← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 80

Sashe 16

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki cikani Sajeeda na fasa yi Mata komai Karen da na ce Miki ba nawa bane na abokina ne Yesmeen ta sakawa shinkafar bera baki ga yadda abokina ke ji da Karen nan ba dazu ma sai da muka yi waya na jadadda Masa zan maida Masa gobe yarinyar nan da ta tashi ta zubawa Karen shinkafar bera"

Kabiru yace cikin dacin zuciya idonsa na Kara cikowa da ruwa dan dauriya kawai yake shi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki da sai da komai yazo masa karshe Yesmeen ta Masa haka, duk saboda cikar burin sa yak'i sallah har tsawon sati daya,yayi wanka da jini,ya Sha jini yaje makabarta karfe biyun dare ya binne abu sai da ya zo matakin karshe Yesmeen ta kashe shi.

Hawaye suka Kara zubo masa daya tuna kalar wahalar da ya Sha har ciwo yaji a garin gudu dayaje makabarta binne abu,

Sajeeda kuwa cak ta tsaya tana kallon shi a lokacin da taga Wai duk wanan abin saboda Karen da ya kawo ne,tsabar mamaki kasa ma matsowa tayi Saboda yadda taga ya fice a hayyacin sa har da kuka,ko da dan cikinsa ne ya rasu iya tashin hankalin da zai nuna kenan, saboda Karen dama yake kirarin kashe Yesmeen har da kukansa.?

Kabiru hanyar waje yayi Yana ji Ina ma mafarki yake yi ya Kara yin bayan gida yana kallon Karen,ko kashe Yesmeen yayi yanzu baya Jin zai hucce,zai so ya azabtar da Yesmeen,zai so yaga Yesmeen ta Sha wahala kafin ma ya kasheta.

Da Jan kafa ya juya yayi hanyar waje dan wajen Rabiu zaije ya fada Masa duk Abubuwan da suka faru.

Sajeeda kuwa har ya fice mamaki bai saketa ba kanta yayi mugun daurewa da wanan al amari dama duk wanan tashin hankalin akan Karen da Kabiru ya kawo ne tana Jin motsin fitarsa.

Ta buga k'ofar toilet din tana "ki bud'e Yesmeen ya fita"

Yesmeen bud'e k'ofar tayi har lokacin jikinta rawa yake idonta yayi jajjur saboda kukan da ta Sha.

Koda ta fito Sajeeda ido ta zuba mata dan bama tasan tunanin da za tayi ba a yanzu

A hankali ta Kira sunan Yesmeen tana "Yesmeen da gaske ne ke Kika kashe Karen da Abban ku ya kawo"?

Yesmeen bata iya magana ba dan batasan yadda zata yiwa Sajeeda bayani ba tunda idan har ta fada Mata ita ta kashe Karen sai ta tambayeta dalili.

"Yesmeen Mai yasa Kika kashe Karen Wai Mai ke faruwane na kasa gane abinda ke faruwa Mai yasa Kika kashe karen"?

"Umma yadda kike mafarki da karen nan haka nake mafarki da Karen ko bacci bana iya yi, haka Zan ta mafarki ya shigo Yana k'ok'awa dani idan kinzo cetona sai ya koma kanki hankalina ya kasa kwanciya da Karen a gidan nan shi yasa na saka masa maganin b'era"

Yesmeen ta karashe tana mamakin yadda ta samu tayiwa Sajeeda karya dan bazata iya fitowa ta fadawa Sajeeda gaskiyar abinda ya faru ba dan da ace duk a hirar su ta tab'a zargin kabirun ne sai ta fada Mata,bata taba zargin sa ba tafi zargin abokinsa idan ta fito ta fada mata abinda ke faruwa ba lailai ta fahimceta ko ta yarda da ita ba"

