← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 93

Sashe 39

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yake fitowa, group din da tun tana hangen su Nanaa da kawayenta sun tattaru a ajinsu ana shewa ana kus-kus a kai cikin yanayin da yai bala'in jan hankalinta har ta fara lekasu, ba sai an gaya mata ba, tasan su Nana sun girmeta, kamar basuyi nasarar da tayi ta samun makaranta da wuri ba. Da yake sun jima suna son yin magana da ita tana sha musu kamshi dan yanayin wayewar su baiyi dai-dai da ra'ayinta ba, har group din ya zama sanadin da take kula su. Ranar da aka sakata wuni tayi da waya a cikin aljihun wando, sai take ganin duk wani sako da yake shigowa ta manhajar WhatsApp dinta kamar wani na kallon ta, kamar wani na kallon kalar abinda take gani take kuma karantawa da bai kamata tayi ba.

Rannan da Ainau Mardiyya da suke kusa da dakin su sanda ta shiga ayi mata kitso suna hirar waya sai taji kamar da ita Ainau take, kasancewarta daliba itama yar aji hudu, sauran yan dakin nasu ma duk yan aji hudune, a cikin su kuma Dina ce takan mata kitso, wata yar asalin garin Kaduna yaren bajju, taji hausa kamar bahaushiya. Hirar illar wayar da tafi amfaninta yawa a zamanin sukeyi, Ainau na fadin

"Yanzun fa zamani yazo da kana iya kokarin ka akan tarbiyar yaranka, kana tsaye ba dare ba rana, da addu'a dan neman kariyar abinda baka gani wayar hannu na warware maka tufka"

Dayar yar dakin su Ainau din Kamila na karbe zancen da

"Wallahi, abin da tsoro, idan baka kai zuciya nesa ba, waya tsaf zata zama halakar ka, ka hana yara waya wani katon banza ya yaudare su da kwadaita musu ita a waje..."

Tabe baki Dina da takewa Layla kitson tayi

"Idan ka basu ma ba tsira kayi ba, kinsan wani group dana gani kwanaki kuwa? Hankalina yayi bala'in tashi, a wayar Gift kanwata nagani...nasa Maman mu ta karbe, amman naki nutsuwa"

Sosai Layla ta takura, tanajin kamar da ita suke, kamar wata ta leka wayarta taga abinda yake faruwa, taga tarin labaran da bata taba cin karo da abinda ya girgiza duniyarta yana rike tunaninta irin kalar labaran ba, abinda take hasashe ne ake nuna mata yanda yake faruwa cikin yanayin da bata taba hangowa ba, ita kuma Allah yayita cikin jerin mutane masu bin kwakkwafi, dole tana sauka gida zata fadama Naana zata fita daga group din idan sun koma makaranta sai a mayar da ita, saboda Mami na da kula, Mami na kuma da bincike, kuma a karo na farko zuciyarta a tsorace take da Mami taga wannan group din.

Rayyan daya kara dumtsa hannunta yana murza yatsunta ya yanke mata tunaninta dan yanayine da taji har tsakiyar kwanyarta, sai yake tuna mata daya daga cikin labaran da ake tattaunawa a kai jiya a group din, wani abu daya tsaya mata a makoshi ta hadiye tana jin wani irin yanayi da bata da fassarar shi yana saukar mata. A haka suka shiga garin Kano, tana jinta sama-sama. Aisha suka fara saukewa suna wucewa gida. Sanda suka sauka, kafafuwanta babu kwari take jinsu, Rayyan kuma bai jirata ba ya shige gida, hada idanuwa tayi da Bilal da yake binta da kallo cikin wani sanyin yanayi kamar yana son karantarta har zuci.

"Ka sha maganin ciwon kai"

Ta fadi tana wuce shi, launin idanuwan shi sun canza, shisa ta gane kan shine yake ciwo, barin shi tayi a tsaye kamar batayi komai ba, kamar bata taba zuciyar shi ba. Tun da ya tashi yake dan jin ciwon kan, amman ita da Rayyan ne suka kara mishi wani sabon ciwon kan, ta kula kamar ko da yaushe, ta kuma gane kan shi yana ciwo. Numfashi yaja yana fitarwa kan shi kamar zai bude, cikin gida ya shige shima, sun fitar da jakunkunan daga baya.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 2, 2020

15

Su Rayyan ne suke makaranta, sune da karatu amman Ayya ce take ramewa saboda tunani. Duk yanda Bilal yake jaddada mata cewa lafiyar su Rayyan din kalau hankalin ta ya kasa kwanciya. Asalin abinda take son ji Bilal ba zaj fada mata, balle kuma tunda suka tafin basu dawo ba sai yanzun da akayi hutun karshen zango. Da kanta ta nemi Hajiya Dije saboda ta samu a shiga tsakanin Rayyan da Layla, harma da Bilal din. Bata da natsuwar binta wani waje ma, tace taje mata ne, tashin farko dubu sittin Ayya ta tura ma Hajiya Dije. Abinda bata sani ba shine wajen shekaru hudu kenan komai ya kwance a gidan Hajiya Dije.

Tunda maigidanta ya dawo da uwargidan shi, ga yara da take dana sanin cusa musu bakin hali tun suna da kankantar su, mazan kusan duk suna da sana'ar su ta kasuwanci da sukeyi. Amman basa bata kudi, idan ta tambaya sai dai suji abinda zatayi da su, idan ta kama su siya mata ne su siya. Komai ta samu kamawa takeyi ta karyar wajen dilla lai ta kai ma Malamai, to yanzun ma tunda ya kamata tana mishi barbade yai mata saki daya, dakyar aka samu aka maida auren, duk wani abu da zai fito daga bangarenta ya daina ci balle ta samo kan shi. Gani takeyi bokan uwargidan tane yafi wanda take bi.

