← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 93

Sashe 9

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta furta muryarta na rawa, dana sani ne yai mata rumfa, saboda tashin hankalin da take ciki na rashin sanin mai maganin zaiyi tunda a kan idanuwanta taga karfin aiki irin na Malami Mainasara.

"Bakwajin magana wallahi, na rasa me yasa kuke ajiye kananun abubuwa da yaran nan zasu iya dauka su hadiye...."

Ahmadi ya karasa maganar yana daukar Rayyan da a lokacin duka shekarun shi basu karasa hudu ba

"Me ka ci Rayyan? Fadamun kaji?"

Kai Rayyan din ya girgiza mishi alamar shi baici komai ba. Babu dabar da Ahmadi bai mishi ba, amman yace shi shayi kawai yasha. Barin shi yayi tunda zai fita aiki, yace ma Maimuna din da taga ko zazzabi ya fara ta dauke shi ta kai shi asibiti, kudi ya dauka ya bata, duk da yakan ba kowaccen su kudi su ajiye tsaron laluri koda wani abu na gaggawa zai taso shi yana wajen aiki. Yinin ranar Rayyan wasan shi yake kamar komai bai faru ba, itace ta wuni ta kuma kwana da zazzabi.

Har alkawari tayi na cewa in dai komai bai sami Rayyan ba, har abada ta daina bin Malamai zata cigaba da addu'a tana shan karya tambaya dai da kaikayi koma kan mashekiya, babu kalar addu'a da alkawurran da bata dingayi ba. Daga wannan zazzabin da takeyine ya juye mata laulayi mai zafin gaske. Ta sha wahala matuka, cikin da ta samu kuma na kara daga kimar aikin Malam Mainasara a idanuwanta. Bata yaye Rukayya ba kuma ta sami cikin Shamsu, kamar yanda tayi a haihuwar Khalifa da Zubaida, harma da Rayyan. Duk yanda Khadi taso su koma wajen Malam Mainasara kiyawa tayi, dan ta tsorata da lamarin shi akan Haris, batasan meye ya bata ba har Rayyan yasha, tsoro kuma ya hana ta furtawa kowa zancen, har aminiyar tata Khadi.

A cikin shekarun biyar din nan, a gaban idanuwanta Rayyan, Bilal da sauran yaran suke girma, amman na Rayyan da Bilal ba ita kadai yake baiwa mamaki ba, har mutanen da duk zasu gansu. Kowa zancen yanda suke tasowa kamar yan biyu yakeyi, duk da akwai banbancin shekara daya da watanni har shida a tsakanin su. Amman hatta tsayin su dayane, dan hasken fata kawai Rayyan yafi Bilal, dan shi Rayyan farine tas-tas, Ahmadi ne yakan kaisu aski, hatta da askin iri daya akeyi musu. Kowa yan biyunta yake kira, idan baka sani ba ba zaka taba cewa ba yan biyu bane, ita kanta Maimuna bata gyarawa mutane in sun fadi.

Balle kuma duk a cikin yaran Rayyan ake cewa yafi kowa kyau tunda shi yake kama da ita, shisa kamannin shi da Bilal ya baci, ko ita in ta gefen idanuwa suka gitta ko tana daga daki taji muryoyin su bata gane wanene a cikin su, balle duk kayan da Ahmadi zai siya iri daya yake siyarwa Bilal da Rayyan din.

"Ka dauki jakar ka?"

Ta tambayi Bilal din

"Hamma ya daukar muna..."

Ahmadi bai yarda da wani bai girmi wani da wasu shekaru ba, ko wata daya wani ya baka a cikin gidan saika bashi girman shi, kuma idan ya saka abu sai kayi. Da yake kaunar da take tsakanin shi da yaran mai girma ce, kowa bayason abinda Abbu zai mishi fada ko yayi fushi.

"Allah ya tsare, ka kula da Hamman ka kaji ko?"

