Sashe 24
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Maryama... Ke kinsan wallahi bokan ki yayi karya... Ke din banza balle kuma yar rikon ki. Ki fito tun wuri ki warware abinda kika kulla"
Dan tana da tabbacin karatun da Maryama taga Rayyan ya natsu yanayine bata so, shine abinda ya tsokane mata ido yasa take neman sabauta mata yaro. Hango wata kofar daki da tayi a bude yasata takawa tana karasawa. Abinda tagani yana saka duk wata jijiya ta jikinta tsinkewa. Rayyan ne da kayan wankin Layla da tayi bata kwashe ba ta ajiye can gefen gado suka dinga shigar mishi ido, ga kuma zaman da yakeyi. Hakan ya sashi mikewa, idan yana wani abu da hannuwan shi yana rage mishi tunani, ko zane ko aiki, ko karatun makaranta, sosai suke hana kwakwalwar shi tunanin komai sai abinda yakeyi din.
Yana daga wata hijab yaga mp3 din Layla hade da earpiece, shi ya sakama kunnuwan shi ya kunna, kusan wakokin yan kasar sudan da sukayi tashe wato Sahwa ne cike da mp3 din, su yake ji, ya saka mp3 din a aljihun shi. Kayan yake ninkewa a nutse, shisa sam baiji hargagin da Ayya takeyi ba, baima san tana bayan shi ba sai da yaji an dafa shi, juyowa yayi ya cire kunne daya na earpiece din dan yaga kamar magana takeyi
"Uban me kakeyi? Na shiga uku ni Maimuna... Rayyan kayan su naga kana linkewa kamar? Me kakeyi a dakin Maryama? Yaushe ka fara shigowa dakin ta?"
Dakuna fuska yayi yana kama hannun Ayya hadi da janta, bin shi take da matukar mamaki, saboda komai ya kwance mata, suna zuwa tsakiyar falon sukaci karo da Mami da ta yanke karatun azkar din bayan la'asar da takeyi ta fito saboda jin tashin hankalin da Ayya. Hakan nasa Ayya fisge hannunta da Rayyan ya riko
"Maryama ki kiyayeni, wallahi ki fita idona. Kin aure mun miji, kamar hakan bai isheki ba, na saka miki ido akan Bilal, bai isheki ba kin biyo Rayyan? Dauki dai-dai zaki mun kenan"
Murmushi Mami tayi, ta rasa kalar zargi irin na Ayya. Duk tsayin shekarun nan basu sa ta fahimci cewar bata da lokacin bibiyarta ba. Ko akan Ahmadi batajin zata iya bibiyar Ayyar, duk kuwa tarin kaunar da takeyi mishi. Idan bin Malamai ne Ayya take magana tana da kudin da zata iya basu. Kawai babu abinda ya fiye mata zaman lafiyarta a kabari ne, zata kwammace tabar mata Ahmadi idan za'a bata zabi tsakanin hakan da bin Malamai. Amman a duk rana gani takeyi bibiyarta takeyi.
Zuwa yanzun shagunan dinkinta biyu, ana kawo mata dubbanin kudi duk karshen watan duniya, ga hijabai da take dinkawa a cikin gida, sari akeyi garuruwa. Ga hidimar yaranta, sam bata da lokacin wani abu, kawa kwara daya bata da ita da zata nuna tace abokiyar shawara, idan abu yasha mata kai da bata son tattaunawa da Ahmadi, Haris ne abokin shawararta. Yau Rayyan ne kawai zai hanata fadawa Ayya maganar da zata kwana tana juyi. Alkawari ne tayiwa kanta, ko dan zumuncin da ke tsakanin yaran su ba zata taba mayar mata magana a gaban su ba.
Shisa ta girgiza kai kawai yanzun ma tana fadin
"Allah ya kyauta"
Ta juya
"Na fada miki, ki kyalemun yarana, kome zakiyi ki kyalemun yarana, ba zai miki kyau ba kina bibiyar mun yara"
Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi yana bude su akan Ayya
"Ayya..."
