Sashe 1
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*RUFAFFEN SIRRI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHEEM*
*PAGE 1*
"Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun bakin ciki haka nake ji a lokacin da naji Abban Nusrah na ta shafani wanda nasan mai hakan ke nufi,tun kafin nayi bacci bai neme ni ba sai yanzu,ban motsa ba dan har ga Allah bazai samu abinda ya keso har ya gamsu ba,sai dai shi kadai yayi kidan sa yayi rawar sa duk da ba abinda ya shafe shi ko baccin nake idan yayi ra'ayi ko ban bashi hadin kai ba zai juyo dani ne ya samu biyan bukatarsa.
Ina Jin lokacin da ya rabani da zanin dana dora a saman t shirt din dake jikina,a madadin ya juyo dani sai naji ya rungumeni ta baya,ya fara k'ok'arin neman hanya da jikinsa dan tsawon zamana dashi ban wani san dan aike ba balle har wai a motsa min sha'awa,shi dai burin sa kawai ya shafani sama sama ya samawa kansa nutsuwa,inda naji Yana k'ok'arin yi yasa nayi saurin janye jikina,sai a lokacin na motsa na juyo Ina kallon sa cikin mamaki,shi kuwa idonsa a kankance ya kara jawoni,sai na juyo a rigingine dan ya samu abinda yake so dan Ina tunanin dan ta gefe yasa yayi hanyar da ba haka ba,sai dai a madadin ya hau kaina sai naga ya Kara juyar dani ya kankameni da hannu daya ya sa hannu daya ya Kara danna jikinsa wajen da yasa na Kara janye jikina da bala'in sauri na Mik'e zaune cikin mamaki Ina kallonsa.
K'ok'arin jawoni yake na janye jikina Ina "Lafiya kuwa Abban Nusrah mai haka"?
"Wane irin tambaya ne wanan Sajeeda bangane mai haka ba ki matso na samu nutsuwa ki koma baccin ki"
"To ai kai din ne bangane ba Kai ma kasan ba wajen nutsuwar ka nufa ba bayana naji kana k'ok'arin shiga"
Tsaki yayi ya Kara jawoni da k'arfi Yana "Ta bayan yafi dadi bari kigani"
Da karfi naga Yana Neman tura jikinsa bayana
Da k'ok'awa na fusge jikina cikin tashin hankali da mamaki na sauka daga gadon na nufi wajen haske na kunna na zuba masa ido kamar yanda shi ma ya zubo min ido, tamkar an like min baki haka naji dan tsabar mamaki na ma kasa magana,shekarar mu Ashirin da biyu da Aure bana Jin da gani har shi bakine a wanan fagen balle ince sani ne bai yi ba shi yasa yake k'ok'arin nema na ta baya har Yana cevmin yafi Dadi.
"Abban Nusrah anya a hayyacin ka kake kuwa"?
Mik'ewa yayi ya nufo wajen da nake tsaye yayi kasa da muryarsa yana "Sajeeda a hayyacina nake nasan zaki ji wani iri amma ki taimaka ki ba ni hadin kai ina so na gwada ta bayan nan ance yafi dadi"
"Allah ya kiyaye Kabiru Allah ya kiyaye ni zaka nema ta baya ta Inda ake kashi,kabiru Anya Kaine kuwa?waye yace ma ka nemi matar ka ta baya, idan Wanda ya baka shawara bashi da ilimi kai ina ka Kai naka ilimin bayan kasan haramun ne, bazan iya ba Kai ma da ka yi tunanin kayi gwajin ka fara istigifari"
Kasa ya Kara yi da murya cikin rarrashi ya matsoni Yana "Sajeeda yanzu baza ki iya taimaka min ba ki bari nayi sau d'aya sai muyi istigifari an dade ana kwadai ta min ta bayan nan haba matata"
Ya fara k'ok'arin rungumoni na ture shi da iya karfina dan zuwa yanzu ma sai naji tsoron uban yayana ya kamani,gani nake kamar bashi ba
"Kabiru Ina ga ba'a hayyacin ka kake ba a tsawon lokacin da nake tare da Kai nasan baka shaye shaye ballantana nace ba'a hayyacin ka kake ba,a iya sani na ka na da ilimin ka daidai gwargwado ka san abinda ya ke daidai da wanda yake haramun, bazan tab'a maka biyayya na Sabawa Mahallicina ba Ina mai rokon ka idan a hayyacinka ka ke wani ne ya baka shawara ka zo ka neme ni ta baya,ka gaggauta rabuwa da koma waye dan so ya ke ya Kai ka halaka"
Daga haka na nufi Kan gado na na dauki zanina na daura nayi hanyar fita daga d'akin ya hau kwalla min kira Yana
"Sajeeda Sajeeda karki sake ki bar d'akin Nan
Ko juyawa ban yi ba har na bar d'akin har lokacin ban daina mamakin sa ba.
Koda na fito dan karamin palon namu fitila na kunna idona ya sauka akan agogo naga karfe uku na dare na zauna akan kujera tare da dafe kaina jikina har rawa yake bansan tunanin ma da ya Kamata nayi ba.
Na kasa yarda da abinda ya faru yanzu a daki,na kasa yarda mijina uban yayana da shekarar mu Ashirin da biyu da aure da arzikin Yara biyar har mun aurar da Yar mu ta fari Nusrah shi ne yau dare daya zai nemeni ta baya wai ya dade yana san yayi gwaji an ce Masa yafi dadi har waye zai ce wa Kabiru ya gwada abinda Allah ya haramta.
