← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 93

Sashe 93

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Numfashi ya sauke yana sake kallon Rayyan daya dakuna mishi fuska

"Na gaji da magana Bilal, bansan me zan kara ce maka ba"

Dariya yayi, kamar yanda yayi murmushi yanzun duk kuwa da yanda yake jin zuciyar shi na mishi rawa. Wayar shi ya zaro daga aljihun shi yana kiran lambarta, sai da ta kusa yankewa sannan aka daga

"Aisha"

Ya fadi yana jin yanda take fitar da numfashi daga dayan bangaren

"Nawan?"

Ta kira cike da shakku da tsoron da yake karanta a yanda muryarta take rawa.

"Ni ne Aisha, ina cikin gidan ku..."

Jin yanda take fitar da numfashi yasa shi dorawa da

"Ban rasu ba, bana cikin motar da ake tunani, bana ciki Aisha"

Daina jin ko motsinta ta dayan bangaren da yayine ya saka shi sauke wayar daga kunnen shi, mintina ya bata ta tattara nutsuwar kafin ya sake kira har sau biyu, amman ba'a daga ba

"Ki daga dan Allah, Aisha ki daga"

Yake fadi yana sake kiranta, da yake kan shi na duke yana kallon wayar baisan ta karaso ba

"Nawan"

Ta fadi tana saka shi dagowa yana kallon ta, tunda yake da ita yaune karo na biyu da take tsaye a gaban shi babu hijabi, na farkon kuma a asibiti ne. Ko takalma babu a kafafunta, shisa baiji takun tafiyarta ba

"Nawan..."

Ta kira wannan karin muryarta na karyewa, kai yake iya daga mata, kafin yayi wani motsin kirki ta hade space din da yake tsakanin su, a jikin shi ya jita, ba haramcin hakan bane tashin hankalin shi, asalima so yake ya zagaya hannuwan shi ya riketa a karo na farko a jikin shi ko dan kewarta da yake ji a ko ina na jikin shi. Amman a cikin gidan su yake, baida idon da zai kalli wani na gidan su idan ya fito ya gansu a haka. Shisa ya kamata yana dago ta daga jikin shi

"Ki rufamun asiri Aisha, laifina mai yawane har a idanuwan yan gidan ku, kar ki mu kara musu dalilin da zasu hana mun ke"

Hannu tasa tana goge hawayen da ta rasa ta inda zata fara tsayar da su. Duk yanda Bilal yaso ta koma gida ta dauko takalma da hijabi kiya tayi, haka ya hakura ya kyaleta, anan suka tsaya yana rasa ta inda zai fara yi mata bayani. Sai ya zabi yaji yanda take a maimakon bayani

"Ban sani ba Nawan, ban san ya nake ba, amman na san komai zai dai-daita tunda ka dawo kafin a hadani aure da wanda bana jin soyayyar shi ko kadan a cikin zuciyata"

Hira sukayi, hirar duk da tazo musu ita sukeyi, dakyar ya iya barinta da tarin alkawurran da yake fatan cikawa. Bai mata bayanin komai ba sai da yaje gida, har aka kira asuba suna manne da juna a waya. A washegarin ranar ya samu Abbu da maganar aje gidan su Aisha, bai musa mishi ba kuwa, da yake itama Aisha ta samu Baban nata da cewar za'a zo a gan shi. Ana isha'i su Abbu sukaje gidan. Bilal da yake gida ya kasa zaune ya kasa tsaye yana jiran dawowar su, sai kiran Aisha yakeyi sai tace mishi

"Ba su tafi ba har yanzun, ban san me suke cewa ba, bana jiyo su daga inda nake. Nawan ba zan iya sake rasaka ba, bana jin zan dawo dai-dai wannan karin"

Bashi da kalaman bata tabbaci idan ba dawowar su Abbu ya gani ba, shisa yake fada mata na shi tsoron. Saboda da gaske ne, babu macen da zata so shi kamar ita. Su Abbu kam da albishir din an bashi Aisha din suka dawo mishi

"Kaddarar su mai girma ce, ni ba zan hana Bilal ita ba, ba zan hana shi Aisha ba. Allah ya san dalilin da ya sake hada su"

Sune kalaman Baban Aisha, shisa Abbu bai boye mishi komai ba har da kaddarar rabon Nur, da yake mutane ne masu dattako da wadataccen ilimin addini daya fadada fahimtar su, hakan bai zame musu matsala ba. Baban Aisha ya jima yana juyayin kaddara irin ta yaran. Bilal kasa hakuri yayi, motar Ayya ya ara yana zuwa gidan Rayyan dan bayason ya fada mishi a waya, ya fi so ya gan shi ido da ido

"Hamma an bani Aisha, an bani ita"

Shine kalaman shi na farko bayan ya shiga gidan Rayyan din

"Shine ba zaka yi sallama ba"

Dariya kawai yayi yana yin sallamar ya karasa cikin falon ya zauna.