Ya kira muryar shi can kasa, baice yana son Mami ba, bai kuma ce bayason ta ba, bayajin komai a kanta sam-sam. Yanajin abu a game da Ayya da Abbu, amman shi kan shi ba zaice ko meye ba, lokutta da dama idan yagansu zuciyar shi nayin duhu, musamman Abbu, ko gwada magana yayi da shi sai kan shi ya fara sarawa, shisa lokutta da dama yake zabar ya wuce batare da yace mishi komai ba. Ya sha jin tana fadar cewa Mami zata barbada musu abu, shisa bayacin abinta. Lafiyar shi nada muhimmanci a wajen shi, kuma idan Ayya tace za ayi abu, ya tabbata za ayi.
Maganar da suke a tsakanin su bata da yawa, amman bata taba mishi karya ba, ita da Bilal na jerin mutanen da ya aminta ba zasu taba cutar da shi ba. Amman hakan baya nufin yana son hayaniyar da Ayya take yawan yi da Mami din, bai taba mata magana bane kawai. Yafi zabar ya wuce yayi abinda yake gaban shi. Yau dinne yake jin shi sama-sama. Ga Bilal da yaga ran shi ya baci kan maganar da bata kai ta kawo ba, Layla da har yanzun baiga alamar tana jin saukin da Mami ta kira mata ba. Ga Ayya yanzun da tazo tana wasu maganganu
"Ayya dan Allah ki tafi. Kin ga Layla bata da lafiya. Kuma dakyar tayi bacci"
Kallon shi Ayya take, tsoro bayyane a fuskarta
"Dan ubankan shanyewar da akayi maka har takai haka? Ni kake fadawa dakyar Layla tayi bacci? Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ayya ta karasa kamar zata fasa ihu saboda tashin hankalin da take ciki, abinda ko a mafarki bata hango bane yake faruwa a gabanta
"Ka zo ka wuce ka koma makaranta kafin ranka ya baci wallahi"
Numfashi Rayyan ya sauke, ran shi ya gama baci, babu wani bacin rai kuma da Ayya zata kira banda wanda yakeji yana taso mishi yanzun
"Zan koma makaranta. Sai gobe in shaa Allah"
Cikin idanuwa take kallon shi
"Idan na isa, idan ina da wata daraja a idanuwanka zaka wuce ka koma makaranta yau"
Maganganunta yake ji sun danne shi da wani irin nauyi, amman duhun daya taso mishi na son bijerewa maganar da tayi ya rinjayi koma meye ya fara shirin tasiri akan shi. Hannun ta ya kama yana janta har kofar dakin Mami din
"Zan koma Ayya... Sai gobe zan koma"
Ya fadi yana juyawa, baki a sake Ayya take kallon Rayyan harya juya yana komawa dakin Layla. A gaban idanuwanta, ba zatace ga yanda akayi ta isa daki ba, amman har wani jiri-jiri take gani saboda tashin hankali. Tana shiga daki a kasa ta zauna dabas, jikinta babu inda baya rawa. Tunda take da Rayyan ko da wasa bai taba gwada tayata wani aiki ba, asalima magana da ita wahala take mishi. Waccen shekarar da tayi jinya ya shiga dakin dai ya zauna, amman baice mata kanzil ba, harta ji sauki haka zai shiga ya samu waje ya zauna.
A fuskar shi babu alamar damuwa ko wani abu, idan ma su Zubaida da suke zaune suna surutu tashi yake ya fice kamar surutun nasu ya fara hawar mishi kai kamar yanda yake fadi. Amman yau Rayyan ne har yake fada mata Layla tana bacci, Rayyan ne da hannun shi tagani ya linke kayan Layla. Wasu hawaye nasu dumi ne suke zubo mata, ta jima a wajen, ko sallar Magriba dakyar ta samu tayi ta, tana zaune tana sharbar kukan ne Ahmadi ya shigo, dan duka yaran suna gidan Yaa Ayuba. Da haka zasu shigo su sameta tana wannan kukan.