Shisa take ganin Ayya rashin godiyar Allah ne yake damunta, sam matsalarta ba matsala bace ba, kukan dadi takeyi, ta ga Laylar da Ayya take ta daga hankali a kai, yarinya ce mai kyawun gaske, yarinyar da gari banza duk kyan Rayyan din shima sai yayi gaske ya samo me kyawun Layla. Mijinta abinda duk take so shi yakeyi, kaffa-kaffa yake da bacin ranta batare da wani aikin malami ko boka ba. Amman kullum bata rasa abin mita, shisa ta samu saniyar tatse, ranar da sukaje wajen wani Malamin tare kudi ake tsulawa Ayya idan sun tafi Hajiya Dije ta koma ta karbo. Rabonta da zuwa ma Ayya wajen wani Malami na kwarai tun wanda yai mata aiki akan Haris da tambayar duniya da tayiwa Ayya akan zancen aikin sai tasan dabarar da tayi suka fada wata hirar.

Watakila taji tsoro ne batayi amfani da maganij ba, duk kudin da ta kashe a kai. Tunda kwanaki ma da taje gidan ta ga Haris din ya shigo har bangaren Ayya yana gaishe da ita, harma da yar hira sukayi yana shiga Kitchen ya zuba tuwo da tayi, ba zata manta cewa Ayya

"Haris dinne nan?"

Saboda ita bata ga alamar lalacewa a tare da shi ko daya ba, mikewa Ayya tayi yana amsa ta da

"Shine, bari in dauko miki leshin da nake magana"

Murmushi kawai Hajiya Dije tayi, tasan dan karta tayar mata da zancen Haris ne. Wannan kuma duk matsalar Ayya dinne a ganinta. Yanzun dai a sama ta sami saniyar tatse. Danma kudin a wajen bin 'yan tsubbu suke tafiya itama. Duk kan mijinta da take tunanin an janye hankalin shi daga kaine. Ayya kuwa ranar wata zuciya aka kawo mata an yayyanka turbude da magani akace ta wanke ta zuba ruwan a bakin kofar dakin su Rayyan, sai ta ajiye zuciyar tayi mishi girki da ita duk idan yazo, daga shi har Bilal din a tabbata sun ci, to zai zama kamar ta kwato musu tasu zuciyar ce da Layla ta lashe.

Karba Ayya tayi, da fari maganin yayi mata kama da ararrabi saboda kalar shi, kamar ta dandana da ta wanke, sai tayi saurin kauda tunanin daga ranta. Duk irin wannan was-wasin kan bata aiki wani lokacin. Yanda akace tayi haka tayi, zuciyar ta kulle a leda ta saka a fridge, take ta ajiyarta tunda su Rayyan din sunki zuwa, sai a satin da tayi waya da Bilal ya tsayar mata ranar zuwan nasu. Cous-cous ta dafa musu da ya sha hanta da zuciyar da kuma kayan hadi. Aikam ranar tas suka cinye shi da Bilal, danma Bilal ya tsaya taince albasar da take ciki.

Duk da haka taki samun natsuwa, rabin rayuwar ta tun zuwan su jikin window take yinta, ko baccin rana ta daina samu tana runtsawa, dan ko ta kwanta sai taji kamar an gitta, da sauri take dirkowa daga kujera ta leqa ta ga ko Layla ce. Ga Rayyan din da ta dan fara gane kan shi kafin ya tafi ya kara hargitse mata. Ko sau daya bai tako dakin ba, itama da taje ta same su a bangaren su kan shi a kasa suka gaisa, surutun duniya da tayi baice mata uffan ba. Haka ta fita cikin kunar rai, Bilal ne ma yabi bayanta yana lallashinta

"Ayya kinsan halin shi ai, kuma baya ma jin dadi kwana biyu tunda muka dawo, nima shiru-shirun ake tayi mun"

Ya karashe da murmushi, ranta na suya tace

"Dan uban shi dan bayajin dadi sai inta magana yanaji na yaki dagowa balle inyi tunanin zai tanka? Har yaushe zai san ina da muhimmanci mai girma a rayuwar shi Bilal? Ace yafi karfin ya taso yazo ya gaishe dani ko da sau dayane a rana? Shikenan..."

Ta karashe muryarta na karyewa cikin yanayin da yasa Bilal fadin

"Dan Allah kiyi hakuri....zai gyara ai..."

Kai ta jinjina, dakyar ta iya cewa

"Hmm...Allah ya shirya"

Nan Bilal ya zauna yana ta mata labari har saida ya ga ta warware tukunna ya tafi. Shisa tayi kewar shi matuqa a watannin nan da baizo ba. Duk wata hanya da zaibi ya rage mata damuwa ya sani. Yafi kowa fahimtarta, akwai halayenta da ko Abbu baisan yanda zaiyi da su ba amman Bilal ya sani. Zata iya cewa idan da na zama amini to Bilal ne amininta, duk wata damuwarta ko ta waya idan ta kira shi ta kai karar Abbu da Mami sai ya lallaba ya bata hakuri, saiya nuna mata yanda yake goyon bayanta, cikin dabarar shi. Neman Malamanta ne kawai abu daya da Bilal bai sani ba, abu daya da ba zata iya rabawa da shi ba saboda bata so yayi mata wani kallo na daban.
Chapter 39 · 0% Book details