"Zan fara zuwa kasuwa, ina son samun abinda zan rike Aisha da shi, makaranta ta jirani na tsayin lokacin nan, zata kara jira shekara daya idan Allah ya aramun lokacin"

Kai Rayyan ya jinjina mishi yana murmushi, dadi yake ji ganin farin cikin da yake shimfide akan fuskar Bilal din, muryar shi can kasan makoshi lokacin daya kalli Bilal yace

"Ba zan baka Nur ba, ba zan baka ita ba Bilal... Yarinyata ce"

Da bayanannen mamaki Bilal yake kallon Rayyan din, ko na rana daya tunanin yarinyar a matsayin tashi duk da daga jikin shi ta fita bai taba je mishi ba. Ya dauke ta sau daya, ya riketa a jikin shi, yanda yaji kaunarta sai da ya tsorata, bai kuma sake daukarta ba. Duka gani nawa ma yayi mata tun dawowar shi, baisan me yasa Rayyan zaiyi wannan tunanij ba, baya nan shekaru uku da suka wuce, ko yana nan ma bashi da zuciyar kiranta tashi.

"Hamma..."

Ya iya kira kawai, yana ganin Rayyan yaja wani numfashi yana fitarwa a hankali, ya fadane saboda ya tabbatar, saboda a tsorace yake, tsoron shi ya karu da yaji Bilal din yana maganar yanda rayuwar zata karasa nutsar mishi, kamar Nur tasan maganarta sukeyi ta fito, tana ganin Bilal ta tsaya tana kallon shi

"Kawu"

Ta fadi, murmushi Bilal yayi mata, Rayyan ya mika mata hannun shi ta karaso ta kama, daukar ta yayi ya dora akan kujera a gefen shi, sai da ya sumbaci hannunta sannan ya sake shi, yana lumshe idanuwan shi da taja kafafuwanta ta dora akan kujera tana kwanciya a jikin shi, kafin ya bude su akan Bilal da yake kallon su da murmushi a fuskar shi.

"Kawu..."

Rayyan ya maimaita sunayin dariya gabaki dayan su. Duka sauran Uncle take kiran su da shi, da gangan Rayyan din yake nuna mata hotunan Jabir yana kiran shi da Kawu.

"Kasan Jabir kawai take kira da Kawu"

Ware idanuwa Bilal yayi, Rayyan ya jinjina mishi kai yana dariya. Ranar farko da ta kalli Jabir tace

"Kawu"

Sai da ya matsa ya fara kalle-kalle yana neman wanda ta kira da Kawu

"Da kai take"

Haris yace mishi, cikin tashin hankali Jabir din yake kallon su

"Nur ya sunana?"

Ya tambaya

"Kawu"

Ta maimaita tana saka Jabir fadin

"La hawla wala quwwata ila billah, wai me yasa? Wa taji ya fada? Me yasa take cemun Kawu saboda Allah?"

Dariya suka dinga mishi, har Abbu saida yayi, dan wani lokaci yakan tsokane shi yace

"Kawu Jabir"

Sai dai yace

"Haba Abbu...idan kuna fada ba zata daina ba wallahi"

Hira suke a nutse suna dariya, wanda duk zai gan su zaiyi tunanin basu da wata damuwa a fadin duniya gabaki daya, zai tunanin basu taba sanin matsala ba, kuma ba haka bane ba, matsala kan tsaida komai, amman zabin kane kayi farin ciki koya yake da yakinin cewa babu wata damuwa da take dawamammiya, da kuma sanin cewa ikon komai ba a hannun ka yake ba, addu'a ce kawai kake da ita, addu'a fa take da karfin sauya kaddarar da take a rubuce tun kafin samuwar ka, shisa suke dariya duk da sanin ko da sun kwanta yau ba lallai su tashi gobe ba, idan sun tashi babu wani tabbaci na ranar zata zo musu da daidaito, amman suna da junan su, komai zai zo da sauki.

*

ALHAMDULILLAH!!!

Ina godiya ga tarin mutanen da basa gajiya da nuna mun kaunar su ta hanyar siyan littafina, bina da fatan alkhairi da addu'o'i. Allah ya saka da alkhairi ya biya muku dukkan bukatun. Allah kuma ya yafe kuskuren mu yayi mana Rahma. Amin thumma amin

Ma'assalam.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
Chapter 93 · 0% Book details