← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 80

Sashe 21

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kabiru kuwa daskarewa yayi a tsaye Yana kallon Yesmeen idan ba yaudarar kansa zaiyi ba da dukan alamu fitilar Yesmeen ta kunna dan fitilar a kunne take,wani irin farincikin da ya dade bai ji ba ya tsinci kansa a ciki kamar yayi ta tsalle dan murna haka ya ringa ji,da shi kadai ne a d'akin ba abinda zai hana shi rawa take ya tafi tunanin abinda shugaban yace Masa "Indai ta kunna fitilar glass din ya fado zata ji yaji a idon ta,baza ta makance a take ba sai washegari idan ta tashi daga bacci zata daina gani saboda gudun zargi"

Da wanan tunanin yayi saurin nufar wajen da Yesmeen ke tsaye Sajeeda na ta san hure mata ido ita kuwa sai ihun idon ta yaji yake.

Sajeeda da hankalinta ya Kai kololuwa wajen tashi ta hau magana tana "Abban Nusrah ko asibiti zamu Kai ta taki fada Mana mai ya samu idon ta.

"Taya zamu kai ta asibiti bayan bata fada mana Mai ya samu idon ta ba sai ihun da ta cika wa mutane kunne dashi mai ya samu idon naki"?

Yesmeen idon ta ta cigaba da murzawa sai da Kabiru ya Kara daka mata tsawa dan ya tabbatar da zargin da yake yi

Ta fara magana tana
"Abba fitila na kunna shine glass din ya fado sai naji yaji ya shigar min ido,idona Kamar an watsa barkono"

"Sakarci ne kawai irin naki daga kunna fitila idon ki zai hau yaji ki wuce bandaki ki wanke fuskar ki"

"Abban Nusrah ko dai asibiti zamu Kai ta"

"Wane irin asibiti wai sai kace wani babban abu sakalci ne kawai irin na yarinya nan dalla wuce kije ki wanke idonki "

Kabiru yace a dan tsawace ya juya ya bar d'akin cikin tsananin murna da mamakin yadda akayi Yesmeen ta kunna fitilar a yau yake Shirin b'atar da ita sai gashi ta saukaka Masa aiki komai ya zo masa cikin sauki

Sajeeda kuwa bandakin taja Yesmeen ta hau wanke mata fuska Yesmeen na cigaba da ihun yaji,duk abinda Sajeeda take yi dauriya kawai take dan ba kwari ne da ita ba Koda Suka fito kasan murya Sajeeda ta hau magana tana "Dan Allah ki bar ihun Nan Yesmeen Kara daga min hankali kike ki barni naji da abinda ke damuna"

Yesmeen har lokacin murza idon ta take abinda taji Sajeeda tace yasa ta daina murza idon tana "Umma Baki da lafiya ne har yanzu?

"Bani da lafiya Yesmeen baki ga ko fitowa na kasa yi ba yau ihunki ne ya fito dani yanzu kin daina Jin yajin"

Kikifta ido Yesmeen ta hau yi tana "dishi dishi nake gani umma har yanzu Ina Jin yaji"

"Ba dole ba kin murza idon da yawa ki daina murzawa a hankali zaki ga kin daina gani dishi dishin,mamanki na hanya ma ta kirani a waya ki daure ki Shiga kitchen ki sama musu abu"

"Umma wlh bazan iya Shiga kitchen ba dusu dusu nake gani"

Sajeeda na k'ok'arin magana Kabiru da ya dawo dakin bayan ya gama waya da Rabiu yace "Ki barta Sajeeda zoki wuce ki kwanta itama ki barta tunda tace dishi dishi take gani,ai bazai Yu ta iya wani abu ba kafin su iso Zan samo musu abinda zasu ci ita Kuma idan na fita Zan samo Mata maganin ciwon ido Allah ya sauwake"