Harta fara kewar Bilal tun ba'a kwana ba, tasan shine kawai baya iya daukar awanni bai ganta ba, ko leka kaine sai yayi
"Ayya nace tun dazun banganki bane fa... Kina lafiya dai ko?"
Ba zai taba gane yanda kulawar shi take kara mata son shi ba.
"Subhanallah, Maimuna... Lafiya? Me ya faru?"
Ahmadi ya fadi yana karasawa cikin dakin sosai, kamar haka take jira ta sake fashewa da wani kukan
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ahmadi ya furta cikin bayanannen tashin hankali
"Duk ina yaran? Suna lafiya? Dan Allah kiyimun magana"
Dan harya fara zufa saboda tashin hankali, muryar Ayya na shakewa saboda kuka ta soma fadin
"Tunda kake, Ahmadi tunda Rayyan ya mallaki hankalin shi ka taba ganin ya tayani aiki? Ko da shara ce?"
Cike da mamaki Ahmadi yake kallonta, ya dauka sun gama yanke hukunci addu'a ita ce kawai abinda zasu dinga bin Rayyan din da ita, ba zasu kara bata ransu akan shi ba. Idan ma sun bata ran nasu zasu yafe mishi da sun huce ko Allah zai sanyaya zuciyar shi. Tunda fushin su zai kara jefa shi cikin wani yanayin ne, kuma idan bai manta ba yau Bilal yace zasu tafi makaranta, hatta kudin Rayyan din ya hada yaba Bilal, to me zaiyi wa Ayyar haka da take wannan kukan.
"Idan nace maka Rayyan na linkewa wasu can daban kayan da suke sakawa abin ba zai baka mamaki ba?"
Bata ma rufe bakinta ba take ganin wani sabon mamakin karara a fuskar Ahmadi, hannu takai tana share kwallarta, wasu sabbi na samun damar zubowa, kada kai tayi cikin kunar zuciya
"Yanzun zaka yarda dani ko? Yau zaka yarda matarka na bibiyata, zaka yarda yarana take so ta rabani da su. Ahmadi na kauda kai iya yanda zan iya... Da Allah nake rokon ka kayi mata magana ta kyalemun yaro, ta kyalemun yarona"
Ta karasa tana sakin wani gunjin kuka. Tabbas zancenta ya daure mishi kai matuqa. Yasan Rayyan, a cikin yaran shi yanzun babu wanda yake kula da takun shi kamar Rayyan. Idan da gaske Ayya takeyi yana linkewa su Mami kaya to tabbas zargin da takeyi na da tushe, duk da a kasan ranshi yasan Mami ba zata tabayin abinda zai cutar da wanin shi ba.
"Kiyi hakuri, zan mata magana. In shaa Allah babu abinda zai faru. Dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan..."
Ahmadi yake fadi, dan kukan nata ya kara daga mishi hankali, bai fita daga dakin ba har saida ya tabbatar ta daina kukan, da kan shi ya zubo mata abinci ya kawo mata ruwa. Sannan ya nufi bangaren Mami. Duba jikin Layla yayi ya shiga yi, ya samu tana bacci, daga nan ya wuce bangaren shi, bai yiwa Mami zancen ba sai bayan sunci abincin dare harma sun kwanta sannan yace
"Maryama me yake faruwa ne?"
Numfashi ta sauke
"Me kake so ince maka? Na dauka ta gaya maka abinda ya faru"
Kai ya jinjina
"Baya nufin bana son ji daga bakin ki"
Murmushin takaici mai sauti Mami tayi, kafin ta labarta mishi iya abinda tasan ya faru tana dorawa da