← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 80

Sashe 2

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abban Nusrah mai na maka kake fushi dani?a iya sanina ba abinda na maka Abban Nusrah wani bak'on al amari ka zo min dashi wanda ni nasan kasan haramun ne,dagani har Kai ba yara bane,ga ta hanyar da Allah ya hallata ma ka neme ni ka samu nutsuwa dani,amma dare daya Abban Nusrah kace zaka neme ni ta baya ta Inda Allah ya haramta kaga dan na k'i bin umarnin ka bai Kamata kayi fushi dani ba dan babu biyayya a sabawa Allah,bansan waye ya baka wanan gurguwar shawarar ba,iya sanina duk wayanda kake mu'ammalla dasu ba mutanen banza bane bansan waye ya ce ma ka gwada ta baya zaka ji dadi ba,taya wajen da ake kashi yayi dadi Ni dai kayi hakuri zan iya k'ok'arina dan na gamsar da Kai amma ban da ta baya"

Sai a lokacin ya dago ya kalleni ya ajiye takarda a gefen pillo Yana "Sajeeda duk abinda nake yi Ina sane tsawon zamana dake Ina ga baki tab'a ganin na neme ki ta baya ba,gwaji ne kawai nake so nayi naji abinda ake ji ba wani abu ba,amma tunda kin nuna bakya so shikenan ba zan Kara nema ba,na dauka duk abinda nake so matsawar bai fi karfin ki ba Zaki iya min"

"Wanan yafi karfina ne Kabiru shi yasa bazan iya ba abinda akace haramun ne ban ga dalilin da zai saka kace zaka gwada ba mu fa ba Yara bane idan muna raye ma wani shekara zaka gan mu da jika"

"Ya isa haka Sajeeda Kinga na Kara neman naki ne yanzu"!?

Shiru nayi Ina kallon sa yaja siririn tsaki ya kwanta ya juya min baya.

Nace masa ga abincin sa yace bazai ci ba.

Wasa Wasa mijina ya fara fushi dani dan naki bari ya nemeni ta baya Wanda zuwa yanzu lamarin nasa ya fara bani tsoro ko Yaya na shawo kansa asan na faranta Masa rai, a madadin yayi ta hanya da ya dace sai naga Yana neman tura jikinsa bayana.

Halin nan daya bijiro min dashi ya matukar daga min hankali dan kullum cikin fada mu ke.

Gashi mu ba Yara ba ballantana nace wani Zan nemi shawarar sa Wanda ni nasan mu ya Kamata ma mu ringa hana wasu ba dai mu ba.

Ko a yanzu da ido nake bin sa har ya gama shiryawa bai ce min komai ba ya fice daga dakin na sauke ajiyar zuciya ina tunanin mafita Kiran Nusrah daya shigo wayata ya katse min tunanin da nake.

Ina dagawa muka gaisa kamar yanda muka saba Inda take sanar min zuwan ta anjima na ajiye mata dambu na saki murmushi Ina sai ta zo.

Na Mik'e nayi waje dan na fadawa Yesmeen zuwan Nusrah duk da nasan kila ma sun yi waya.

Ina fitowa naga Abban Nusrah a zaune a doguwar kujera duk a tunanina Yama fita ashe fitowa yayi ya zauna a palon.

Yesmeen kuma na tsugunne a gabansa tana hada mi shi shayi.

Fitowa ta yasa ta dago tana "Umma Ina kwana"

Zama nayi a gefen shi fuskata d'auke da faraa na hau amsa gaisuwar ta ko kad'an bana so yarana su fahimci wani abu.

Tana gama hada masa ta mike tana bari ta d'auko kofi ta hado min shayin na girgiza mata kai akan ta bar shi sai anjima.

KABIR

Da ido ya bi Yesmeen din har ta shige d'aki ya d'auki shayin ya fara kurba a hankali har ya shanye Yana Jin idon Sajeeda a kansa.

