Sashe 24
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*
*PAGE 15*
Yesmeen ganin Kabiru na k'ok'arin dagowa dan ya nemo ruwa yasa tayi saurin maida fuskarta sama hawaye na zubo mata na halin da Sajeeda ke ciki cikin ihun ta ringa lalube da hannu tana "Mai ya samu ummana ku fada min dan Allah mai ya sameta"?
"Dalla ki rufewa mutane baki kin cika mutane da ihu duk ke kika jawo ma ta sume,haka kawai zaki daina gani ga idonki tarr a bud'e"
Yaya Abu tace a tsawace a daidai lokacin da Kabiru ya kawo ruwa aka hau watsawa Sajeeda dogon numfashi kawai taja,hakane yasa Yaya asmau tace "Ina ganin mu kaita asibiti tunda har yanzu tana numfashi,a hada da Yesmeen din kawai muji mai ya samu idonta,da wanan Kabiru ya fara k'ok'arin kinkimar Sajeeda da taimakon Yaya Abu.
Asmau Kuma ta saka saka hijabinta ta ruko hannun Yesmeen dake ta kuka tana kallon sama,tasan saboda ita Sajeeda ta yanke Jiki ta Fadi tana tsoron wani abu ya samu Sajeeda Kamar bata gani ta ringa hada hanya har suka isa bakin motar Kabiru,suka shige, Kabiru yaja motar a guje.
Suna isa asibiti akayi emergency da Sajeeda Yesmeen Kuma Yaya Asmau tayi bangaren da likitan ido, yake, Kabiru sam bata Yesmeen yake ba dan yasan likita bai isa ya gano silar makancewar ta ba yau ranar farinciki ce a gare shi Amma Sajeeda na neman daga masa hankali ya rasa wane irin kauna take yiwa Yesmeen haka,ko Annur daya kurmance bata daga hankalin ta kamar haka ba.
Yana tsaye a kanta da Yaya Abu likita na duba ta dan private ya Kai su.
Yesmeen
Jikinta rawa kawai yake tana Jin kamar ta zura da gudu tana tsoron likita ya dubata ya gano tana gani,bata San ya zatayi ba.
Har kinkina take wajen amsa tambayoyin da likita ya ringa mata akan idon nata Mai ya fara samun idon nata kafin ta daina gani,haka ta ringa bashi Amsa Yaya asmau na tayata da ya taimaka ya dubata taya tashi daya zata daina gani.
Likita gadon dake can gefe yace Yaya Asmau ta Kai Yesmeen ta kwantar da ita zai haska idon nata.
Da wanan Yaya Asmau ta rik'e hannun Yesmeen ta kaita Kan gadon Yesmeen ta kwanta idonta a sama tana hawaye, addua take Allah yasa Yaya Asmau ta fita daga office din ta roki likita ya rufa mata asiri"
Yaya Asmau na tsaye a kanta.
Likitan ya iso wajen gadon ya samu wani cocilan ya dallarewa Yesmeen Ido,Yesmeen ta rufe idonta da sauri,cikin mamaki likitan ya Kara gyara tsayuwar sa dan daga yanda ta rufe idonta na nufin tana gani,dan da bata ganin ko motsa idon ba za ta yi ba.
Ya Kara kure duk hasken cocilan din ya haske idonta ta Kara rufe idonta dan ji tayi hasken na ci mata ido,
Likitan kuwa cikin mamaki ya kalli Asmau ya maida kallon sa kan Yesmeen yana "Ai tana gani baa abinda ya samu idonta gaskiya"
Yaya Asmau ta saki baki tana kallon likitar Yesmeen hankali a tashe ta fara girgiza kai tana "Bana gani likita dagaske bana gani ka yarda dani bana ganin komai sai duhu"
Likitan a dan rikice yace "Bakya gani fa ki ka ce idan ba kya gani ai ba za ki rufe idon ki da na haska da cocilan ba,gaskiya a dubawar da nayi kina gani"
"Likita anya tana gani kuwa ya za'ayi tana gani tace maka bata gani"?
Tom bansani Mai yasa bata gani ba,amma indai bata gani yadda na haska idon ta ko motsi baza tayi da idon ba"
Amma bari na Kara duba idon nata.
Ya d'auko wani Abu kamar glass ya sawa Yesmeen dogon igiyar ya jona da wani Abu Mai Kama da computer dake saman wajen gadon ya fara duba idon yesmeen,sai da ya duba komai daya shafi idon ta amma bai ga wani matsalar da zata saka Yesmeen taki gani ba"
Koda ya gama dubawa cire glass din yayi daga idon yesmeen yace Yaya Asmau ta sauko da ita,ya koma wajen zaman sa ya hau rubuce rubuce sai da ya gama ya kalli Yaya Asmau yana "Ni dai duk binciken da nayi gaskiya ba abinda ya samu idon ta idan dai har bata ganin Ina ga larurar tata bata asibiti bace"
Yaya Asmau kuwa cikin mamaki tace "Abin nan da da ban mamaki ga idonta a bud'e dai amma Wai bata gani Kai ma ka duba baka ga komai ba"
Yaya Asmau tace tana Kai hannu wajen fuskar Yesmeen ta ringa juya hannun Kamar zata tsone mata Ido Amma Yesmeen ko motsawa bata yi ba ta ringa kallon sama, likita ya mik'a wa Yaya Asmau takarda akan ga magungunan dai a siya mata.
Haka Yaya Asmau ta ruko hannun Yesmeen suka fito daga office din Suka nufi d'akin da aka kwantar da Sajeeda.
