Sashe 29
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda Yaya Ayuba ya kula da yanda yake yawan ganin sun zo gida daga makaranta, shima nashi yaran biyu da suke karatu a Bauchi motar ya hadasu da ita. Kuma ya dauki shawarar Yaya Ayuba. Akwai 'yar karamar mota a gidan da yakan dauka wani lokaci, ko in za'a kai Mami unguwa. Tunda ita Ayya tana da abin hawa. Ya kuma rigada ya kira Bilal tun dazun yace su taho da Rayyan, shigar da sukayi kuwa a fuskar Rayyan zaka fahimci yanda yake a takure, dan ko zama cikin kujera sosai yakiyi, a gefen hannun kujerar da Bilal ya zauna shima nan ya samu ya zauna.
Yana saka Abbu jinjina wannan lamari. Ace ka haifi yaro, kiri-kiri yana gudunka, shekaranjiya Rayyan na hango shi yayi baya yana komawa inda ya fito, abin yayiwa Abbu ciwo ba kadan ba. Ya kasa sabawa da yanda Rayyan yake baya-baya da shi. Ko lambar wayar Rayyan din bashida ita, baya kuma zaton Rayyan yana da lambar shi a waya shima. Inda ace ya yarda da sihirine, yana kuma da abokin gaba, tabbas zaice an saka mishi hannu ne, an shiga tsakanin shi da danshi. Amman yasan bashida abokin fada, babu wanda zai kuma zarga da lokacin batawa wajen bibiyar rayuwar shi.
Dauke idanuwa yayi daga kan Rayyan yana mayarwa kan Bilal bayan sun gaisa
"Daman naga zirga-zirgar da kuke tsakanin Kano da Zaria tayi yawa, ga Layla kuma yanzun. Shisa nace wannan karin ku koma da mota, kunga duk idan zaku zo ba sai kunyi ta jigilar zuwa tasha ba"
Murmushi Bilal yayi yana tashi ya karbi mukullin motar da Abbu ya dago hadi da cewa
"Allah ya kara arziqi da lafiya Abbu...mungode..."
Ya koma ya zauna yana kallon Rayyan
"Hamma ga mota Abbu ya bamu"
Kamar Rayyan din baya dakin, sai lokacin ya dago da idanuwan shi yana kallon Bilal
"Kai kasan ban iya tuqi ba, me yasa kake fadamun?"
Rayyan ya karasa maganar yana dan kankance idanuwan shi saboda yanda kanshi yake bala'in sarawa tun da Bilal yace mishi Abbu yana kiran su. Sanda yake dosar dakin Abbu din ji yake kamar ana zare mishi rai. Kafafuwan shi ma rawa suka dingayi kamar ba zai iya karasawa ba, shisa kallo daya yayiwa Abbu ya mayar da kanshi ya sauke. Muryar Abbu dinma cikin kunnuwan shi kara mishi abinda yake ji takeyi. Jikin shi yayi wani irin dumi kamar gidan biredi. Duk akan za'a bada wata mota ne aka kira shi ya shiga wannan halin.
Duk ranar bayajin dadin jikin shi, shisa ko da Bilal yayi mishi magana baiyi gardama ba ya mike, yasan halin Abbu, in har magana yake sonyi dasu da gaske, idan ma baije ba shi zaizo ya same su har daki, da kuma yasan yanda Rayyan din yake ji duk idan sukayi kusanci taku goma a tsakanin su da bai fara zuwa kusa da shi ba, balle harya shigo dakin da yake yana saka iskar duk da take dakin tayi mishi kadan, zai rantse ko meye a tsakanin su da Abbu, yana girma ne abin ma yana kara girma. Ga mugaye mafarkan da yake fama dasu daya runtse idanuwan shi.