Yana dire kofin ya mik'e yayi waje batare da ya tsaya Jin mai Sajeeda ke cewa ba.

Yana fita ya haye machine din sa bai zame ko'ina ba sai wani hadadden gida da fadar haduwar sa bata Baki ne.

Mai gadi ya riga da ya gane shi hakane yasa ya bude masa ya shige da machine dinsa kansa tsaye ya nufi d'akin saukar baki dake farfajiyar gidan.

Kamar yanda yayi tsamani a zaune ya tarar da Alhaji Rabiu a cikin dakakiyar shaddarsa dake ta kyalli kamar madubi.

Sai da Kabiru ya sama wa kansa wajen zama.

Alhaji Rabiu yace "An dace kuwa"?

Sai da Kabiru ya sauke ajiyar zuciya yace "wlh ba'a dace ba duk ta inda kake tunanin zan biyo mata na biyo mata wlh tak'i bani hadin kai"

Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana "Na fa san irin su haka suke da balain taurin kai Amma idan tasan wata ai bata San wata ba ka tashi muje wajen shugaba mu masa bayani"

Ya mik'e Yana k'ok'arin yin hanyar waje.

Kabiru yayi saurin dakatar dashi yana "Rabiu Ina kaunar matata tunda na yarda zan yi harkar nan zuciyata take cike da fargaba da tsoro ko bacci bana iya yi dan Allah muje wajen shugaba ka fada masa ya duba min ko zan iya yi da wata na samu biyan bukatata ba sai Sajeeda ba.

"Ikon Allah toh wa zaka samo"?

"Akwai yar kanwarta da nake rike da ita da ita nake so na samu biyan bukatar tawa"

"Bani da ta cewa muje daga can muji ko zai yu......

Hmmm

*RUFAFFEN SIRRI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Page 2*

Kabiru har suka je Suka dawo bai iya magana ba sabida kasan zuciyarsa cike take da tsoro,ji yake Kamar ba zai iya ba dokokin da Abubuwan da akace yayi sun masa yawa da tsauri,a hankali ya Kai dubansa wajen Alhaji Rabiu da ya kasance abokinsa tun primary da a lokacin ya fi shi k'ok'ari nesa ba kusa ba dan shi yake zuwa na karshe ma a ajinsu da kuwa suka gama primary bai Kara saka shi a idonsa ba,bai Kara jin labarin sa ba sai a shekara biyu da suka wuce ya had'u dashi,sai da yayi da gaske ya gane shi sabida yanda ya dawo fari kal sabida yadda hutu da Jin dadi suka zauna masa tashin farko,kyautar dubu dari ya Masa,ya hada da bashi lambarsa,duk kalar rayuwar da yaso tun Yana karami na rayuwar Jin dadi shi yake gani a wajen Rabiu.

Gashi ya girma zai iya cewa ya d'auko tsufa tunda Yana dab da aurar da 'yar cikin sa duk bai samu cikar burin nasa ba.

Tuni yaji ya kwadaitu da san yayi kudin fiye ma da da hakane yasa ya makalewa Alhaji Rabiu ko zai taimaka Masa ya sama mi shi aiki irin nashi da shi ma zai samu kudin.

A haka Alhaji Rabiu ya ringa masa yawo da hankali Yana kasuwanci yake yi sai da yayi dagaske Rabiu ya fito ya nuna masa ta hanyar da ya samu kudin sa,idan har yaga zai iya.

Tsayuwar motar Alhaji Rabiu a wani tamfatsatsen gidansa da matarsa ta uku take ciki ya katse tunanin da Kabiru ya tafi.

Yayi horn Mai gadi ya bud'e masa.