Suna Shiga suka ga Sajeeda a zaune duk da ruwa a jikinta kuka kawai take sharba Yaya Abu na masifar tayi shiru ita fa ba yarinya bace Mai haka zata cika asibitin da kuka,
Kabiru kuwa shiru kawai yayi dan tana farfadowa ta fara kuka.
Sajeeda kuwa Yesmeen data ga tana kallon sama hannun ta na lalube sun shigo d'akin yasa ta Kara rushewa da wani kukan tana "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha "Yaya Asmau mai likita yace ya samu idon yesmeen dan Allah karki ce min dagaske ne Yesmeen ta daina gani"
Yaya Asmau na k'ok'arin magana Yaya Abu ta Kara dakawa Sajeeda tsawa tana "Wai ke Mai hakane Sajeeda ke fa ba yarinya bace ke idan kina irin wanan kukan Mai kikeso ita Yesmeen din tayi"?
"Ki barni Yaya Abu dole nayi kuka dan tunda Abban Nusrah ya hadu da wanan abokin nasa ya shigo rayuwar mu da Sunan taimako nake ganin masifa kala kala,wlh rabona da kwanciyar hankali tun kafin Abban Nusrah ya had'u da abokin nan nasa,tunda kuwa suka hadu,daga wanan sai wanan,daga komawar mu gidan daya bamu Annur ya kurmance,nima kaina ba lafiya ce dani ba,Wai yanzu tashi daya Yesmeen ta wayi gari tace bata gani,sai nayi magana Abban Nusrah yace ba haka ba wlh bazan iya cigaba da zama a gidanan ba idan har Abban Nusrah bazai maida Masa dukiyar sa ba wlh gida Zan koma,ko shekara daya bamu yi ba masifar yau daban na gobe daban"
"Ikon Allah Sajeeda a hayyacin ki kike kuwa,Mai ya hada kurmancewar Annur da makancewar Yesmeen da abokin mijinki, Mai laifin Wanda ya taimakawa mijinki ya tsamo shi daga talauci dan ya dandana arziki kina nufin kin fi karfin Allah ya jarrabce ki"?
"Haka nake fama da ita Yaya Abu ban taba sanin Sajeeda makiyata bace sai yanzu,tunda ta bud'e ido taga Allah ya amsa adduata na samu mai taimaka min ta dorawa kanta masifa Bata tab'a zaton alheri kullum sai sharri da zargin abokina take,
ta dage bata hanyar halal abokina ke samun kudi ba, Bayan abokina Yana da balain kudi,shikenan duk wani Mai kudi ba ta hanyar halal yake neman kudinsa ba,yanzu sai ace dangote ma ba ta hanyar halal yake samun kudinsa ba,Sajeeda burinta taga na Kare rayuwata a talauci Ina yawo gida gida Ina gyara Allah ya kawo min wanan bawan Allah dan ya taimaka min Sajeeda tace ba haka ba tsabar masifa ko tuntub'e tayi sai tace tana zargin ba ta hanyar halal abokina ke samun kudi ba"
"Nasan mai nake cewa Abban Nusrah Kar idonka ya rufe da San kudi ka kasa gane abinda nake so na nuna maka,Mai ya kurmantar mun da yaro har gobe ba Wanda yasan dalili,yanzu ma Yesmeen ta makance bata gani,Kai Kuma kasan halin da nake ciki ban da mugayen mafarkai da nake fama dashi Abban Nusrah mai yasa tun a baya duk wanan masifun basu sameni ba sai yanzu?
"Saboda a yanzu Allah yaga damar jarrabtarki yau naga masifa a wajen yarinya nan,Sajeeda iya sanina Baa miki baki ba,idan Allah zai maka arziki haka kawai kake wayar gari kaga kayi kudi,?naga dole sai da sila silar arzikin Kabiru ta hannun abokin sa ne idan Zaki tsarkaka zuciyar ki ki kwantar da hankalin ki ki tsarkake zuciyar ki"
Ta kalli Asmau tana "Wai Mai likita yace ya samu idon nata ne"?
"Yace bai ga komai ba sau biyu ya duba idon yace ba abinda ya samu idon ta idan dai bata gani toh matsalar bata asibiti bace ba dan ko Ina zamu Kai ta a dubata zaa ga idonta kalau yake"
"Kinji ko Yaya Abu Wai Mai yasa bazaki fahimceni bane haka kawai Yesmeen zata daina gani ki duba lamarin nan"
Kabiru a fusace ya fara magana Yana "Yaya abu na gaji da halin Sajeeda ki Mata gargadi,Kar ta Kara danganta koma me ya faru da abokina Ni musulmi ne na yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka,kurmancewar Annur da Yesmeen daga Allah ne na karbi wanan jarrabta da hannu biyu idan bazata iya ba sai tasan nayi"
Daga haka Kabiru ya fice daga d'akin Yaya Abu ta hau bashi hakuri Yana fita ta rufe Sajeeda da fada tana "wlh bansan Baki da hankali ba sai yau wato kinfi san rayuwar talauci akan na arziki toh wlh ki gagauta cire wanan tunanin a ranki ki mori arziki mu mora Asmau kiji min masifa a wajen Sajeeda"
Sajeeda kuka kawai take dan ba Mai fahimtar ta dama tasan Yaya Abu bazata tab'a ganewa ba har gwara ma Yaya Asmau a yanzu ta fara ma zargin kabirun dole ta fara saka mishi ido,ya fara abubuwan da take dasa zargi akansa.