Sashe 55
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryarta da yake ji can kasa na kara taba shi, kamar bataji duk abinda ya fada ba, dan ta zabi amsa shine da
"Ina son ka, wallahi ina son ka da yawa. Dan Allah karka barni, Hamma ina son ka"
Ta karasa da kukan da ya saka shi fadin
"Ina zanje Layla?"
Dan tun daga dan yatsan kafar shi yake jin babu inda zashi yabarta. Baima san itace mutum na biyu mai matuqar muhimmanci a rayuwar shi ba sai yau, Bilal ne na farko, yau yasan matsayin Bilal ba zai taba haduwa dana kowa ba. Yana jin yanda zuciyar shi take zafi da rashin ganin Layla, amman awannin da suka wuce Bilal ya danneta a zuciyar shi da kan shi gabaki daya.
"Ina son ka"
Ta sake fadi, muryarta na isowa kunnen shi cike da firgici, baisan tsoron da take ji ba, amman ya taba zuciyar shi
"Ina son ki Layla, watakila yaune rana ta farko kuma ta karshe da zan fada miki, saboda nayi magana mai yawa yau, ina tayi har yanzun. Amman ina son ki, ko da bazan fada ba, zan nuna miki, ina nuna miki, ke ce bakya gani"
Ajiyar zuciyar da tayi na nutsar da wani abu a cikin kan shi
"Mafarki nakeyi ko Hamma? Daya daga cikin mafarkina ne yau ma"
Kai Rayyan ya girgiza mata, baisan soyayyarta na da yawa a tare da shi ba sai yanzun da yake jin kamar zata danne shi
"Zan sake fadi a karo na biyu, sai ina ganin ki, kafin lokacin ki kula mun da kanki"
Jin tayi shiru ya sa shi dorawa da
"Zan iya yarda dake? Zan iya yarda zaki kula mun da kanki?"
Shirun ta sakeyi sai sautin numfashin ta da yake tabbatar mishi da kuka take
"Kasheni kike son yi Layla? Idan banji zaki kula da kanki ba abin zai mun yawa, dan Allah kiyi mun magana"
Ya karasa yana kai hannu ya murza kirjin shi, inda zuciyar shi ke ciwo har kaikayi takeyi, amman murzawar baisa yaji kamar ya sosata ba
"Eh"
Ta fadi, kai ya jinjina ba sai ta tsawaita maganar ta ba
"Idan kin kasa bacci sai ki kirani muyi labari, ki sha tea din yanzun kinji ko?"
Bata amsa ba, amman yasan kai ta daga mishi, dakyar ya raba wayar da kunnen shi yana sauke ajiyar zuciya. Inda wayar Bilal take ya karasa ya kunna, yasan password din shi dan haka ya shigar, ya jira wayar ta gama kawowa, saboda Aisha ta fado mishi a rai. Yasan hankalinta ba'a kwance yake ba, kuma ba zata taba iya tako kafafuwanta gidan su ba, in dai yanda Bilal yake labarinta ne, yana da wannan tabbacin. Missed calls ya gani har guda sittin da bakwai, baibi ta kan su ba, lambar Aisha ya dubo, yana tura mata text
"Rayyan ne, muna asibiti da Bilal bashi da lafiya. Amman da sauki. Idan ya tashi zai kira ki"
Karantawa yayi yaga ko yayi sannan ya tura mata, kamar tana jira dan yana shiga tana dawo da amsa
"Subhanallah, Allah ya bashi lafiya. Dan Allah daya tashi ya kirani, da safe zan kira sai in zo in gan shi"
Har zai ajiye wayar saiya kula da tarin sakonnin da ta turo babu amsa, guda daya ya karanta
"Dan girman Allah Nawan ka rufa mun asiri, dan Allah be ok be fine, dan girman Allah"
Sai ta bashi tausayi, saboda yasan yanda firgicin nan yake
"In shaa Allah daya tashi zan kiraki sai kuyi magana. Da sauki fa, kiyi bacci"
Ya sake tura mata, wannan karin yana saka wayar a key, har zai ajiye kira ya shigo. Ya ga Ayya ce, zareta yayi daga jikin cajin yana dagawa
"Bilal!"
Muryar Ayya ta daki kunnen shi da wani yanayi
"Ayya nine"
Ya furta a gajiye, bakin shi harya gaji, tunda yake bazai tuna ranar karshe da yayi surutu mai yawan na yau ba, ya gaji da komai, so yake ko dan kwanciya yayi ko zai samu sauki.
"Rayyan.. Ina Bilal? Me ya faru tun jiya nake kira ba'a dagawa? Gobe da sassafe in shaa Allah zamu taho Zaria... Yau babu hali, Abbun mu yace mu jira shi mu taho gabaki daya, saboda akwai taron da sukeyi da ba zasu bar shi ba a wajen aiki"
Sai da ya bari ta gama yi mishi bayani, ya bude baki yaji tana fadin
"Maryama! Maryama... Ga Rayyan na samu"
Kamar zata fasa mishi dodon kunne, sannan tayi kasa da muryarta tana sake fadin
"Ina Bilal din?"