Bari nazo na kwashe glass din nan Kar wani yazo ya taka

Sajeeda yadda take Jin kaikaiyi yasa ta saurin mik'ewa duk da kamar ta zub'e saboda rashin kwari haka ta fice daga d'akin ta koma d'akinta ta hau susa tana kwalla

Kabiru kuwa Yana ganin fitar ta yayi sauri ya fara duduba dutsen maganin daya saka a fitilar dan bai San Mai yasa yake Jin Kamar Yesmeen karya take a yanzu da yayi waya da Rabiu yake fada masa anya ba karya Yesmeen take ba ta gano shirin sa tunda jiya daya so tilasta mata ki tayi taya tashi daya zata je ta kunna fitilar"

Hakane yasa yace ya duba dutsen indai ya gani a kasa tabbas kunna fitilar tayi idan kuwa bai gani ba karya take bata kunna ba.

Yana cikin dube duben ya hango dutsen a wajen kofa,da sauri yaje ya dauki dutsen ya saka a Aljihunsa Yana ji Kamar an Masa bushara da gidan Aljanna wani irin kallo ya zubawa Yesmeen da har lokacin murza idon ta kawai take,yayi kasa da murya Yana "Sai naga da wane idon zaki cigaba da munafirci ke da gani sai dai a lahira"

Ya fice daga d'akin da sauri.

Wajen Sha biyu yayar Sajeeda da Asmau suka iso gidan, Kabiru ne ya d'auko su a Tasha a lokacin da Suka bugo waya akan sun iso dan baa garin suke ba daga Malumfashi suka zo dan Sajeeda duk haifaffun can ne har kabirun da ya zama dan Aminin mahaifinsu tsabar abotar Yasa Suka hada yayansu Aure,da fari Nuratu mahaifiyar Yesmeen Kabiru yaso aura ita Kuma a lokacin sai ta nuna Bata kaunar sa hakane yasa ya koma Kan Sajeeda da ta amsa tayin soyayyar sa iyayensu da suka Dade suna san zumunci ya Kara kulluwa a tsakanin su suka shige musu gaba wajen hada auren.

Mallam Ayuba shine mahaifin Sajeeda yaransa hud'u akwai Garba Zainabu Abu da suke kiran ta da Yaya Abu sai Sajeeda sai Nuratu mahaifiyar Yesmeen da ta kasance Auta.
Duk da Sajeeda ke bin Yaya Abu basu fiye shiri Kamar yadda take Shiri da Nuratu ba,dan Nuratu mahaifiyar Yesmeen nada balain saukin kai Kamar yadda itama Sajeeda ke da saukin Kai,Yaya Abu kuwa tana da balain zafi dan ko su bata daga musu kafa idan abu ya hado su,ba Wanda bai San bata da dadin shaani da dadin zama ba,hakane yasa Koda Nuratu ta rasu Sajeeda ta dage ita zata rik'e Yesmeen dan tasan,Yaya Abu bazata iya rik'e Yesmeen da amana ba.

Yaya Abu shekara biyu da suka wuce mijinta ya rasu,yarta daya mace itama tayi aure a can Malumfashi,labarin dake Kai musu a can garin akan Kabiru ya zama Mai kudi yasa suka taho dan su gane wa idon su,dama Yaya Abu ta Dade tana san ta zauna a birni dan ko da can ji take dama itace a matsayin Sajeeda dake Aure a birni,a Kuma idonta a lokacin Sajeeda tana cikin Jin dadi da take Jin dama itace.

Bata san tazo ita kadai hakane yasa ta taho da Yar kanwar mahaifiyar su Asmau wanan kenan"

Tunda Suka shigo harabar gidan Yaya Abu take ta kalle kalle tana mamakin girman gidan,daga motar ma da Kabiru ya dauko su tasan cewar kudi ya zauna ba karya.

A haka Kabiru yayi musu jagora har cikin palon sai da suka zauna ya tafi d'akin Kiran Sajeeda.