Tun da suka shiga gidan Kabiru ya saki baki da hanci Yana kallon Aljannar duniya,maganar shugaba na dawo Masa a kunne,"zaka yi kudi, idan nace ma kudi,Ina nufin kazamin kudin da zai saka duniya ta san ka zaka ji dadin rayuwar ka zaka bar wa yayanka tarin dukiya ka tabbata baka tsallake duk sharuddan da aka gindaya ma ba daga yanzu kafin wata ukun zaka fara dandana arziki amma ka iya takun ka"

"Sauko mu Shiga daga ciki ka gaisa da Aseeya"

Muryar Alhaji Rabiu ya katse Masa tunanin da yake.

"Rabiu anya zan iya wlh bansan mai yasa nake Jin bazan iya ba gani nake za'a iya gano ni da wuri bazan iya yiwa Sajeeda haka ba"

Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana "Tunda na iya yiwa Sakeena Yar uwata haka Kai ma zaka iya bafa kasheta zaka yi ba,a cikin kankanin lokaci Kai ma zaka zama kamar ni,kayi amfani da abinda kake dashi ka samu cikar burin ka,kar ka karaya abokina muje dai daga ciki indai Muka bi komai a yanda Muka tsara wlh baza'a samu matsala ba"

Kabiru gyada Kai yayi duk da a kasan zuciyarsa gani yake bazai iya ba.

Yabi bayan Alhaji Rabiu yana karewa gidan kallo,hararo kansa kawai yake a matsayin Rabiun ya mallaki irin wanan gidan,ya ginawa su Saifullahi manya manyan gida daidai da Nusrah ma sai ya mallaka Mata gida da mota, tuni yaji ya Kara kwadaituwa da ya samu kudin,a lokacin da suka Shiga palon da Kamar a kasar waje suke da suka shiga.

A lokacin kuwa daya zauna kalle kalle ya cigaba da yi Alhaji Rabiu ya haye Sama minti biyar a tsakani sai gashi ya sauko ya zauna.

Kafin kace me masu aiki sun cika gabansu da kayan ciye ciye.

Alhaji Rabiu kuwa sai murmushi yake dayaga yanda Kabiru ke hadiyar yawu.

Takun takalmin Aseeya matar Alhaji Rabiu dake saukowa daga saman benen yasa Kabiru maida hankalin sa wajen benen.

Yarinya ce bata fi saar Nusrah Yar sa ba ko zata girmi Nusrah bazai fi da shekara biyu ba,kyakyawa ce ta ajin karshe tamkar ita tayi kanta fuskarta d'auke da murmushi,har ta karaso gefen Alhaji Rabiu ta zauna ta fara gaida Kabiru da ya hau washe baki kasan ransa Yana ta mamakin yanda yarinya karama ta yarda ta auri sa'an mahaifinta.

Bayan sun gama gaisawa ta mik'e ta koma sama,

"Rabiu yanzu Wanan Yar yarinyar ka Aura"?

Murmushi Alhaji Rabiu ya saki ya zuba Lemo a kofi sai da ya kurba ya ajiye ya kalli Kabiru Yana "Shekara uku kenan da Auren mu Kuma ta wajen nan da matarka ta hana ka ta wajen nake neman ta"

Ido Kabiru ya zaro waje Yana "Kuma sai ta yarda"?

"Kwarai kuwa ba Ina da kudi ba,a yanzu da kake ganin ta bama tasan Inda zata Kai kudi ba kaga kuwa ko dan su dole ta yarda da bukatata dan sai da na tabbata Iyayenta irin talakawan nan ne sosai,dan a garin talla ma na hadu da ita,na cikata da kudi na cika Iyayenta da kudi, basu da gidan kansu kafin na aureta yanzu kuwa har yayyenta maza ba Wanda ban siyawa gida ba tana morata a zahiri Ina morarta a badini"

Sai yayi kasa da murya

"Tana samun ciki take b'ari na riga na bada mahaifarta"

Ni kuwa Ina nan da yayana bakwai suna jin dadin su a waje"

Kabiru mamaki ya sa ya kasa ma magana dan sai a yanzu ya gane da rabon amaryar kudin sa ke Kara hab'aka uwar yayan sa kuma ta masa silar kudin.
Chapter 2 · 0% Book details