← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 93

Sashe 63

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan tasan halin Jabir baya gajiya da tsokanarta, kawai dan yaga tana mitarta da kai kara. Wucewar yayi, bai jima ba ya dawo. Mami yasan ba sha zatayi ba, ruwa ya siyo mata, shi ya siyowa kan shi coke. Suna zaune aka ce musu result din ya fito

"Mami kiji me zaice, jiri nakeji Allah"

Kai Mami ta daga mata, nan ta ajiye robar ruwan da ta fasa ta dan sha, sai Layla take jin ta dan samu, ba kamar sanda suka fito daga gida ba, har ranta ta dauka ciwon ajaline ya kamata. Zaune sukayi abinsu ita da Jabir yana mata hirar wani film da suke kalla su dukan su mai suna Blind spot

"Hamma banyi nisa ba, kabarni, bana son jin me zai faru..."

Dariya yayi, ya bude baki yayi magana ya hango Mami, yanayin ta na saka shi mayar da bakin shi ya rufe, saboda a hargitse take, a hargitse kuma ta karaso inda suke

"Ki bude bakin ki Layla, ki fadamun karyane, ki ce mun likitoci da kan su nayin kuskure, na'urar su na samun tangarda..."

Cike da rashin fahimta suke kallon Mami da take magana kamar ta sami tabin hankali

"Mami..."

Jabir ya fara magana Mamin ta katse shi ta hanyar daga mishi hannu, idanuwanta kafe suke cikin na Layla

"Ki tashi muje ki fada mishi ke din budurwa ce, ki kalli idanuwan shi ki fada mishi babu yanda za ayi ki samu ciki!"

Wannan karin har mutanen da suke wajen sai da hankulan su ya tattaru ya dawo kan su, robar lemon da take hannun Jabir tana subuce mishi

"Ciki? Mami ciki? Bashi da hankali? Wanne irin ciki kuma?"

Layla tun daga kalmar "ciki" komai ya daina karasawa kwakwalwar ta, in dai ciki likita ya gano mata tasan inda ta same shi, in dai da gaske akwai wani abu a cikin ta tasan ya akayi, ba karya yayi ba, na'urar su bata da matsalar komai, kwakwalwar ta ce ta samu tangarda, tunaninta ne ya yaudareta da alamomin duk da ta dinga gani amman ta kasa fahimta, ba infection bane ya dauke mata al'ada, shigar cikine.

"Layla..."

Mami tayi maganar tana girgizata cikin yanayin da ya sata daga ido ta kalli Mami din

"Ciki Mami... Ciki ne da ni"

Ta karasa cikin wata irin murya da yasa wani abu kullewa a cikin Jabir, yaune ya fara sanin tashin hankalin, Mami kuma da ta yanke jiki ta fadi tana kara mishi wani sabon tashin hankalin, ya sha ganin yanda duniya take birkicewa mutane a fina-finai. Yau a gaske yake ganin yanda duniyar ta karkata ta juya da shi a ciki, kamar film haka wani gefe na kwakwalwar shi yake daukar hoton komai, kafin ya tsugunna a kasa cikin lemon daya zubar yana kama Mami, magana yake amman sautin muryar shi baya fita saboda tashin hankali.

Cikin Nurses din wajen ne wasu suka rugo dan su taimaka mishi, har aka dauke Mami yana tsugunne a wajen, Layla na zaune ko motsi ta kasa, tun tasowar shi duk wata damuwa tashi kafin Mami ta sani Abbu ya sani, ya saba abu koya kai ko bai kai ba ya nemi Abbu, shine babban abokin da yake da shi saboda mutum ne shi da yarda da mutane takewa wahala, shisa yanzun ma wayar shi ya laluba yana kiran Abbu

"Abbu kazo Aminu Kano, Layla bata da lafiya"

Ya iya fadi saboda kirjin shi da yayi nauyi, bayason fadama Abbu cewar Mami ta yanke jiki ta fadi, baima ji me Abbu yake fadi ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana sakata a aljihun shi. Yana wani irin sauke numfashi yake kallon Layla

"Ciki gare ki Layla?"

Ya bukata yanajin maganar ta fito mishi kamar da wani irin yare, saboda kalamai ne da baisan yanda za ayi ace sun gifta tsakanin shi da kanwar shi ba, tsakanin shi da Layla, sai da ta dago kanta tana kallon idanuwan shi da suke rokonta da ta karyata maganar, ko da ta zamana da gaskene ta saukaka mishi tashin hankalin da yake ciki ta karyata. Amman bata san ta inda zata fara ba itama, ta dauka ta gama fahimtar menene shock, sai yau tasan da gaske komai zai iya tsaya maka cak, ciki harda emotions dinka

"Ciki ne da ni Hamma"

Ta karasa maganar da dariyar da batasan ta inda ta fito ba, duk da kuwa tana jin idanuwanta cike suke taf da hawaye

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Jabir ya furta yana zama a kasa, cikin asibiti, batare daya damu da cewa cikin lemar lemon daya zube bane, balle kuma ya damu da cewa fararen kayane a jikin shi. Tarin tashin hankalin daya kunno musu yake hasasowa, MARTABAR SU da ta samu gurbata ta fannonin da ba zasu misaltu ba ke mishi yawo, rayuwar kanwar shi da ta canza har mutuwarta yake dubawa.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Dec 26, 2020.

