← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 93

Sashe 14

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biskit daya Bilal ya dauka yana jifan Rayyan din da yake dariya dashi. Bai cika magana ba, amman randa duk ya saka shi gaba da tsokana sai ya rasa bakin ramawa. Musamman yanzun akan Aisha yafi samun damar tsokanar shi da yawa haka. Ko Rayyan din aka tsare ba zaice ga asalin yanda soyayya take ba balle kuma shi. Kawai yanajin Aisha har ran shine, baisan ko haka soyayya take ba, amman yasan ko dariya tayi sai ya ga kamar Layla, idan tana mishi surutunta ma, kominta yana mishi kamar Layla. Zai rantse lokutta da yawa har idanuwan Layla yake gani a cikin nata.

Shi dai yasan Layla ce dalilin kusancin shi da Aisha, Layla ce sanadin fara maganar shi da Aisha, idan akwai wani abu bayan wannan baisan shi ba. Saboda duka gidan Layla ce kawai take kula da ran shi ya baci, kowa kawai dauka yake ran Bilal baya baci, ba'awa Bilal laifi, ba zai manta ranar da tace mishi

"Hamma na rana daya ka nuna ranka ya baci, ka daina bari a cikin ka"

Murmushin da yakan yi ko da ranshi a bace yake shi yai mata

"Waye yace miki raina ya baci"

Dariya tayi

"Murmushin ka baya kaiwa cikin idanuwanka. Idan kayi murmushi ko kayi dariya harda idanuwan ka kakeyi, idan ranka ya baci idanuwanka basa dariya... Bansan ya zan maka bayani ka gane ba"

Numfashi kawai ya sauke

"Me yasa ba zaka fadama Hamma Rayyan ya bata maka rai ba?"

Kai kawai ya jinjina mata. Kuma tun daga ranar ko a haduwa sukayi tai mishi magana yanayin murmushi zata ce

"Waya bata ma Hamma Bilal rai?"

Ita kadai take ganewa, kuma ita kadai yakan fadama ran shi ya baci wani lokacin. Ayya damuwar Rayyan kawai ta isheta, shisa baya taba nuna yana cikin matsala, ko rashin lafiya saiya kwanta sosai da sosai ake ganewa. Sai yayi ciwo a tsaye ya warke babu wanda yasani sai Layla. Yanzun ma mikewa yayi yana ficewa daga dakin, wata irin yunwa yake ji, bangaren Mami zashi yaga ko ta dafa wani abin da yake ci, tuwo Ayya tayi miyar taushe, bayason dafaffiyar albasa, ko a dafaduka aka saka saiya tsince tas yake iya cin abincin. Yanzun tunda Rayyan ya zuba yaga tayi yawan da baisan ya zaiyi ya tsince ba, shisa ya hakura ya fito kawai.

Bai karasa bangaren Mami da yake lallabawa kar Ayya tagan shi ba, yasan bataso yana cin abincin Mami din, amman zuwa yanzun sai dai ta bishi da ido kawai, tunda taga ba zata iya hana shi ba, shine abu guda daya da Bilal ya taba gardama mata a kai, ta hana shi yaki hanuwa, amman kome zatace yayi baya taba nuna mata bayaso ko a fuskar shi kuwa. Layla yaci karo da ita

"Hamma..."

Ta furta da fara'a a fuskarta

"Me kuka dafa Layla?"

Bilal ya tambaya

"Wake da shinkafa ne, akwai miya. Amman yayyanka kayan miyar Mami tayi, bari ingani dai..."

Ta furta tana juyawa ta koma ciki, ta kai mintina kusan goma kafin ta fito da filet a hannunta da abinci harda cokali a ciki.

"Na ciccire albasar, amman saika duba akwai kadan a ciki..."

Karba yayi yana murmushi

"Ni nace bana cin albasa?"

Dariya Layla tayi

"Ba saika fada ba, kana barin shi a plate din abincinka da yawa...."

