← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 93

Sashe 60

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yake iya furtawa, ga shi Aisha ta riga su gama jarabawa, anzo an dauketa tun shekaranjiya, saboda za'ayi bikin yayarta a cikin satin. Daga shi sai ita zasu tafi, bai san mintinan daya dauka a zaune cikin motar ba. Layla ma tun da taga text din shi cewar yana kofar hostel din su wani abu ya kulle a cikinta, a tsorace take, ita tace mishi su manta da komai, amman ta karanta text din yafi sau hamsin kafin ta iya goge shi, ko itama sakon zai isar mata, ko zata iya mantawa da abinda ya faru.

Amman har yanzun tana jinta kamar babu suttura a jikinta, ko da ita kadai ce a kwance. Sam a aji bataso wani ya zauna kusa da ita, kamar abinda ya faru ya saka mata tsoron maza gabaki dayan su, tayi jimla ne saboda yanda har kanta sarawa yayi ranar farko da Rayyan ya daga hannun shi da niyyar ya kai shi jikinta, wani irin matsananci tsoro taji ya shigeta, sai take ganin duk idan tayi kuskuren yin kusanci da wani namiji abinda ya faru tsakaninta da Bilal zai iya sake faruwa, ta kara shiga wani sabon rudanin.

Tana son Rayyan, wata irin soyayya da har tashin ta take da tsakar dare, rokonta karya taba ganewa ko sanin wani abu ya taba faruwa a tsakanin ta da Bilal, group din su ma fita tayi, dan tafi sati tama manta da shi, sai ranar da ta dan samu natsuwa taga sakonnin su, fita tayi tana goge komai, babu wanda ya tambayeta dalili, a aji ma basu ga fuska ba, ta daina musu dariya, ta koma hade fuska kamar yanda takeyi daga farko, da yake babu wanda baisan ta iya masifa ba duk sai suka kiyayeta. Duk da suna mamakin canzawar ta lokaci daya haka.

Sosai ta kan dauki waya ta gwada kiran Bilal, ko gaisawa suyi kamar yanda suka saba, amman sai ta tsinci kanta da kasawa, bata san me zatace mishi ba, saboda kafin ma ta kira din take jin zufa na karyo mata. Tashin hankalin da take ciki daban yake, dakyar ta iya janyo akwatinta ta sauko da shi, amman ta dade bayan ta sauko kafin ta sami kafafuwan ta su motsa ta fita waje, tana ganin motar shi ta hango shi a ciki ya hada kan shi da gaban motar sai da zuciyar ta tayi wata irin dokawa, kamar ta koma ciki da gudu haka take ji.

Bakinta ko yawu babu sanda ta karasa wajen motar, hannuwanta duk sunyi gumi saboda tashin hankali, ta kama baya ta bude saita kasa, hakan yasa ta kama gaban motar tana budewa, cikin yanayin da ya sanar da Bilal ta karaso. A firgice ya dago yana juya kai ya kalleta, sai ya bude nashi bangaren ya fita kamar tana shirin shigowa da bomb, itama yanda kafafuwanta suke rawa yasa ta shiga cikin motar ta zauna tana mayarwa ta rufe

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Kawai yake furtawa bayan ya fita daga motar, jikin shi babu inda baya bari saboda tashin hankali. Dakyar ya zagaya ya dauki akwatin Layla ya saka a bayan motar, amman ya kasa shiga, ya rasa ta inda zai zagaya ya shiga cikin motar. Ya kusan mintina goma kafin ya samu ya karasa, ya bude ya zauna. Jikin shi ko ina bari yake sanda ya tayar da motar, babu kowa, babu komai a bayan shi, amman sai yaji kamar yana kara motar da wani abu, dakyar yayi kwana, ya runtsa idanuwan shi ya bude su yafi sau biyar yaki daina ganin kamar akwai yana a cikin su.

Sai da suka fita titi, taga yanda yake gefe da gefe, motar na yawo, in suka kara mintina goma akan titin tabbas zai bugawa wani, ko ya giftawa wani su a buga musu

"Hamma..."

Layla ta kira tana jin hawaye sun cika mata ido, mutane zasu ce Rayyan na abubuwa a nutse, amman har gobe ba zata ga mutum da yake komai da natsuwa kamar Bilal ba, shisa take gane idan ran shi a bace yake, ko Haris baya abu da natsuwar da Bilal yakeyi. Ba sanyin jiki gare shi ba, wata irin nutsuwa yake da ita, kamar komai a lissafe yake yin shi. Shisa yau da karara take ganin natsuwa ta kwace mishi abin yake kara tabata

"Hamma kayi parking dan girman Allah"

Ta karasa maganar muryarta na karyewa. Parking din Bilal yayi, zuciyar shi zafi takeyi, baisan da wanne ido zai kalleta ba, baisan me take ji ba idan har shi yana jin kamar duniyar shi tazo karshe. Kan shi ya sake hadewa da jikin steering wheel din, baisan hawayen shi na zuba ba, sai da yaji digar su akan cinyar shi. Kuka yake saboda baisan yanda zaiyi ba, baisan inda zai saka ran shi yaji sanyi ba, yanayin kafadar shi tagani tasan kuka yake marar sauti. Nata hawayen zuba sukeyi itama.

Batajin kowa zai fahimci kunci na zuciya sai ka farka cikin dare, jikinka ko ina yana bari da tashin hankalin da ba zaka iya sanar da mutanen da kasan zasu sama maka sauki ba, mutanen da suka fi kusanci da kai akan kowa, saboda kana tsoron tashin hankalin da kake ciki zai hargitsa tasu duniyar, a lokacin hawayen zasu fara zubar maka, kukan da kake tsoron fitar sautin shi dan kar wani yaji yai maka tambayar da ba zaka taba iya amsa shi ba.

