← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 80

Sashe 41

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan da wanan zai samu yayi abinda zai yi dan yasan Sajeeda na can kila ta kasa tashi duk da bai lekata ba

Dubu hamsin ya d'auko daga dakinsa ya koma d'akin Yesmeen ya mikawa Yaya Asmau su kuwa sai godiya suke masa yace ba komai ya koma palo ya zauna.

Sai da sukayi wanka Suka karya suka fito Suka leka Sajeeda dake ta numfarfashi idonta jajjur dan ko bacci bata yi ba.

Sannu kawai Suka mata suna sauri suke zasu je kasuwa su dawo ko magana basu bari tayi ba Suka yi waje.

Kabiru dake labe a daki Yana ganin sun fita bai yi wata wata ba ya nufi d'akin yesmeen.....

Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya da yanmata albishir gareku

BONONZA; BONONZA;BONONZA;

Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K

MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 14*

Sajeeda bandakin Yesmeen ta shige da sauri ta hau susa a yanzu ba iya kaikaiyin take ji ba har ruwa mai kalar ruwan ke jikata Kamar tana period ko da take tsaye tana iya Jin yadda ruwan ke wari,bata san lokacin da ta saki sallati jikinta na rawa ba taya zaace a jikinta wanan ruwan ke fita,tana Jin Yesmeen na buga k'ofa tayi saurin toshe bakinta tana k'ok'arin maida hawayen dake zubo mata, dan bazata iya kallon Yesmeen tace mata ga halin da take ciki ba bata Jin zata ma iya jiran Kabiru a yanzu zata shirya ta tafi asibiti tana daga bandaki tace wa Yesmeen taje Palo su Yaya abu sun zo.

Yesmeen kuwa waje tayi da jajjayen idonta da ta murzawa rob,dan dagaske take so ta nuna ta samu matsalar ido,tunda har kau da ita kawai Kabiru ke so yayi,idan tace ma zata gudu,kabiru zai iya sawa a nemota,gwara ta makance din, hankalin ta bai Kara tashi ba sai da taji Sajeeda na ce mata bata Jin dadi ko bata fada ba kana ganin ta kasan ba daidai take ba,Kamar ta samu wajen da ba kowa tayi ta kukan tausayin Sajeeda Sam bata cancanci haka daga wajen Kabiru ba ko ya ta rufe idonta yadda Kabiru ke saduwa da Kare ke fado mata ta kasa goge abinda ta gani a kanta,duk akan neman duniya Kabiru ya cutar da Sajeeda,

Sanin halin Yaya Abu yasa ta cigaba da mitsitsika idonta dan tana da saa ido ba kadan ba tana tsoron ta gano ba ciwon ido take ba"

Tana zuwa ta zub'e a kasa ta hau gaishe su

Suka amsa gaisuwar Yaya abu na kare Mata kallo ta jefa Mata tambayar mai ya samu idonta tana k'ok'arin magana Kabiru ya shigo da sallama hannun sa d'auke da ledoji idonsa akan Yesmeen yasan gobe uwar haka Yesmeen sai dai ta Kare rayuwar ta a duhu.

Ledojin da Yaya Abu ta gani a hannun Kabirun ya d'auke Mata hankali daga Kan Yesmeen,Yesmeen ta mik'e tsaye tana k'ok'arin komawa daki,dan dole sai ta nuna tana balain Jin jiki, Kabiru kuwa yace "Wai har yanzu idon naki ne"?

"Eee Abba wlh zugi idona ke min dusu dusu nake gani"

"Yanzu nake tambayarta mai ya samu idonta yayi ja haka"?
Yaya Abu tace tana satar kallon ledojin da Kabiru ya shigo dasu

Wai Abu ya fado mata a ido Ina ga gobe idan bata ji sauki ba dole taje Asibiti"

Kabiru yace Yana ajiye ledojin hannun sa Yesmeen Kuma ta nufi d'akin ta a daidai lokacin da Sajeeda ta fito daga bandaki tana Jin wani irin zugi a kasanta dan a garin susa har ciwo taji wa kanta.

Ganin Kabiru ya dawo yasa ta daure ta d'auko ledojin ta nufi kitchen ta juye fried rice da Kabiru ya siyo da yawa ta zuba a flask ta zuba musu a plate ta Kai musu d'akin Yesmeen dan gani take sai sun fi sakewa acan duk da tasan Yaya Abu ba abinda ya shafeta zata iya ci a gaban kabirun har da loma,ko a yanzu kafin ta Kai musu abincin Hira kawai take da Kabiru tana sainting haduwar gidan.

Ita Kuma abinda ta tsana kenan,dan yanda take yiwa Kabirun yasa ya raina ta ba wani girmama ta yake a matsayin yayarta ba.