Wannan karin shi yayi dariyar

"Ke kam Allah ya shiryeki"

Yanajin dariyarta harya wuce, tun a hanya ya fara cin abincin saboda yunwar da yakeji, harya karasa daki

"Kai ba zaka daina cin abincin matar can ba, Ayya ta hana, sai an barbada maka abu tukunna ko?"

Saida Bilal ya hadiye abincin da yake bakin shi tukunna yace

"Abu nawa Ayya ta hanaka baka daina ba? Kuma kasan zato babu kyau ko a addini..."

Cewar Bilal din yana kara cakuda abincin hadi da diba ya saka a bakin shi

"Ni daban, kai daban, bana so kana cin abincin ta, amman ba zaka jini ba"

Shiru yayi ya kyale Rayyan din, idan wannan maganar ce sun saba, Ayya tagaji, shi dinne ya kasa hakura har yanzun. Duk cikin karatun duniya da ake mishi babu wanda ya rike da kyau irin cewa Mami zata barbada mishi abu yaci. Abincin shi yaci gaba daci kan shi a tsaye, yana ganin Rayyan din ya mike ya dauko uniform din shi da safa

"Wanki zakayi?"

Kai Rayyan ya girgiza

"Me yasa zan wanke, Layla zata wanke mun"

Yanda yayi maganar zaka rantse da Allah Layla din yar aiki ce a gidan ba 'ya ba.

"Layla baiwar kace? Me yasa kaci ka takurama yarinyar nan ne wai?"

Kallon shi Rayyan yayi

"Me yasa ita bata damu ba sai kai?"

Kai kawai Bilal ya jinjina, yana kallon Rayyan din ya fita. Ba shiga bangaren Mami yakeyi ba, idan ba wani yaron zai daka ya ruga ya shiga bangaren nata ba, itama sam bata shiga harkar shi tunda rashin kunya yake mata kamar zai daketa.

"Layla!"

Ya kira, itama sai lokacin da ta zubama Bilal abinci ta samu ta zuba nata, tana zaune da remote a hannunta da ta kasa tsayawa waje daya taji ya kwala mata kira

"Rayyan ne ko?"

Mami ta tambaya, duk da muryar su shida Bilal din ba ko yaushe ake banbance taba, amman tasan idan Bilal ne zai shiga har ciki, ba zai tsaya daga bakin kofa yana kwala ma Layla kira haka ba. Cokalinta ta mayar cikin abincin tana mikewa, marin da yayi mata yau da safe ta fadama kanta tana zaune zai zo nemanta, zatayi banza da shi, haka ma tacewa Mami data shiga tana kuka

"Ina zaune zai kirani, kinsan Allah Mami ba zanje ba nima, kowa yayi harkar shi"

Murmushi kawai Mami tayi, ita yanzun ta daina tsoma bakinta a tsakanin su. Tun tasowar Layla idan Rayyan din yai mata wani duka har ranta Mami take ji, tayi fada da Ayya yafi a kirga kan cin zalin Layla da Rayyan yakeyi. Sau biyu ta taba kaiwa Abbu kara, duka lokutta biyun kuma tana shan kunya, dan ko muryar Rayyan din Layla taji da gudu take fita, sai ta dauki ido kawai ta saka musu. Yanzun zata shigo tana kuka shabe-shabe, tana fadar yanda ita da Rayyan sun raba hanya, sai ya aiko kiranta ta ajiye koma meye takeyi ta tafi.

Kamar yanzun da ta ajiye abinci, jikinta har kyarma yakeyi ta fita

"Ki wanke mun"

Ya fadi yana ajiye uniform din a kasa

"Yanzun idan na gama cin abinci"

Kallonta yayi

"Idan ba zaki wanke mun ba ki fadamun, tun dazun bakici abincin ba sai yanzun?"