Rabon shi da bacci da daddare batare da taimakon wasu kwayoyi ba harya manta, zuwa yanzun saboda karatun shi yana fahimtar abubuwa da yawa da suka shafi kwakwalwar shi, yana kokarin ganin ya fassara matsalolin shi scientifically batare da zargin iskokai da yakan ji ana hada shi dasu ba. Yasan yana da matsaloli kala-kala, ciki harda abinda ake kira depression a turance, yanayin da kwararrun likitocin daya gani a fannin kwakwalwa sun kasa taimaka mishi wajen gano abinda ya haddasa mishi depression din. Kuma shine ma a fadar su ya jaza mishi insomnia. Shisa baya iya bacci da dare, babu wanda yasan baya iya bacci da dare tun tasowar shi.
Har Bilal da suke kwana waje daya su tashi baisan baya iya bacci da dare ba, tunda zai kwanta ya huta, zai saka hakarkarin shi a kasa, lokacin kuma duk da zaiji baccin to yana runtsa idanuwan shi ya fara wasu irin hargitsatstsun mafarkai da baya iya tuna farkon su balle karshen sune suke tashin shi. Da farko-farko magungunan da aka bashi kala biyu wato Anti-depressant sun dan fara mishi aiki, tunda yana bacci, amman magungunan suna saka mishi wani irin qunci na daban, sun kara mishi rashin hakuri da mutane.
Abu kadan ne yake harzuqa shi fiye da yanda yakeyi da. Daga baya ma guda biyu sun mishi kadan, bayajin komai idan ya sha. Yanzun a halin da yake ciki guda hudu asibiti sukace ya dinga sha. Kuma ba'a bayarwa da yawa, na sati biyu suke bashi, idan ma ya shanye kafin lokacin yasan ba zasu sake siyar mishi ba. Sai dai cikin gidan da yake haya akwai yaro daya daya kula yana siyar da kwayoyi, a wajen shi Rayyan yake siya, akwai wanda suka fi na asibitin karfi, kuma suna taimaka mishi ba kadan ba. Yanzun ma so yake ya tashi yaje yayi wani hadin da zai batar mishi da ciwon kan da yake ji. Inda yasan maganar wata mota ce Abbu zai mishi sam bazai zo ba.
Idan waje baya kama dole ya hau mota ba, bata dame shi ba. Ko makaranta yana rigan Bilal fita, daya saka earpiece da wayar shi zai taka da kafafuwan shi, yafi zabar yayi tafiya akan ya hau mashin. Saboda ita kadaice abinda yakan taimaka mishi ya samu natsuwa wasu lokuttan.
"Jikin ka baya maka ciwo?"
Bilal kan tambaye shi wani lokaci, kafadu yakan dagawa Bilal din kawai tunda baisan yanda zai fara mishi bayani cewar wannan doguwar tafiyar da yakeyi wani lokaci ita kadaice katangar da yakeji a tsakanin shi da tabin hankali, lokutta da dama yanajin kamar zai ta kurma ihu saboda duhun da yakeji cikin kan shi. Wasu lokuttan har sallah ma bai samun nutsuwa idan yayita, kullum cikin neman wani abu da zai saka mishi natsuwar zuciya yake amman ya rasa. Haka yake rayuwa badan yanajin dadinta ba, amman babu wanda yake fahimtar haka.
Wani lokacin yakan ji dariya daga dukkan zuciyar shi idan ya addabi Layla. Ko yana ganin yanda take son kwala mishi wani abu a cikin idanuwan nan nata da suke fadar mishi da gaba amman babu yanda zatayi. Shisa idan bai ganta ba bayajin dadi, Layla kan samar mishi da natsuwa wasu lokuttan. Mikewa yayi, daga Abbu har Bilal binshi sukeyi da kallo harya fice daga dakin, kafin Bilal ya mayar da idanuwan shi kan Abbu da yake kallon kofa har lokacin da wani yanayi a fuskar Abbun da Bilal yakeji har cikin zuciyar shi. Shima mikewa yayi
"Abbu sai da safe"
Wani numfashi mai nauyi Abbu ya sauke yana fadin
"Sai da safe Bilal, Allah ya tashemu lafiya. Allah kuma ya saukeku lafiya idan bamu kara haduwa da safe kafin ku wuce ba"
Kai Bilal ya jinjina
"Amin. Zamu shigo ma ai in shaa Allah..."
