Sashe 62
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wata dirama ce fa, kamar ma kullum sukeyi"
Tv din Bilal ya dan kalla, yana mayar da hankalin shi kan abincin da yake ci, yasan jikin shi na bukata, amman tunda yazo gidan ba gane kan abinci yakeyi ba. Texts din Rayyan suke tuna mishi wasu lokuttan
"Kaci abinci Bilal"
Shine abinda yake rubutowa da safe, da rana, da kuma dare, bai taba kara wani abu a kai ba, ko ya rage, in sukayi waya kuma baya tambayar shi yaga sakon ko me yasa bai bashi amsa ba, ko da bai tuna mishi ba yana kokarin ganin ya saka wani abu a cikin shi ko da sau daya ne a rana. Duniyar ce yakeji ta hade mishi waje daya. Idan zaka tambaye shi ya yake kwanciya ya tashi da safe ba zai iya fada maka ba, wata rana akan darduma in da yakan yi salloli nan bacci yake dauke shi, ya fara sallolin ne saboda tunanin neman wani abu ya sha dan ya taimaka mishi wajen bacci ya fara damun shi
"Muryar ka na mun kama da wanda depression yake shirin kamawa Bilal, idan ba zaka iya mun magana a dan uwan ka ba, kai mun magana a matsayin likitan da zai iya taimaka maka..."
Rayyan yace mishi jiya da safe, yana kara saka shi jin babu dadi, saboda ya saka shi cikin damuwa, bayan abinda yakejin yayi mishi
"Ban san me zance maka ba... Idan na kara ce maka babu abinda yake damuna zai zamana wata karyar akan wadda nake tayi a kwanakin nan, saboda haka zan fada maka gaskiya Hamma, wani abu na damuna, amman bana son inyi magana a kai, dan Allah ka daina tambaya, kana karamun nauyi da tambayoyin ka"
Yanajin numfashin da Rayyan ya sauke ta dayan bangaren, runtsa idanuwan shi Bilal yayi yana bude su
"Ba zan sake tambaya ba, in kayi mun alkawarin ko da kaje asibiti sun baka wani abu karka sha sai naga menene"
Dan murmushi Bilal yayi, shi me zai ma kaishi asibiti. Har yanzun duk yanda ake magana kan mental health bai shiga zuciyar shi ta yanda zai dauki kafafuwan shi yaje asibiti a kai ba.
"In shaa Allah. Lafiyata kalau da gaske, damuwa ce kuma kowa na tare da ita yanzun..."
Ya karasa da yar dariya dan ya saukaka musu yanayin daga shi har Rayyan din
"Zan zo karshen wata In shaa Allah... Zan zo in gan ka"
Kai Bilal yake girgizawa
"Kar ka baro hidimar ka nace maka lafiyata kalau Hamma"
Wayar Rayyan ya kashe a kunnen shi alamar ya rigada ya gama yanke hukuncin zuwa, babu kuma abinda zai sake hakan. Tun jiyan yake lissafa kwanakin da suka rage a cikin watan, yana ganin saura kwana tara, tabbas nauyin da kan shi yayi zai karu idan Rayyan da Abbu suka kasance waje daya yana ganin su a duk rana. Tunda yazo ya kasa bari idanuwan shi su shiga cikin na Abbu sam, ko hira mai tsayi ya kasa zama suyi, kullum cikin uzuri yake dan yabar dakin Abbu din. Ga Aisha yanzun da fada suke na rashin dalili, ko yau sai da sukayi kafin ya taho
"Damuwar ka na damuna duk da ban santa ba, amman baka mun adalci ka sani..."
Ta fadi tana tashi tabar shi a wajen, ya rasa yanda zai ya dinga bata hankalin shi kamar da, ko waya suke yakan shiga wani tunani sai taita magana bai san tanayi ba, haka idan suna chatting yakan manta ya ajiye wayar, wasu lokuttan sai ta kira sannan yake tunawa, banda hakuri babu abinda yake da shi da zai bata, amman yana bukatar duk wasu kalamai na hakuri da zai iya adanawa, saboda yanajin yanda shine kawai abinda ya rage a tsakanin shi da mutanen da suka fi kowa kusanci da shi.
*
Ganin karfe sha biyu saura yasa Mami sake tashi dan taje ta duba taga ko lafiyar Layla. Bataji motsin ta ba da asuba sai da ta tasheta, wajen tara na safe ma ta sake tashin ta dan ta karya. Tana tura dakin kuwa taga bacci takeyi, karasawa tayi tana dan bubbugata
"Layla..."
Mami ta kira a dan tsorace, dakyar Layla ta bude idanuwanta, da zazzabi ta kwana ga kasala, jikinta kamar ta aro takeji, da tana sallah da asuba sai takejin jiri na dibarta, raka'a ta biyu a zaune ta karasa ta dakyar
"Lafiyar ki kuwa?"
Mami ta tambaya tana taba jikin Layla da taji kamar wuta
"Subhanallah..."
Ta furta tana kama Layla ta dago ta
"Mami bani da lafiya"
Cewar Layla tana sake komawa ta kwanta saboda yanda take jinta, tana zazzabi kala-kala, amman wannan daban yake, tunda take a duniya bata taba jinta a irin yanayin da take jinta yanzun ba, ko dazun da Mami ta shigo ba bacci takeyi ba, maganar ce take mata wahala da ta fada mata bata da lafiya. Gabaki daya Mami ta gama rikicewa, tashi tayi tana wucewa ta dauko hijabi ta saka a jikinta tana dawowa dakin Layla da take jin wani sanyi na ratsa sassan jikinta, lokaci daya tunanin mutuwa na gifta mata, yana sakata jin ko dai ciwon ajali ne ya kamata
"Ko mutuwa zanyi Mami? Jikina baya mun dadi"
Zuciyarta Mami taji tayo wani tsalle tana dawowa makoshinta
"Wacce irin magana ce wannan? Jiba shirme"
Ta karasa tana daukar wayarta da take kan gadon Layla tana rasa waya kamata ta fara kira, Haris dai baya garin ma, sunje wani Seminar a Katsina. Idan ta kira Jabir da wahala yana kusa, lambar Bilal ta lalubo tana kiran shi, sai da tayi tunanin ba zai dauka ba sannan taji sallamar shi cikin kunnenta
"Dan Allah Bilal idan kana kusa kazo ka kaimu asibiti, Layla bata da lafiya..."
