← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 93

Sashe 25

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rayyan bai tana shigowa bangarena ba, idan ya taba lokacin yarinta na manta... Amman yau ya shigo saboda Layla... Ina tsoro, har raina ina tsoron wannan kaddarar ko wacce iri ce, saboda ina hango tarin tashin hankalin da yake cikinta"

Wannan karin Ahmadi ne ya sauke numfashi, gabaki daya abin ya saka jikin shi yayi sanyi, idan da gaske saboda Layla ne Rayyan din ya shigo ba Mami bace kawai a tsorace, shi kanshi zuciyar shi yaji tana rawa.

"Allah karka doramun kaddarar da bazan iya dauka ba, Allah ka dubeni da Rahmar ka ka saukakama yarana kaddarar su..."

Daren kusan Ahmadi, Mami da Ayya kanta kwana sukayi suna juyi. Ayya na jinjina aikin bokan Maryama da yanda ya zame mata dole ta kira Hajiya Dije su tattauna wannan al'amarin. Mami na tunani amanar Layla da take hannunta, tana kuma tsoron abinda zuciyarta take sanar da ita yana faruwa tsakanin Layla da Rayyan din da bata jin sun sani. Ahmadi kuwa gabaki daya lamarin ne yake sanyaya jikin shi, yaran nashine yake ganin kamar sunyi kankanta, kamar ma basu da hankalin hango kaddarar da take bibiyar su.

Rayyan ne kaddarar su
Rayyan ne suke tunanin zai zama tushen komai.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 22, 2020

10

BAYAN SHEKARA UKU

Ita kadai tasan cikin kalar fargaba da tashin hankalin da take a shekarun nan. Yanda duk taso ta nisanta kanta da Hajiya Dije ko dan gudun suje inda za'a binciko mata abinda zai daga mata hankali sai ta kasa, Rayyan na bata tsoro, yanda yake manne da Layla duk idan ya dawo makaranta yana karya mata zuciya. Musamman yanzun da take ganin suna kara girma, yaranta na wani irin girma da har mamakin shi takeyi. Ita ce harta aurar da Khalifa da Zubaida. Kuma duk lokacin da zata sami Ahmadi da maganar takan ga gajiyawa a fuskar shi, kamar ya gaji da yanda ta kasa daukar ido ta saka akan Rayyan din da Layla kamar yanda yayi

"Ya kike so inyi? Ko akan dukan da yakeyi mata nayi magana tsini ne kawai bakina baiyi ba. Kinsan halin Rayyan, abinda ya ga dama shi yakeyi"

Ahmadin yace mata wani lokacin, ita ko dukan bata so, batason wani abu na hada danta da Layla. Batason ganin shi a bangaren Mami sam-sam. Rayyan din ya kara mata tsanar matar kamar zata hadiyi zuciya haka takeji duk idan taga giccinta. Yau da kanta ta shiga kitchen, har Rukayya na mata tsegumi

"Ayya saboda su Hamma zasu dawo shisa kika ce ke zakiyi girki..."

Dariya kawai tayi, wannan karin sun dade, watansu na hudu kenan rabon su da gida. Duk da ta wani fannin dadewar tayi mata dadi bana wasa ba. Hakan na nufin aikin da Malam Ma'azu kwano kamar yanda Hajiya Dije ta kira shi yaci. Daman tace a borno yayo karatun allo, a haka idan ka ganshi zaka raina shi, sai dai aiki yake kamar babu gobe. Tashin farko dubu goma Ayya ta ajiye mishi na bugun kasa, inda yace ta saka tafin hannunta kan wani rairayi da yake cikin falankin katako. Batayi musu ba ta saka, duk da tasan zancen gizo ba zai wuce na koki ba, ba nan bane wajen farko da sukaje da Hajiya Dije, kuma duk maganar shige dayace, Layla na rike da kurwar Rayyan, danma yana da dakakkiyar zuciya da sai abinda tace ne zaiyi.

Wannan ma suna shiga ta fara labarta mishi matsalarta akan Rayyan din, kafin yace yasan kasa zata nuna mishi komai, ta saka hannunta akan yashin, suna zaune suna kallon yanda yake rubutu yana sharewa yana sakeyin wani, kafin yayi numfashi mai nauyi yana dago kai ya kalli Ayya

"Yaron ki zai zama shahararren mai kudi, akwai nasarori da suke biye da shi. Shisa abokiyar zamanki ta kasa zaune da tsaye a kan shi. Saboda taje an duba mata yanda kaf gidan ba za'ayi mai arziqin shi ba. Yarinyar da kike magana da ita aka, idan baki tashi tsaye ba duk abinda zai samo a kansu zai kare, ke kanki ga katanga nan naga ana ginawa tsakanin ku"

Wani irin numfashi Ayya taja, tana duban Hajiya Dije, zuciyarta na wata irin dokawa

"Yaushe Maryama zata kyaleni in huta?"