Cewar Maimuna, duk da tasan Rayyan ne ya kamata ya kula da Bilal din, sai dai rigimar Rayyan a yan shekarun shi har mamaki take ba Maimuna, ga taurin kai kamar mutanen farko, idan abu yakeyi ko kashe shi zatayi saiya koma ya karasa, yanzun ma Ahmadi ya hana mata dukan shi, a cewar shi zai kangare. Taci gaba da mishi addu'a kawai. Amman ko yaran gidan Yaya Ayuba suka shigo, har wanda suka girmi Rayyan basa shiga gonar shi, duka yake musu, ga rikicin shi baya rabuwa, in ana fada dashi in bashi ya hakura ba, haduwa goma in kukayi sai ya kara cakumarka, abinda Maimuna ta kula dashi yan watannin nan, Bilal ne kawai zai shiga tsakani in ana fada da Rayyan din ya hakura.

Wani lokacin in Bilal yaita janye shi sai fadan ya koma kan Bilal din, tana kuma kula da yaron baya taba daga hannu da sunan ya rama duk wani duka da Rayyan din zai mishi, sai dai in karewa zaiyi, har sai yaga zuciyar shi tayi sanyi tukunna zaka ji yace mishi

"Ka daina fada Hamma, Ayya bata so, Abbu ma bayaso, nima bana so, ka daina"

Amman idan ba Bilal ba babu wanda ya isa ya taba fadan Rayyan cikin dadin rai, yana kuka yana zillewa zata samu ta rufe shi a daki. Amman ko kowa ya manta inya fito saiyaci gaba. Har kuka tayi shekaranjiya akan taurin kan Rayyan, sai take ganin kamar abinda yasha ne yake saka shi wannan abubuwan, kamar tana da laifi a kaddarar Rayyan, kuka takeyi har a sujjada tana rokon idan wani laifin ne ma Allah ya jarabceta ta wani fanni bata kan yaranta ba, kishi da Maryama ba tasan yanda zata bari ba, amman bin Malamai ta hakura dashi, duk da yanzun tana jin kamar ta aiki Khadi a buga mata kasa akan Rayyan, amman tana tsoron a gano mata abinda zai kara daga mata hankali.

Har waje ta fito taga Ahmadi ya tattara kan yaran

"Ayya sai mun dawo"

Haris ya fadi da murmushin da baka raba fuskar yaran dashi, sai ta tsinci kanta da mayar mishi da murmushin

"Allah ya tsare, ku kula da kyau, ayi karatu kuma"

Kai ya jinjina, ya juya kenan sukai karo da Rayyan, da kafin wani yai motsi ya dauke Haris din da mari yana saka Ahmadi karasowa ya tallafe mishi kai

"Rayyan... Bana hanaka dukan yayyanka ba? Haris din ba Hamman ka bane ba? Ka bashi hakuri yanzun nan"

Kallon Ahmadi din Rayyan yayi kamar zaice wani abu, sai kuma ya fasa yana kama hanya ya nufi waje, Bilal na rufa mishi baya da saurin shi. Numfashi Ahmadi ya sauke

"Allah ka tausasa mun zafin zuciyar yaron nan. Allah ka tausasamun shi, kai kabani, Allah ka bani ikon sauke amana"

Yake fadi a cikin ranshi,kwatankwacin addu'ar da yakanyi wa duka yaran duk lokacin da zasuyi wani abu ba dai-dai ba, musamman Rayyan da bayason yawan dukan shi saboda kalar yaran ta fita daban duk a cikin yaran. Haris da yake tsaye ya sadda kan shi kasa Ahmadi ya kamo

"Haris saika dinga hakuri da kanin naka kaji ko?"