Shine halin da suke ciki ita da Bilal, kuka sukeyi, kukan abinda ya faru da su da basu da kalaman misalta shi, kukan yanda rayuwa ba zata taba zamar musu dai-dai ba, karshe kuka suke na alakar da take tsakanin su da ta samu tangardar da basu da tabbacin zata taba komawa dai-dai, dakyar ta iya dago da kanta tana share hawayenta, bata san me yasa take jin kamar ta fi shi karfin zuciya ba

"Hamma... "

Ta kira da wani irin yanayi da ya saka Bilal kara shigewa cikin abin tuqin kamar yana so ya bace daga motar gabaki daya

"Ba laifin ka bane, na fada maka ba laifin ka bane ba, ba zan taba ganin laifin ka ba... Karka taba tunanin zan ga laifin ka, kaddarar mu ce tazo a haka"

Kai Bilal yake girgiza mata, ya kasa dagowa, idan tana fada mishi ba laifin shi bane tana kara saka kirjin shi yin nauyi, tana tuna mishi da tarin mutanen da suka bashi amanar ta, tana tuna mishi da cewa abinda take tunani bashi da wani muhimmanci in har su din ba haka suke tunani ba, a duk yanda ya hasko su, baiga zasuyi mishi uzuri ba, saboda ya kasa yima kan shi uzuri.

"Dan Allah ka daina... Ka daina kuka"

Dakyar ya iya dagowa, ya kasa kallonta, fuskar shi ya goge, ta gefen idanuwan shi yaga ta bude jakarta ta zaro hankici ta dora mishi akan cinyar shi, dauka yayi yana goge fuskar shi sosai, yayi gyaran muryar da yakejin ko da yayi magana ba zata fito ba. Layla ba zata taba gane tashin hankalin shi ba, su Ayya ka dai yake da a fadin duniyar shi, tana da wasu yan uwan bayan Mami, akwai wanda suke uba daya, bashi da kowa daya rage mishi a duniyar shi banda Ayya. Ba hulda takeyi da daginta ba sosai, balle ya san sauran dangin shi na bangarenta.

Su da Abbu ne kadai makusantan da yake da su sai Rayyan da ita, sune kuma mutanen da ya kasa rikewa amana. Aisha ma da yake jin tashi ce, yake jin ba zata bar shi ba, bayajin zata zauna da shi bayan tasan abinda ya faru, sai da ya kunna motar tukunna yace

"Kaddara, ita ce kalmar da kika zaba Layla?"

Ya karasa tambayar yana juyawa ya kalleta, sai take ganin idanuwan shi sun mata wayam, kamar babu emotions ko daya a cikin su, wani irin murmushi yayi mai ciwo daya karya wani abu a cikin zuciyarta

"Kaddarar nan zata iya rabani da mutanen da su kadai nake dasu a fadin duniyata... Idan kin mun uzuri baya nufin su din zasuyi mun"

Shiru tayi, tana jujjuya maganar shi badan bata da amsar bashi ba, in ta bude bakinta sautin kukane zai fito, har saida ya hau titi, wannan karin a nutse yake tuqin, sai da ta tabbatar zata iya magana batare da ta fashe da kuka ba sannan tace

"Shisa ba zamu taba fada musu ba"

Titi Bilal yake kallo, yaji me tace, ya zabi yin shiru ne kawai, saboda zuciyar shi na cikin wani hali.

Taya zai kalli idanuwan Abbu bakin shi yayi shiru?
Ta ina zai hada idanuwa da Abbu kamar bai ci amanar daya bashi ba?
Ana mutuwa sau daya, shine yardar kowa, amman a tsayin satikan nan, ya mutu a duk ranar da zai tashi daki daya da Rayyan, ya ga Rayyan yayi mishi murmushi, numfashin shi daukewa yake yi
Ba zai iya kallon Mami kamar bai taba amanar da ta dauko ba
Wannan karin bayajin mutuwar da zata dauke shi ta wasa ce
Bashi da tabbacin idan numfashin shi ya tsaya zai dawo.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:08 PM - 111: Dec 20, 2020.

23

"Layla ta dawo ko?"

Naadir ya tambaya yana shigowa dakin, murmushi Mami tayi

"Bata dawo ba"

Ta amsa shi, kallon ta yakeyi da murmushi a tashi fuskar kafin ya wuce kitchen, bude-bude ya fara yana ganin wake da shinkafa, sai sauce din manja da ta sha kifi, yana zubawa yake fadin

"Layla ta dawo Allah Mami...ni na sani"

Dariya tayi wannan karin, da yake nan BUK Naadir din yakeyi, kuma duk a cikin yaranta shine makaranta take wahalar wa, saboda kokarin shi bai kai nasu ba, yana cikin gari amman ba kullum yake kwana a gida ba, musamman lokacin jarabawa irin haka, a makaranta yake kwana suna dan taba karatu, wani lokacin har tausayin shi take ji, akan Naadir ta yarda kokari halitta ne, amman babu wanda zaice baya fahimta, idan harka sakawa zuciyarka hakuri da juriyar bibiyar abu, hatta da Marwan tana kallon shi ya ajiye islamiyya, gashi da kokarin amman karatun bawai ya dame shi bane can-can. Yafi gane harkar kasuwan ci da yakan bi Yaya Ayuba.
Chapter 60 · 0% Book details