D'akin Yesmeen din ma da ta Kai su haka tayi ta kalle kalle tana fadar haduwar d'akin.

Sajeeda kuwa ta barsu a d'akin tana zata je asibiti ta dawo.

Ko da ta fito daga d'akin gani tayi Kabiru ya shirya a cikin dakakken shadda da kana kallon shaddar kasan Mai balain tsada ce,sai taga gabad'aya kabirun ya canza kamar bashi ba,ganinta ya saka ya tsaya sai da ta karasa wajen sa ya fara magana Yana "Zan dan fita yanzu nan na dawo wani Kaya muke so a tura can cotonou"

"Yanzu Abban Nusrah ba asibiti kace zaka kaini ba,kasan mai nake ji a jikina kuwa Abban Nusrah so kake sai na fara susa a gaban mutane zaka kaini asibiti har yanzu ruwa mai doyi zubo min yake"

"Yanzu dan Allah ya ki ke so nayi ga mahimmin abu da nace miki zanje nayi,yanzu kije ki Kara Shan maganin ki gobe da sassafe Zan Kai ki asibiti ni bansan Ina Kika kwasowa kanki wanan abin ba bari naje na dawo Kinga ma bai Kamata ki fita da baki a gidan ba"

Daga Haka ya yi hanyar fita

Sajeeda ta bi shi da ido,tana Jin wani irin takaici na rufeta,har ace tana cikin irin wanan tashin hankalin Kabiru bai wani damu ba,ta shige daki ta kwanta ta fara matsawa kanta da tunanin yadda akayi ta wayi gari da wanan masifar a jikinta.

Duk yadda taso ta gano ta kasa ganewa sai ta d'auko zargin kabiru ne ya goga mata sai ta fasa dan iya sanin ta baya neman matan banza bata sani ba ko haduwa da abokinsa da yake kirarin ya canza Masa rayuwa ya jefa shi a cikin halin banza,

Sai da ta sake wanke jikinta ta canza komai na jikinta ta koma d'akin Yesmeen hira Asmau da Yaya Abu kawai suke Yesmeen na rabe a gefe da jajjayen ido,duk minti minti sai ta sosa idon, Sajeeda sai sannu take jera mata,yaya abu kuwa sai tabe baki tayi tana ciwon idon Yesmeen take yiwa wanan rakin Sajeeda ma ke biyeta taja saki tana Kara karewa d'akin Yesmeen kallo tana "Allah ya baki Sajeeda kiga Wai hadadden d'akin nan ne d'akin Yesmeen har yanzu baki fada min yadda aka yi mijinki ya kudance haka ba"?

Murmushin yake Sajeeda tayi tana "Yaya Abu naga kina hira dashi idan ya dawo ki tambaye shi kiji"

"Karki gaya min magana mana kawai dan na tambaye ki ya aka yi mijinki ya samu kudi haka shine zaki gaya min magana"

"Allah ya baki hakuri Yaya Abu wlh ba haka bane idan na fada Miki yadda yayi kudin ba lailai ki yarda ba Kamar yadda har yanzu nake cikin fargabar yadda yayi kudinsa dare daya,Wai wani abokinsa ne Rabiu Yana da balain kudi,abokin sa ne tun primary shine Suka hadu watanin da suka wuce shine ya sama mishi aiki a company sa wanan gidan ma da kike gani shi ya bamu kyauta,baki ga yadda yake facaka da kudi ba,shi yasa nake a tsorace dan hidimar tayi yawa gani nake kamar abokin nasa ba ta hanyar arizki ya samu kudinsa ba dan abin yayi yawa kudi da aka nema ta halal bazai yu a ringa kashe su kamar baa San zafin su ba,amma duk yadda naso nunawa Abban Nusrah yayi baya da abokin nasa yak'i yarda idonsa ya riga da ya rufe"

Sallati Yaya Abu ta saka tana tafa hannuwa sai da ta gama ta fara magana tana "Sajeeda kamar anyi Miki baki Allah ya muku wanan arzikin ki wani tsaya kwokwanto ke Ina ruwanki da yadda abokin nasa ke samun kudinsa,ko fashi yake yi Ina ruwan ki lokacin arzikin ku ne yazo gwara ki saki jiki ki more arziki nidai idan mijinki ya dawo zan roke shi arziki na zauna da ku yadda na ga wanan daula ba abinda zai maidani gida tunda ni ba aure ba,ba komai ba idan Allah yasoni da arziki sai kiga nima na hadu da Mai kudin

Murmushin yake kawai Sajeeda tayi dan bata san mai zata cewa Yaya Abu ba ko lokacin da basuyi kudi ba tana zuwa ta shafe wata a gidanta a zaune balle yanzu da Kabiru yayi kudi.

Kabiru
Chapter 41 · 0% Book details