Kayan ta tattara tana turo labbanta gaba, ta wuce ta koma ciki, tana jin tsakin da Rayyan din yayi. Sai da ya dafe kirjin shi duk da yayi kokarin ganin bai hada idanuwan da ita ba, amman sai da taja zuciyar shi ta doka. Ita kuwa cikin daki ta shiga

"Ni fa zan taimaka in wanke mishi Mami, amman shine wai ba zan gama cin abincina ba, zaiyi fushi ya dauka"

Murmushi kawai Mami tayi tana kallon Layla harta wuce da wankin tana kuma cigaba da mita.

"Allah ya kyautata kaddarar da take tsakanin ku Layla. Allah ya kare maraicin ki"

Shine addu'ar da Mami take bin ta da ita a lokutta irin haka. Har tsoro takeji idan taga sunyi wani abin ita da Rayyan. Ko yara batajin suna cewa Hamma Rayyan ya basu abu, amman wani lokacin zakaga Layla da abu kuma tace shi ya bata. Har kudi a cikin aljihun makarantar shi duk idan ya bata wanki

"Ki mayar mishi da kudin shi"

Mami kance idan ta nuna mata ta tsinta, amman sau biyu ta gwada tana shan maruka, yana fada mata yanda bayaso tana zuwa kusa da shi

"Hamma zai sauke Jujun shi a kaina Mami"

Ta bawa Bilal kuma sau biyu shima ya mayar mishi, saiya Bilal din ya dawo mata dasu yace mata ca yayi ta rike, yana sane yake bari, ba zai bata da hannun shi bane ba. Ba kuma zai bude baki yace ta dauka ba. Shisa har a ranta Mami tana tsoron kaddarar da take tsakanin Layla da Rayyan din. Bata da wanda zata furtawa ne kawai, tunda ita ba wasu kawaye gareta ba, sirrinta yana cikinta, gara ta zanta damuwarta da Haris da ta fadawa wani can. Shikuma yanzun ya sami gurbin karatu a Zaria, duk da yakan yi kokarin zuwa wani lokacin duk karshen wata, idan karatu yayi tsanani kuma sai yakai wata uku ma bata saka shi a idanuwanta ba.

Tana nan zaune, sai da Layla ta gama wankin tukunna ta dawo ta zauna tana daukar abincin

"Har abincina yayi sanyi"

Ta furta cikin yanayin mitarta

"Ki dumama"

Cewar Mami, kai kawai ta girgiza

"Nifa bama na son wanki, Mami kinsan bana son wanki, shine Hamma yake sakani"

Murmushi kawai Mami tayi, indan Layla ce ba gajiya takeyi da mita ba musamman akan Rayyan. Haka ta gama cin abincin tana mitar ta tashi ta wuce kitchen, kwanonin ba yawa garesu ba, ta daifi so ta wanke, sam batason aiki a kanta. Duk da akwai miya da yawa, Mami tace ko taliya sai a kara dafawa, gara tayi wanke-wanken saita fi jin dadin zama tayi kallonta a nutse. 

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:06 PM - 111: Nov 11, 2020

06

"Abbu...Sannu da zuwa"

Huda da take zaune a cikin falon ta fadi cike da farin cikin ganin shi, idan kaga yanayin autar ta Ayya zaka rantse tayi satika bata ga Abbun ba, a maimakon kwanaki hudu

"Huda"

Cewar Ahmadi yana dorawa da

"Ke kadai? Duk ina kowa? Ina Ayyar ku?"

Da murmushi a fuskar Huda har lokacin tace

"Kowa yana daki, Ayya tana sallar isha'i"

Numfashi Ahmadi ya sauke, a gajiye yake jin shi, ko dan tun da suka isa Abuja bawai sun zauna waje daya bane ba, hidimar da ta kaisu kawai sukeyi

"Ma shaa Allah, Ke kinyi sallar dai ko?"

Kai ta jinjina mishi

"Tun dazun ma... Hamma Bilal ne daya shigo sai yace inje inyi"

Wannan karin Ahmadi ne yayi murmushi

"Madallah da Hamma Bilal...bari inzo kafin ta idar"
Chapter 14 · 0% Book details