"Da kinsani baki kashe shi ba Yesmeen tunda na fada miki gobe yace zai maida Karen wajen Mai shi,ransa yayi mugun b'aci da abinda kika yi,ni tunda nake dashi ma ban tab'a ganin bacin ransa haka ba abin ya bani mamaki akan Kare hankalin sa ya tashi haka har da kukan sa wlh har yanzu mamaki nake na d'auka wani mugun abu Kika masa Allah dai ya kyauta Yesmeen abinda za'ayi ki hada kayan ki kala biyu kije wajen hajiya kareema kice nace kiyi kwana biyu zuwa lokacin nasan Abban ku ya hucce sai na Miki waya ki dawo"

Yesmeen jiki na rawa ta hau hada kayanta dan ko Sajeeda bata ce ta tafi wani wajen ba bata isa ta kwana a gidan ba,tasan Kabiru bazai tab'a barin ta ba dole zai mata wani Abu,idan har zai iya cutar da Sajeeda matar sa uwar yayansa wacce ita da bazai cutar da ita ba.

Tana gama hada kayan ta Sajeeda ta d'auko kudi ta bata akan tayi kudin mota dan hajiya kareema kawar tace a Kuma tsohon unguwar su take.

Koda ta karba har tazo fita ta dawo baya tana kallon Sajeeda ji take Kamar ta rik'e hannun ta ta fada Mata duk abinda ke faruwa,sau uku tana gwada bud'e bakin ta dan ta fadawa Sajeeda abinda ke faruwa sai taji ta kasa,haka kawai hawaye ya hau zubo mata gani take idan ta tafi Kabiru zai cutar da ita amma ba yadda za tayi.

Sajeeda dungure Mata Kai tayi tana "ke Kika jawowa kanki ai da kinyi hakuri da gobe zai fitar mana da Karen daga gidanan kije idan na samu na shawo Kan sa yau Zan kiraki ki dawo yau gidan wani iri zai yi idan bakya Nan"

"Umma Dan Allah ki dage da Addu'a umma Ina yawan mafarki marasa dadi umma karki yi wasa da Addu'a Kamar yadda kike zargin abokin Abba nima na fara zargin sa dan Allah umma kiringa addua kina yi mana"

Murmushi Sajeeda ta saki tana "Ina Addu'a yata in Sha Allah ba abinda ya Isa ya mana har sadaka zan fara yi dan sadaka maganin masifa ce in Sha Allah ba abinda zai iya yi mana idan tarayyar sa da Abban ku ba alheri bane Ina rokon Allah ya kawo karshen abotar su Allah ya Miki albarka"

Ameen umma

Yesmeen tace tana jin zuciyarta wani iri bazata yafewa kanta ba idan har wani Abu ya samu Sajeeda Anya bazata tsaya ta fada Mata gaskiya ba Mai yasa Sajeeda ta kasa d'aukar haske a duk abinda ya faru,daga tashin hankalin da Kabiru ya nuna na mutuwar Karen ya Kamata ace Sajeeda ta gane wani Abu amma ta kasa ganewa.

Har bakin gate Sajeeda ta rakata sai tayi kamar zata mata magana sai ta kasa har Sajeeda ta maida k'ofar gate din ta rufe.

Banda bata san ta dagawa Sajeeda hankali ba abinda zai dawo da ita gidan kabiru ba abinda ya faranta Mata sama da karen da ta kashe dan tasan ta wargaza komai a yanzu Kuma addua zata dage ba dare ba rana.

Kafin ta samu abun Hawa ta tsaya a hanya ta siyi alewa duk yaron da tagani sai ta bashi.

Sajeeda

Har karfe goma na dare Abban Nusrah bai dawo ba zuwa yanzu sai naji hankalina ya tashi na kasa gane Mai yake damun Abban Nusrah hakika uban yayana ya canza akwai wani boyayyen al amari,tunda Yesmeen ta tafi na fara mazartar maganganun ta sai naga kamar akwai abinda take b'oyemin haka kawai bazata ce na ringa addua ba,yadda Abban Nusrah ya nuna tashin hankalin sa akan Kare har yanzu kaina a daure yake.