Numfashi Rayyan ya sauke
"Gashi nan muna tare, bashi da lafiya. Muna asibiti, Layla ma bata da lafiya tana asibiti, amman waje daban daban"
Yana jin salatin da Ayya takeyi tana kara wani
"In shaa Allah gobe da sassafe zamu taho... Allah ya basu lafiya"
Amin din a zuciyar shi ya amsa wannan karin yana sauke wayar daga kunnen shi hadi da kashewa. Ya jima anan tsugunne kafin ya iya mikewa yana komawa kan kujerar, jakar shi da take gefe ya dauka yana dubawa, ba shi da sigari ko daya, ya zuqe ta tas kuma bai samu damar siyan wata ba. Yana bukatar wani abu da zai dan nutsar da shi. Cikin magungunan Bilal da aka siyo ya duba, tunda duk yasan su, akwai sedative a cikin su kuwa. Budewa yayi yana ballar guda shida ya dauki ruwan da su Abdul suka kawo ya fasa ya shanye. Sauran maganin ya saka a cikin jakar shi, da safe yaje ya siyo wani yayi replacing da wanda ya dauka din.
Badan yana jin bacci ba, ya dai dora kan shine a jikin gadon Bilal din dan yadan huta. Wayar shima a gefe ya ajiye. Yana son Layla ta huta, a lokaci daya kuma yana son ta kasa samun baccin dan ta kira shi ya kara jin muryarta, tunda ba zai iya kiranta ba gara yaji muryarta. Baisan iya lokacin daya dauka a haka ba, amman lokaci zuwa lokaci yakan tashi ya dora hannun shi a kirjin Bilal din yaji ko zuciyar shi na bugawa, sannan kuma ya kara duba wayar shi ko Layla ta kira baiji ba. Kan kunnen shi aka kira sallar asuba, kan shi yake ji yayi nauyi kamar an dora mishi dutse saboda kwanaki biyu kenan rabon shi da samun bacci, sosai ya so ya tambayi Bappa yanda yayi ya samu bacci, saboda magani guda daya yaga ya sha, kuma bacci yayi har asuba.
Amman ya adana abinne a bayan zuciyar shi, duk idan ya samu wata dama zai san yanda zaiyi ya tambayi Bappa, ko a asibiti wajen karbar magani bai taba cin karo da wani ba, Bappa ne mutum na farko da ya gani akan Anti-depressant, duk da yasan akwai dubban mutane da matsalar depression, shi din dai ya fara cin karo da shi. Da tunani barkatai a kan shi ya daura alwalar asuba, dakyar ya iya tattara natsuwa ya kabbara sallah.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: 14 Dec, 2020
21
Su Ayya basu isa Zaria ba sai wajen bakwai da rabi, dan ma yau a karo na farko ta ga Abbu ya taka mota sosai. Wajen su Rayyan suka fara biyawa saboda Ayya, maganar farko da Abba ya fara bayan sun shiga dakin shine
"Me yasa zaku kawo shi wannan asibitin? Baku san na makaranta yafi kowanne kyau a Zaria ba? Kuma sai yafi samun kulawa fiye da ko Ina"
Kallon shi Rayyan yayi kafin ya sauke kan shi, saboda shi dai asibiti yasan Bilal yana bukata, ko da asibitin kauye aka kaisu a daren jiya in dai zasu iya bawa Bilal din wani taimako a halin da yake ciki zai barsu. Bai iya magana ba saboda kan shi da yayi bala'in nauyi, ga ganin Abbu ya kara mishi nauyin kan da yake ji ba kadan ba. Ayya kam bata bi takan Rayyan ba, kujera ta ja ta zauna kusa da Bilal tana tunanin a fadin duniya wanne ciwone zai kwantar mata da yaro haka
"Bilal..."
Ta kira da wani irin yanayi a muryarta dan tun suna hanya take tarbe hawaye, Abbu na kallon yanda lokaci zuwa lokaci take kai hannu tana goge gefen idanuwanta, gabaki daya hankalinta a tashe yake
"Me suka ce yana damun shi?"
Abbu ya sake fadi zuciyar shi na kara shiga cikin wani hali, dan shima bai taba ganin Bilal din ya kwanta ba
"Bashi da lafiya Abbu"
Rayyan ya furta dakyar, kyale shi Abbu yayi, duk da shikam daya ga Bilal din a zaune, zaije yayi magana a basu sallama su tafi asibitin makaranta gabaki dayan su. Amman a kwance yake da alamar bacci yakeyi. Mami ba damuwa da Bilal bane batayi ba, amman sun gan shi, ya kamata su karasa su duba Layla itama tunda tasan da wahalar gaske daga Rayyan har Ayya subar gefen Bilal din
"Bacci yake?"
Ayya ta tambaya tana kallon Rayyan da ya dan daga mata kai kawai. Gabaki daya zaman Abbu a dakin ya takura mishi, kan shi harya fara dawowa da ciwo. Wani abu yake tsikarin shi daya fita yabar dakin har sai Abbu ya tafi, amman saboda Bilal ba zai iya matsawa ko nan da can ba. Mami bata ce komai ba, saboda duk wata tambaya da zatayi su Ayya sun rigada sunyi. Rayyan din ba gaishe da su yake ba sai ta kama, zata iya haduwa da shi ya sadda kan shi kasa, ko yayi tsaye in da yake kan nashi a kasa har saita wuce sannan ya tafi inda zaije shima.
Kuma tun ranar da ta gansu da Layla sai ta kula kamar ya kara nisanta da ita. Ba abin bane ya dameta, amman batason kowa ya kullace ta, Ayya ma dan babu yanda zatayi ne shisa suke wannan zaman doya da manjan. Amman iya soyayyar da zata iya nuna musu a lokacin shine a tsawatar musu. Idan basu fahimceta yanzun ba, wata rana zasu fahimce ta.
"Maimuna kina nan ne? Mu dubo Layla?"