Murmushin "Na fada miki ai" Hajiya Dije tayi mata

"Da nace miki ki dinga nemar wa yaranki ko da tsarine ca kikayi kamar Maryama ba zata iya cutar da su ba. Kin daiji da kunnuwan ki yanzun ai"

Kai Ayya ta jinjina mata, taji kam, ba waje daya ba biyu ba, kuma ta gasgata tunda zuwan karshe da Rayyan din yayi, saboda ta mishi magana akan Layla yasa shi daina shiga bangaren ta gabaki daya har suka koma. Sosai abin ya bata tsoro, ashe katanga ake mata da dan data tsugunna ta haifa, dan daya fito daga cikinta. Rashin imani irin na Maryama ba zai misaltu ba. Aiki Malam Muazu yace za ayi sosai akan Rayyan din

"Gaskiya kudin ki zaiyi yawa, saboda za'a yanka raguna baki da fari guda daya, da zuciyar su za'ayi aikin, sai an hada guda biyu za'a musanya su da ta danki da take rike a wajen su... Aikine babba, zan kuma baki garin maganin da nake so ki tabbata ko yayane shi yaron yaci dan ya karya katangar da take tsakanin ku"

Hakan kuwa akayi, kudaden duk daya bukata ta bashi su. Daman yace zata ga canji, ba karamin dadi take ji ba ganin yanda Rayyan din ya zauna a makaranta har tsayin wata hudu,mutumin da baya iya hada satika hudu batare da yazo Kano kona kwana daya ba. Shisa take shirya girkin nan da kanta. Duka zata hade abincin ta barbade, har Bilal ma yaci dan shima yana bukatar duk wata kariya da zata ba Rayyan. Dan ma shi tana kula da yanda yake janye jikin shi daga bangaren Maryama, ya rage shiga kamar da, hakan ba karamin dadi yake mata ba.

Gabaki daya cikin nishadi take a duka ranar. Saima da taji sallamar Bilal, da murmushi dauke a fuskar shi. Su Rukayya kance basa bambance muryar Bilal da ta Rayyan musamman yanzun da suka zama Samari, sannan idan a fisge ka kalle su zaka iya dauka Bilal ne, sai ya shigo sosai zaka ga Rayyan ne. Kamannin su har Abbu suke ba mamaki, yana kara jinjina karfin dangantaka ta jini, duk da mutane da yawa kan iya yin kamanceceniya batare da alaka ta komai ta hadasu ba.

Sai dai Rayyan yafi Bilal din haske, kuma yanzun ya dan fishi tsayi duk da su duka dogaye ne, Ayya kan cewa Abbu itama ai doguwar ce duk idan yace tsayin shine yaran suka biyo. Yanzun kuma Bilal na tara suma a kan shi, Rayyan kuma yana asketa kasa sosai sosai, kuma ya tara kasumba a fuskar da ta saka shi wani kwarjini na daban, Bilal gemu ne da samarin yanzun suke ajiyewa da har dariya yake baiwa Ayya. Wani lokacin ma fayau zakaga fuskar shi, ya aske komai.

"Ayya..."

Bilal ya furta yana fadada murmushin shi, kafin ya karasa cikin dakin yana zama kan kujera hadi da sauke numfashi

"Yan Zaria"

Ayya ta fadi tana saka Bilal din yin dariya, yayi kewarta matuka

"Harma mun zama yan Zaria kenan Ayya... Ina kowa? Wallahi nayi kewarki da yawa..."

Sosai Ayya take murmushi, tasan yayi kewarta, tunda yana iya kiranta sau biyar ma a rana. Itama idan ta cika awa hudu bata ga kiran shi ba sai ta neme shi. Rayyan ne ma harta saba, a cikin watannin nan hudune da take tunanin aikin Malam ne ya kirata sau biyu, daga gaisuwa yayi shiru, sai tace ta dinga tambayar shi makaranta da lafiyar shi da ya dinga amsa ta dai-dai

"Ayya gaisuwa ce kawai"

Ya fadi a hankali, da yasan yanda taji dadin gaisuwar da ko sau dayane a wata ya kirata. Tunda yai wayar hannu sai a wajen Bilal ta sami lambar shi saboda yanda bai taba gwada kiranta ba. Idan sunyi magana to Bilal ya bashi wayar shi ya gaisheta, shima daga yanayin yanda zai magana tasan a kunne kawai Bilal ya saka mishi wayar batare daya shirya ba

"Duk idanuwanka yayi zuru-zuru"

Dariya mai sauti Bilal yayi

"Jarabawa ce Ayya... Sai kinga Hamma, gara nima tunda komai na samu ina ci"

Numfashi ta sauke, ai baizo ba ballantana ta gan shi. Da kanta ta mike tare da fadin

"Allah yasa an rubuta a sa'a, bari in dauko maka abincin ku..."

Kitchen ta wuce ta dauko mishi kuloli guda biyu da cokula, mikewa Bilal yayi ya amsa yana ficewa daga dakin zuwa dakin su, tunda ya karya kwana ya hango Layla a tsaye, jikinta sanye da wandon jeans ruwan bula da riga ja a jikinta, sai hula, tayi mishi kyau tun ta gefen ta daya hango, yana jin zuciyar shi ta matse a kirjin shi, cikin shekarun nan ya fahimci muhimmanci da Layla take da shi a rayuwar shi. A cikin shekarun ne kuma yayi kokarin janye jikin shi saboda yanda kusancinta da Rayyan yake wahalar da shi.

Suna zaune su biyu zata zo waje, daga nesa zaka ga yanda idanuwanta suke kafe kan Rayyan, lokutta da yawa in ba kuka Rayyan din ya sata ba, sam bata kula da yana waje. Idan Rayyan yana nan idanuwanta a rufe suke daga sauran abubuwan da bashi ba. Ranar da Rayyan ya riko hannunta ji yayi wani abu na budewa a kirjin shi, shisa yanzun yake tashi yana basu waje, yafi mishi kwanciyar hankali, abinda bai gani ba bazai bata mishi rai ba sam.
Chapter 25 · 0% Book details