwa itama fuskantar da tayi da maganar bana so nayi saboda tahowar sa d'akin yasa tayi shiru ta kawo hannun ta jikina tana "Umma jikin ki zafi ko asibiti zamu je"?
Ido na na Kara rufewa Ina danne zuciyata a
daidai lokacin da Ya shigo d'akin dan ji nake kamar na tashi na cakumi wuyan rigar sa na tona masa asiri a gaban kowa da kowa,amma tuna idan ban daure ba Yesmeen zan jefa a matsala yasa na ringa danna zuciyata,Ina jin Nusrah na gaishe shi ya amsa Yana "Tun yaushe kika zo wai jikin nata ne har yanzu ai da kun kirani a waya nazo na Kai ta asibiti"
Ya zauna a gefen gadon tare da yaye bargon jikina ya tab'a goshina Yana "Sannu Sajeeda ki tashi muje Asibiti"
Duk yadda naso na daure kasawa nayi sai da na ture hannun sa Ina Jin wani mugun bakin ciki na rufeni,wai ni zai kai asibiti bayan ya riga da yasan mai ke damuna ya riga da yasan shi ne silar kwanciyata ya bada ni a kungiyar su"
Da wanan tunanin na fara kuka idona a rufe dan bana so na bud'e ido na ganshi, gefena ma da naji shi a zaune ji nake kamar wuta yake huro min.
Ina Jin sa ya mik'e tsaye Yana "Sajeeda kina da matsala ke fa ba yarinya bace abu kad'an sai ki fara kuka,ko Nusrah bazata yi wanan abinda kike ba ki tashi mu tafi asibiti
Nusrah taimaka mata ta shirya na Kai ta asibiti bari na dan watsa ruwa nazo mu tafi"
Daga haka yasa Kai ya fice daga d'akin sai da naji fitarsa na bud'e idona Nusrah kuwa tana ganin ya fita ta tsugunna a gabana tana "Umma hankalina ya kasa kwanciya mai Abba ya miki"?
"Zan fada miki Amma ba yanzu ba"
Gyada kanta tayi ta mik'e tayi waje tana "Ban ga Yesmeen ba tunda nazo ko bata nan ne"?
Bance Mata komai ba har ta fice daga d'akin,nasan yanzu zata dawo tana koke koke,mintuna da fitar ta sai gata ta dawo tana "Umma Aiken Yesmeen ki ka yi ne banganta a d'akin ba"?
Ji nayi gabana yayi mugun faduwa duk da azabar da nake ji sai da na tashi tsaye ba dai guduwa Yesmeen tayi ba.
"Bangane baki ganta a d'akin ba Yesmeen Ina zata je ita da bata gani"
Nayi waje da sauri Ina Neman hantsilawa dan ko kad'an bani da kwari,idan kuwa har Yesmeen guduwa tayi ba abinda zai hana yau na tonawa Abban Nusrah asiri.
Koda na fita a Palo na tarar da Yaya Abu da Asmau suna kallo,daga can daki Kuma Ina jiyo muryar su Saifullahi.
D'akin Yesmeen din na nufa Koda na Shiga ba kowa na lek'a bandakin bata nan.
Na fito daga d'akin da sauri Nusrah na biye dani tana ta tambayata Kamar ya Yesmeen bata gani,Ina ga su Saifullahi basu Kai ga gaya Mata ba.
Ina fito wa palon na tsaya a gaban su Yaya Abu Ina "Yaya Abu Ina Yesmeen take ban ganta a d'akin ta ba"?
"Kamar ya baki ganta a d'akin ta ba? A can muka barota a kwance yarinya ce ita da zamu ringa gadin ta?
"Wallahi bata d'akinta Yaya Abu"
"To ina zata je ita da bata gani Yaya Abu ta mik'e tana gyara daurin zaninta ta Kara da "Kai yarinya nan anyi tsinaniya tunda nazo gidanan take bani ciwon kai Ina zata je ita da ba gani take ba"
Jikina da ke balain rawa yasa na zube akan kujera na dafe kaina naso nayi waje amma kafafuna sunki bani hadin kai Yesmeen guduwa tayi,saboda tana tunanin zan fadawa Abban Nusrah ta fada min sirrin sa,bayan na ce Mata ta zauna bazan nuna Masa ba ko a yanzu yadda zamu bar gidan nake tunani idan har na iya danne zuciyata ban nuna masa komai ba,na gudu nida yarana na fada musu dani Abban su yayi kudi,Abban Nusrah ya cutar dani ya tarwatsa min rayuwa yanzu gashi a garin tsoron sa Yesmeen ta gudu"
Fitowar Yaya Abu daga d'akin da Yaya Asmau yayi daidai da fitowar Abban Nusrah daga d'akin sa.
Yaya Abu cikin sallati ta hau tafa hannuwa tana "wlh bata d'akin Ina zata je ita da bata gani,kiga muna zaune yarinya zata tona Mana asiri"
"Mai yake faruwa ne yaya Abu"?
Abban Nusrah yace a daidai lokacin daya karaso tsakiyar palon Nusrah kuwa kuka ta fara zundumawa tana "Yesmeen din ce bata gani bangane bata gani ba mai ya samu idon ta ta daina gani"?
Dagowa nayi Ina kallon Abban Nusrah da yake kallon Yaya abu dake ta zuba Masa bayanin yadda nake dagawa kaina hankali saboda Yesmeen tunda ya fita muka shige daka da Yesmeen na saka ta a gaba Ina kuka nabi na takura kaina gashi nan ita nema take ta tona min asiri.
Kallon sa kawai nake yadda yake tsaye kamar mutum nan kuwa dabba ne saboda kudi ya kwanta da Kare,hararo yadda ya kwanta da Karen kawai nake,wane irin zuciya ne a kirjin Abban Nusrah har mai yake nema a gidan duniya da har zai nemi yayi kudi ta hanyar haram har saboda kudi ya kwanta da dabba ya zo ya kwanta dani,Karen da muke Jin labarin a jikinsu aka fara samo Aids da wanan tunanin na rushe da kuka wata kila ba iya wanan cutar da nake gani ya saka min ba kila nima ya saka min AIDS din tunda naga kafafuna da hannayena na rama,Naman jikina ma gani nayi yana karewa Abban Nusrah so yake na mutu ya fara sabon rayuwa da ciwo Wanda ka amincewa ka d'auki shi a matsayin abokin rayuwa Wanda yardar da ka mishi yasa kake tunanin shi mai kare ka ne daga duk wani Abu da zai sameka sai gashi uban yayana da kansa ya cutar dani saboda ya samu duniya duk wahalar da na sha dashi a rayuwa,sakayar da zai min kenan kuka kawai nake Ina kallon sa