24

Can nesa Layla take jin duk wata magana da sukeyi, ba zata ce ga abinda ya dinga faruwa ba, daga asibiti, zuwan Abbu, dawowar su gida, banda sautin kukan Mami babu abinda take ji, dan yanzun haka da suke a tsakar gidan ta samu wajene ta zauna a kasa, gefen Mami da ta kasa shiga daki ta durkushe a wajen. Kuka takeyi kamar ranta zai fita, dan har yanzun ta rasa ta inda zata fara yiwa Abbu bayani, sanda yazo asibitin ta farfado, dan haka suka dawo gida, ita da shi a mota daya, sai Jabir daya kama hannun Layla yana sakata a motar da suka zo suka taho.

"Wai dan Allah wani a cikin ku ya bude baki yayi mun magana, tun dazun na tambaye ku abinda ya faru"

Abbu yake maganar da wani yanayi a muryar shi, hankalin shi a tashe ya same su asibiti, sai dai lokacin harma sun fito, tun daga can kuma Mami take kuka, sau daya ya tambayeta abinda ya faru, da bata amsa ba sai yayi shiru saboda bayason su fada mishi abinda zai saka shi kasa yin tuqin su iso gida.

"Layla me ya faru? Wani abin suka ce ya same ki?"

Ya karasa tambayar yana kallon Layla da ta dago idanuwanta tana saka su cikin na shi, bata san me zata ce mishi ba, saboda har yanzun wani irin shiru take ji cikin kanta. Kafin jikinta gabaki daya ya dauki bari, zuciyarta na soma dokawa, girman abinda yake faruwa da ita yana danneta, so take ta bude bakinta, ba ta dan ta bawa Abbu amsa ba, sai dan ta kira sunan Allah, ta furta kalmar

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ko zata samu sauki, ko Allah zai kawo mata dauki abinda yake faruwa ya zama mafarki, amman ta kasa, Abbu kallon shi ya mayar kan Jabir da karo na farko a duniya yake son kasancewa ko ma ina ne da cikin gidan, banda fuskantar abin nan da yake faruwa da su

"Abbu karka tambayeni, dan Allah karka sa in fara fada maka"

Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, zuciyar shi zafi takeyi, so yake yabar wajen, amman ya kasa, ba kukan Mami bane baya ci mishi rai, tunanin halin da Abbu zai shiga ne yake hautsina mishi lissafi.

"Ciki gare ta, cikine a jikin Layla... Ahmadi ciki"

Mami ta karasa tana jin kamar ana zare mata rai, ya kusan mintina biyu maganganunta na yawata mishi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, so yake ya ga shin shi kadai ne yake ganin wani duhu-duhu ko kuma garin ne gabaki daya ranar da ake kwallawa ta lumshe, amman da ya bude wannan karin ma duhun ya sake gani, kamar a cikin duhun wani abu na jujjuya mishi. Ba dan Bilal daya fito daga bangaren Ayya da kofi a hannun shi ba, ya hango su ya fara karasowa in da yake ganin kamar Abbu na shirin faduwa, yanayin da ya saka shi yin jifa da kofin zobon da yake rike da shi ya karasa ya tallafe shi yana taimaka mishi ya tsaya kan kafafuwan shi, tabbas da zancen ya bambanta

"Subhanallah, Abbu..."

Bilal ya kira zuciyar shi na wani tsalle cike da tashin hankali, Abbu kuwa kafadar Bilal ya dafa yana samu ya tsugunna saboda kafafuwan shi da suke rawa, kokawa yake da numfashin shi saboda tashin hankali, baiga ta yanda Mami zata ce mishi Layla na dauke da ciki ba. Kirjin shi na zafi yake kallon Mami

"Maryama ki fadamun abinda zuciyata zata iya dauka... Dan girman Allah, rokon ki nakeyi"

Hannu ta saka tana share hawayen da suke sake zubo mata, ta bude bakinta yafi sau biyar tana rasa kalaman fadi, haka kawai Bilal ya tsinci kan shi da shiga tashin hankali, bai san me yake faruwa ba, amman zuciyar shi duk ta gama birkicewa, hannun shi yaji Abbu ya kamo

"Bilal kaji me tace? Wai Layla ce take dauke da ciki, yata Bilal, yarinyata, amana ta"

Runtsa idanuwan shi Bilal yayi, ya bude su a cikin na Layla da take kallon shi, duniyar na karasa hautsine musu a lokaci daya. Kai ta girgiza mishi a hankali tana neman hawayen da zasu sama mata sauki ko yayane. Amman ta rasa su, sunki fitowa. Tsaye Bilal yake a waje daya, amman duniyar duka juyawa takeyi da shi, kamar wanda aka dauka ana zagayen cikar shekara haka yake jin shi, so yake wani ya taba shi ko zai daina jujjuyawa haka, kamar an amsa rokon shi yaji hannuwan Ayya akan kafadar shi, hannun da yake da yakinin zai gane shi a cikin dubban hannaye.

Hannun daya kama nashi a lokacin daya rasa kowa, hannun daya taimaka mishi tun kafin ya budi bakin rokon hakan. Ayyar shi, juyawa yayi yana ganin damuwar da take kan fuskarta

"Ayya"

Ya kira da wani yanayi da ya sata fadin

"Menene? Me akayi maka? Me akace kayi?"
Chapter 63 · 0% Book details