Sallama yayiwa Abbu yana fita, dakin su ya nufa inda ya sami Rayyan a zaune da kofin ruwa a hannun shi. Da alama hankalin shi na wani wajen dan ko sallamar da Bilal yayi bai amsa ba. Shikuma yayi shirune saboda yanda kan shi yake sarawa har lokacin, yaki jin numfashin shi ya koma dai-dai. Iska bata kai mishi inda ya kamata, kwayoyin da ya sha yake jira su narke su fara mishi aiki ko zai dawo dai-dai. Shisa yake zaune shiru yana sauraren ikon Allah. Bilal gado ya hau ya matsa can yana kwanciya saboda baccin da yake idanuwan shi, kuma ya kasance cikin jerin mutanen da baccin su yake da muhimmanci a wajen su, sam abinda yake shiga tsakanin shi da bacci to gagarumine.
*
Idan tace yanda taga dare haka taga rana batajin zatayi karya. Bacci ko da ya saceta to barawo ne tabbas, haka ta kwana tana juyi, ta kwana tana tunanin a duniya abinda tayiwa Mami mai zafi haka da take son taga bayanta. Kamar ba ita ta aure mata miji ba, kamar ba ita tayi mata babban laifi ba, kamar ba ita ta sakata raba soyayyar Ahmadi da take ji har kasan ruhinta ba. Duk ta hakura, duk ta kauda kai, badan kishinta ya ragu ko kadan ba, ko giccin Abbu tagani ta bangaren Mami sai taji kamar zuciyarta zata fado.
Ranar karshe da taga Abbu yana dariya da Mami numfashinta barazana ya dinga yi mata. Dariyar Abbu ita kadai take son jin sautinta, a yanzun inda zata baiwa Mami duk wani abu data mallaka ciki harda dukiyar Abbu din ta fice tabarta daga ita sai shi zata mika mata da gudu. Amman Mami tabbas mayya ce, bata hada jini da nupawa ba kamar Layla, amman watakila kafin Allah ya dauki ran Mannira ta baiwa Layla kankarun maitar, ta kuma zo dasu cikin gidan nan ta raba su da Mami.
Duk abinda tayi mata bai isheta ba, tana hango tauraron Rayyan da Malam ya fada musu mai haskene sosai, shisa take son dishe shi. Saboda bata tsoron Allah, bata tunanin ya kamata ta kyaleta ta huta haka
"Allah ya isa tsakanina dake Maryama, wallahi ba zan yafe miki ba. Kin hanamun natsuwa, kudin dana tara ma kina neman sakani asarar su wajen malamai, me nayi miki haka?"
Ayya ta dinga fadi tana juyi har wayewar gari, kan kunnenta aka kira sallar asuba. Dakyar ta mike tana gabatar da sallah, addu'ar nemarwa yaranta tsari tayi tana mikewa ta wuce kitchen tunda tasan Rukayya ko da zata fito sai ta gama karatun Qur'ani da azkar dinta na safe. Kuma tana son su Bilal suci wani abu kafin su fita, akan ce
"Mayu sunfi samun damar kama mutum idan ya fita baiyi karin safe ba"
To su da Mayya zasuyi tafiyar tasu kacokan, gara ta basu duk wata kariya da zata iya, kafin ta samu ta kira Hajiya Dije dan samun mafitar wannan bala'in, farraku take so ayi ma Layla tsakaninta da Bilal da Rayyan. Gara ayi musu katanga ta bakin karfe yanda zata sama musu lafiya duk kowa ya huta. Ko nawane kuwa zata kashe dan ganin an rabasu, da ita Mami take magana.
"Mu zuba mugani Maryama. Ke din banza"