Haka tunani ya cike min zuciya na rasa tunanin ma da ya kamata nayi.

Abban Nusrah bai dawo gidan ba sai wajen Sha biyu na dare na dauka zai dawo fuskarsa a hade sai naga fuskarsa a sake ya dawo.

Bai nuna wani abu ba Kamar ma wani Abu bai faru ba har na bashi abincin sa ya fara ci Yana fada min dalilin daya sa bai dawo da wuri ba Kaya ya Kai wani kauye,

Ni kuwa ganin sam bai nuna wani abu ba yasa na fara magana cikin kwantar da murya Ina "Abban Nusrah dan Allah kayi hakuri da abinda Yesmeen ta maka na hadaka da girman Allah"

"Haba haba ba komai fa ni har na manta ma dan dama abokin nawa nake ji Koda naje wajen sa na fada Masa abinda ya faru bai wani nuna bacin ransa ba shi ya sa na sauko dama shi nake ji ya bani aron Kare na kashe masa,Amma a yanzu na sake gano wani goben nan Zan d'auko bai Kai Wanda ya mutu girma ba muna bukatar Kare a gidanan"

"Abban Nusrah da ma hakura kayi da kawo Mana Kare cikin gidanan malaikun Rahama basa shiga gidan da ake da Kare wallahi"

"Karki damu wlh wanan Bai Kai wancan girma ba Mai kyau ne Sajeeda gidanan fa sai da Kare saboda gadi nidai fatana ki jawa yarki kunne Kar ta sake ta cutar min da Karen nan wlh idan ta tab'a wanan ba kyalle ta Zan yi ba"

"Ai bama ta gidanan saboda ta tsorata saboda yadda kayi fushi shi ne nace sai ka dawo na baka hakuri naga ka hucce sai ta dawo"

"Haba ba komai tayi dawowar ta"

"Na gode Abban Nusrah"

Hira muka Dan tab'a har bacci yayi awon gaba dani.

Kabiru

Wajen karfe biyun dare ya tashi ya fice daga d'akin yayi waje ba jima wa ya dawo cikin sand'a ya nufi d'akin Yesmeen Yana murnar yadda komai yazo masa da mugun sauki zai aiwatar da aikinsa Yesmeen bata nan.

Yana Shiga d'akin Yesmeen ya taka kujera ya cire glass din fitilar dakinta Yana zuba murmushin mugun ta mulmulen abunda shugaba ya bashi ya saka a fitilar kwan ya maida glass din Kamar Bai saka komai ba ya kashe fitilar Yana "ke da gani Yesmeen sai dai a lahira ke da gani sai dai idan baki dawo cikin gidan nan kin kunna fitilar nan ba shegiya tsinaniya"

Ya fito daga d'akin ya rufo k'ofar ya koma d'akin Sajeeda.

Washegari da yamma sai gashi ya kawo wani Karen sai dai wanan Karen bai Kai Wanda ya mutu muni ba.

Sajeeda kanta da ta ga Karen bata wani ji ta tsorata ba da sassafe ta kira Yesmeen akan ta dawo Abban ta ya hakura.

Wajen karfe biyu ta dawo gidan Dan haka kawai taji ta matsu ta dawo dan Bata so Kabiru yayi wa Sajeeda wani abu.

A lokacin da Kabiru ya dawo da hijabin ta har kasa ta fita ta gaishe shi.

Bai nuna mata komai ba ya amsa cikin faraa ta Kara bashi hakurin abinda ta masa ya saki murmushi Yana "kinci darajar abokina ya hakura bai yi fushi ba yanzu ma na sake kawo wani Karen saura ki Kara kashe min shi"

Yesmeen sunkuyar da kanta tayi dan tasan akwai mugun abun da yake so ya aikata
Chapter 16 · 0% Book details