Da sauri ya amsa da
"Gani nan... Bari in shigo"
Sauke wayar tayi daga kunnenta tana mikewa, hijabi ta samo ta kama Layla ta dago ta tana saka mata, duk ta langabe a jikin Mami, ga amai da yake tukarta amman yaki fitowa, tunda asuba take jin shi. Gabaki daya sama-sama take ji, kamar rabinta a duniya rabinta a wani waje da bata san ina bane ba. Ko minti goma ba ayi ba sai ga Bilal din ya shigo bangaren Mami da sallamar shi, dan a kwance yake sanda kiran Mami ya shigo, da kamar ba zai daga ba, baisan me zaice mata ba, tunda ya dawo sau biyu ya ganta, yana duk kokarin shi wajen ganin basu hadu ba, sai dai Mami ba zata taba kiran shi babu wani dalili mai karfi ba.
Yana dagawa kuwa yaji dalilin ne mai karfi, motar su ta sami matsala tun shekaranjiya daya ajiyeta wajen gyara bai waiwayeta ba sam. Kuma yaji muryar Mami kamar hankalinta a tashe yake, shisa yana fitowa ya wuce dakin Ayya, a Kitchen ma ya sameta
"Bilal... Lafiya?"
Ayya ta tambaya, ganin yana balle maballan rigar shi kamar a hanya ya sakata
"Mukullin mota zaki bani Ayya, yanzun Mami ta kirani inzo in kaisu asibiti Layla bata da lafiya"
Wani irin kallo Ayya takeyi mishi, duk yaran Maryama din sai ta kira Bilal saboda gulma da neman dalili, Haris baya nan tasani tunda ko da safe sunyi waya. Amman Jabir aikin me yakeyi
"Ina Jabir? Sai kaine zaka kaisu asibiti? Ita ina motar hannun ta?"
Numfashi Bilal ya sauke
"Ayya dan Allah, tun da kikaga ta kirani watakila basa nan ne shisa"
Karamin tsaki Ayya taja
"Kinibibi ne dai da neman magana irin nata, sai kaje ka dauka yana kan drawer din gefen gado, in ka kaisu ka dawo mun da motata zan fita"
Wucewar yayi ya dauko, yanajin Ayya na fadin
"Kabi a hankali kaketa rawar jiki..."
Baiko juya ba harya fice ya na nufar dakin Mami. Aikam yanayin da ya ga Layla din ya daga mishi hankali
"Ki taso Mami"
Ya fadi, kama Layla tayi suna fitowa, sunzo harabar gidan dan ya dauki motar Ayya, sai ga Jabir ya shigo shima da motar Mami din da Ayya take magana a kai
"Bilal ga Jabir nan ma ya dawo, bari sai mu tafi kawai"
Kai ya jinjina mata
"Bari in maidawa Ayya mukullin dan zata fita sai in zo mu tafi"
Wannan karin kai Mami ta girgiza mishi, daman saboda tana tunanin idan ta tsaya jiran Jabir za'a bata lokaci shisa. Tasan halin Ayya, zata iya fadar maganganu idan Bilal din ya bisu asibiti, kwana biyu basuyi ba, bata neman tashin hankali
"Nasan muma ba jimawa zamuyi ba In shaa Allah...ka koma kawai dan Allah"
Dan juya zancen yayi, kafin ya jinjina kai
"In dai sun rike ku dan Allah a kirani"
Ya fadi yana rakasu har wajen motar, sai da yaga sun shiga har sun juya sannan ya koma ciki. Kai tsaye Aminu Kano Jabir ya nufa da su, in da ba'a bata lokaci ba, basu ma samu layi ba, Jabir ya sai musu kati, mutum daya aka gani sai su da suka shiga, Mami ta zaunar da Layla da take jin kamar zata shide akan kujera ita tana tsayawa, tambayoyi likitan ya fara yi kamar yanda sukan yi
"Tun yaushe kike zazzabin?"
Ya tambaya, dan jim Layla tayi, takan kwana da shi tun dawowar ta, amman baya damun ta, tun da sai ta farka ko fitsari taji shi, in ta samu ta koma bacci kuma da safe ya tafi, yaune kawai ya kwantar da ita haka, cikin rawar murya ta amsa shi
"Na kai sati, amman da dare ne kawai. Yaune har yanzun bai tafi ba"
Sosai yaci gaba da mata tambayoyi kala-kala, jin ance za ayi awon jini dana fitsari yasa Mami fadin
"Bata da aure fa"
Murmushi kawai likitan yayi
"Za'a duba komai ne Hajiya, babu wata matsala"
Haka kawai sai ta tsinci kanta da shiga damuwa, tare da Jabir sukaje aka dibi jini da su biyan kudi, zuwa duk wani abu da ake bukata suka dawo suka zauna suna jiran results din
"Ko zaki sha wani abu in siyo miki?"
Kai Layla ta jinjina
"Ka siyomun Sprite"
Da mamaki Jabir yake kallonta
"Yaushe kika fara shan sprite?"
A shagwabe ta kalli Mami
"Ka wuce ka siyo mata bata da lafiya karku sakani surutu"