Sajeeda

A yanzu bazan iya fadar tashin hankalin da nake ciki ba dan wanan ruwa mai doyin ne ha sake zubo min zuwa yanzu na fara zargin wanan masifar Abban Nusrah ne ya saka min dan tsawon zaman mu hakan bata tab'a faruwa dani ba,ba bandakin wasu nake Shiga ba balle nace a bandaki mutane na kwasowa kaina cuta,bansan dai zargin da Zan yiwa Abban Nusrah ba,dan yadda nake fama da kaikayi banga yana yi ba,har yanzu ban manta shekaranjiya da ya kusanceni yadda naji jikinsa kamar ba nashi ba jikina ya dauki sanyi na Rasa tunanin da zanyi,Ina kuka na shige bandaki na Kara wanke jikina na fito a daidai lokacin da ya shigo d'akin Yana "Yaya Abu sun iso tana Palo ki fito ki same su zanje na samo musu abu basu kadai ba duka gidan gabad'aya tunda Yesmeen na fama da matsalar ido"

"Abban Nusrah har yanzu ruwa mai doyin nan zubo min yake kuma"

"Ya isa haka Sajeeda yanzu ba lokacin magana bane ba da bak'i a gidan ki bari idan na dawo sai muje asibiti kifito suna Palo"

Daga haka ya fice daga d'akin nabi bayansa da kallo har ya fice.

Haka na daure nayi waje dan banaso Yaya Abu ta gane banida lafiya yayata ce uwa daya uba daya amma tana da wani irin Hali da bana so ba wacce nake bud'ewa cikina na fada mata sirrina kamar Nuratu mahaifiyar Yesmeen shi yasa har gobe nake kukan rashin ta,tun muna Yara ciwona ciwonta ne,amma banda Yaya abu da kamar ma so take ta ganka a cikin masifa.

Murmushi na aro na yafa a fuskata na hau musu sannu da zuwa

Yaya Abu kuwa ta yatsine fuska tana "Sai da Kika ga dama kika fito saboda kunyi arziki Sajeeda ace tun dazu da muka zo sai yanzu zaki fito"

"Kiyi hakuri Yaya Abu wlh ba ni da lafiya ne daga bacci ma na tashi"

"Allah sarki ya jikin"

"Da sauki Yaya Abu ya Kika baro su baba yaya Asmau ya yaran"?

Nace Ina kallon Yaya asmau da take saar Yaya Abu Yar kanwar maman mu ce itama kusan halin su daya da Yaya Abu.

Yaya Abu bata ko kalli ruwa da lemon da na ajiye musu ba ta mik'e ta hau kalle kallen palon tana "Sajeeda haka Kika samu duniya Ina Kabiru ya samo kudi haka naga ga katon gida ga katon mota"

Murmushi yak'e nayi dan ba Wanda yasan Kabiru a baya da idan yaga yadda yayi kudi yanzu bai yi tambaya ba dole ayi mamakin yadda ya kudance dare daya,kunya ma nake ji a tambayeni Wai nace abokin sa ne ya taimaka Masa.

Murmushi kawai nake ita kuwa Yaya abu ta washe baki tana "wlh na samu wajen zama ba Abunda zai maidani kauye anan zanyi zamana kayana kawai zan debo wanan uwar daula haka ace jinina ke da Wanan daular ni Ina can Ina fama a haya,Ina ai bari mijinki ya dawo dan ni ba kunyarsa zanji ba.

Wanan Yana cikin abinda yasa bana kaunar Yaya Abu tazo wajen da nake dan ko kad'an bata san Mai ake cewa kunya ba.

Nidai bance komai ba dan na fara Jin kaikaiyi sai da ta kurbi lemo tace "Ni Ina Yesmeen take ne ko taje makaranta dan nasan su saifullahi dai suna makaranta"

"Tana daki dazu abu ya fado mata a ido bari na dubo ta nasan bata San kin iso ba"
Chapter 21 · 0% Book details