Murmushi Haris yayi mishi

"Ni na buge shi Abbu, bangani ba amman"

Kai kawai Ahmadi ya jinjina, yana kama hannun Haris din, ya juyo ya kalli Maimuna da fuskarta take dauke da ban hakuri kan halayen Rayyan din, murmushin karfin gwiwa yayi mata

"A dawo lafiya, ka kula da kanka"

Ya furta a hankali

"Kema haka"

Ya fadi suna ficewa, daki ta koma tana sauke numfashi. Da tunanin halayen Rayyan manne a zuciyarta.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:06 PM - 111: Nov 1, 2020

04

1993, Kano.

Zata iya cewa tunda Ahmadi yabarta tafiyar nan take shiri, kusan sati daya kenan. Sau daya ta taba tafiya mai nisan awa biyu. Wani lokaci ko da irin hakane, Ahmadi baya barinta

"Tsoro ya miki yawa Maryama... Shisa banason kina nisa ke kadai"

Yakan ce, kuma da gaskene, har tsiya akeyi mata a gida wasu lokuttan, ace da tazo a karkara ba zatayi kyawun gani ba. Dariya kawai takanyi ta kyale su, sau daya kafafuwanta suka taka kauyen Kankia da yake a jihar Katsina, shima rasuwa Mannira ce, matar Yayanta Deeni. Zata tuna yanda aka kai ruwa rana kafin a barshi auren Mannira, na daya bata kasance daga danginsu kamar yanda suka saba ba, duk da yanzun wasu na bijirewa auren dangin. Amman rabon tilar yarinyar su Laila ne kawai ya saka shi kafewa da watsi da maganganun da kowa yakeyi na yaren Mannira

"Ka rasa wa zaka jajibo kana zaune lafiya da matarka sai banufiya, salon duk tazo yanda ta lashe maka kurwa ta lashe kurwar sauran yaran ko?"

Maryama ta tuna maganganun Mahaifiyar su lokacin da yazo mata da zancen auren Mannirar, kowa a dangi da abinda yake fadi, mahaifin sune kawai ya bashi goyon baya, sosai ya dinga fada

"Nayi bincike, iyayen yarinyar nan mutanen kirkine, suna zaune da kowa lafiya. Ita ma nagartacciya ce, addinin musulunci dai shi muke bi, kuma a sharuddan da aka kafa mana na neman aure, bamuda wani dalili na hana shi aurenta"

Hakan yasa dole kowa ya hakura, amman badan anaso ba, yanda yan uwa suka daga hankalin su akan auren Deeni da Mannira, ko matar shi da zai hada zama da Mannirar bata tunanin ta damu haka, ko ita da suka zauna da Deenie suna zancen ta jinjina al'amarin matuka

"Ni banki ka kara aure ba Yaya, da ba'a karawa nima da ina gidan wani ba Ahmadi ba, amman banufiya fa, ka dai kara duba lamarin"

Dan yanda sukayi kaurin suna wajen shaidar da akeyi musu ta maita da tsafi na sanyaya jikinta

"Duk musuluncin banufe sai yayi tsafi"

Haka takanji ana fadi, tana kaunar Deeni har ranta, bata son abinda zaizo ya cutar dashi sam.

"Ke dai kiyimun fatan alkhairi kawai"

Deeni ya fadi yana dariya, sai gashi daga baya kowa na yabon kirkinta. Cikin kankanin lokaci ta shiga zukatan jama'a. Maryama da kowa sun alakanta hakan bayan rasuwar Mannira mintina kadan bayan haihuwar 'yarta mace. Mutuwar ta daki Deeni ba kadan ba, har akayi jana'iza baisan inda kan shi yake ba. Kowa ya budi baki ca yakeyi rabone kawai ya hada kaddarar Mannira da Deeni, shisa duk yanda akaso hana shi aurenta yaki ji, ashe ma zaman nasu bamai tsayi bane, tunda duka watannin su sha hudu. To lokacin ne tafiyar da tayi mai tsayi, shekaru kusan biyu kenan da suka wuce.
Chapter 9 · 0% Book details