Sosai na zurfafa a tunani bansan tsawon lokacin da na d'auka Ina saka da warwara ba,sai Kiran sallah ne ya katse min tunanin da na tafi.
Mik'ewa nayi na koma d'akin.
A kwance na ganshi Yana dan girgiza kafarsa da alama ba Bacci yake ba idonsa biyu.
Bandaki na shige na daura alwala na fito har lokacin Yana kwance bai motsa ba,nasan fushi yayi,da ace wani abin na Masa da har zai yi fushi dani da sai na bashi hakuri,amma ni nasan ba laifin da na masa bazan tab'a masa biyayya a sabon Allah ba ba muyi haka tun kuruciya ba sai yanzu da muka Manyan ta,tsawon zamana dashi ban tab'a hana shi hakkin sa ba Koda kuwa fada mu ke amma dai yau na bijire masa dan bazan iya Sabawa Allah ba,
tsigar jikina har tashi yake idan Ina hararo yanda wai zai sadu dani ta baya.
Sallah nake amma na kasa yin sa a nutse sabida tunanin da ya dankare min zuciya.
Har na sallame Yana kwance zuwa yanzu sai naji kamar canzo kabiru aka yi bashi bane dan iya sani na baya Wasa da Sallah fushi dani bazai saka wai yak'i fita massallaci sallah ba.
Kasa hakuri nayi da carbina a hannu na Mik'e na zagaya ta wajen da ya kwanta Ina "Abban Nusrah "Abban Nusrah yau ba zaka yi sallah bane"?
"Dama can ke kike saka ni nayi Sallah"?
"Bani nake saka ka kayi sallah ba amma dai bai dace idon ka biyu kana Jin ana sallah ka k'i tashi kayi akan lokaci ba"
Tsaki yayi ya juya min baya.
Zuwa yanzu bazan iya fadan kalar mamakin da nake na sauyawar halin mijina dare daya ba,ga nemana ta baya ga k'in sallah.
Bai tashi ba sai da gari yayi haske ya shige bandaki ya dauro alwala yazo ya tada sallah Yana sallamewa ya fice daga d'akin.
A ranar sukuku na wuni na rasa mai ke damuna dan tunda Abban Nusrah ya fice daga gidan bai Kara dawowa ba.
Har karfe hud'u na yamma Ina zaune zuciyata fal da tunanin muryar Yasmeen ya katse min tunanin da na tafi "Umma ko dai magani zan d'auko miki ki sha"?
Girgiza kaina nayi na aro murmushi na yafa a fuskata sam bana so ta fahimci Ina cikin damuwa,dan nasan sai ta fini ma shiga cikin damuwar, kallonta da nake fuskar kanwata nake gani a fuskarta Margayiya Nuratu damuwar da nake ciki yasa naji hawaye na zubo min.
"Umma kuka kike"?
Share hawayena nayi Ina "ba kuka nake ba Yesmeen na tuna kanwata ne kawai Allah ya gafartawa Nuratu"
"Bata amsa ba illa idon ta da naga ya ciko da kwalla shekara goma kenan da rasuwar kanwata da ta kasance mahaifiyar Yesmeen.
Ruk'onta ya dawo hannuna Ina balain kaunar yesmeen tamkar yanda nake kaunar yayan cikina,
Yesmeen ta Kara siye zuciyata ne daga lokacin da rukon ta ya dawo hannuna,tana da bala'in biyayya da hankali duk wani abu data san ina so bata Wasa dashi bata da burin daya wuce taga ta faranta min ko Yaya ta gani a cikin damuwa itama tayi ta damuwa kenan.
Ko yanzu ma nasan ba lailai taci abinci ba sabida ta gani a cikin damuwa.
"Jeki d'auko mana abinci mu ci dan nasan baki ci abinci ba.
Tura abincin kawai nake ba wai dan Ina gane dandanon sa ba,na daure na hadiye damuwar da nake ciki dan Kar na Kara dagawa Yesmeen hankali.
Koda muka gama cin abincin daki na shige na cewa Yesmeen zan dan kwanta dan itace take yin aikace aikacen gidan Kamar yanda ta Saba kafin Nusrah tayi Aure tare suke aikace aikacen gidan,dan su biyu ne kawai Mata kannen Nusrah duka maza ne,Saifullahi Fahad Hamza da Annur.
Sosai na tsinci kaina a cikin damuwa dan tunda nake da Abban Nusrah bai tab'a fita Yana fushi dani ba dan muna samun sabani zamu shirya,duk da Yana da zuciya nasan hanyar da nake bi na shawo kansa,amma jiya abinda ya b'ullo min dashi ya girmama tunanina bazan tab'a iya barin sa ya neme ni ta baya ba sai kace wasu jahilai.
Karfe goma Sha daya ya shigo gidan fuskarsa a bala'in hade ina zaune a palo Ina jiran dawowar sa dan har yara duk sun yi Bacci.
Ko sallama bai yi ba ballantana ya kalli Inda nake, d'aki ya shige batare da ya amsa sannu da zuwan da nake masa ba.
Da ido na bi bayan sa Ina Kara mamakin fushin da ya ke dani na rashin gaskiya har ga Allah mamaki da al ajabi nake ,mik'ewa nayi na d'auko farantin da na jera abincinsa na bi shi d'akin.
Ko da na shiga a gefen gado na gan sa a zaune yana duba wani abu kamar a takarda ban dai san mai yake dubawa ba"
Na ajiye farantin a gefen teburin dake gefen gadon Ina
"Abban Nusrah Sannu da dawowa"
Bai dago ba ya cigaba da duba takardar Hannun sa