← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 93

Sashe 41

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ta shiga aji biyu sakandire ta zaunar da ita tana kara jaddada mata yanda babu halaccin wannan rirrike rirriken a tsakaninta da duka mazan gidan. Har misali tayi mata da su Rukayya, da yanda ko su basa rike hannun Rayyan. Sosai ta tsawatar mata saboda ta ganta da ta Rayyan din yazo nemanta ta rike mishi hannu. Ta dauka tun a lokacin ta bari, tunda a gabanta Rayyan din ya fisge hannun shi har duka ya kai mata, sai Mamin taji sanyi. Idan ita Layla bata da hankali Rayyan yana da shi.

Amman ko da Layla tana tunanin Rayyan din Yayanta ne, wannan rikon da tayi mishi ya wuce na yan uwantaka, idan ba idanuwanta bane suka gane mata kamar sumba Layla take shirin mannawa Rayyan din

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Mami ta fadi tana nufar Layla da ta raba jikinta daga na Rayyan da bayanannen tsoro a cikin idanuwanta

"Ma.. Mami"

Ta furta muryarta na fitowa a sarke, Mami na karasawa wani mari ta dauke Layla da shi tana kai mata dukan da Rayyan yaji har tsakiyar zuciyar shi. Lokaci daya kan shi ya sara yana daukar ciwo, bai dai motsa daga inda yake ba, idanuwan shi na kafe kan wayar da hankalin shi baya kai.

"Ashe baki da hankali? Ashe baku da hankali"

Cewar Mami da wani irin firgici marar misaltuwa, tana kara kaiwa Layla da take zubar da hawaye duka tana damko hannunta, Rayyan da yake tsaye Mami take kallo

"Idan ita bata da hankali kai baka da shi? Baka san haramcin da yake cikin abinda kuke aikatawa ba ko? Wallahi da Abbun ku zan hada ku, ba zan iya ba, ba zaku ja mana magana ba"

Mami ta karasa tana fisgar Layla zuwa bangaren Abbu, sai tirjewa takeyi saboda tsoron da yake cike da zuciyarta. Rayyan ba zaice ga abinda yake ji ba, amman jikin shi har bari yake daya kare Layla daga dukan Mami din, sosai zuciyar shi take jin ciwon dukan da tayi mata. Baice abinda tagani me kyau bane ba, har Bilal ya fada mishi ya daina baiji ba, ba laifin Layla bane ba, shine daya barta. Yaso ya bude baki yau ya gayawa Mami haka, amman baisan ta inda zai fara ba, shisa yayi shiru. Ya kasa barin wajen, yana nan tsaye har lokacin yaga Abbu yayo wajen, Mami na biye da shi, sai Layla da take biye da Mami din tana kukan da yake shigar mishi rai.

Yau yasan bayason hannun kowa ya taba jikin Laylar, bayason kowa ya zama dalilin kukanta idan bashi ba. Ita yake kallo har suka karaso wajen da Abbu yana kiran

"Rayyan?"

Saboda shima zuciyar shi bugawa takeyi, ya zauna kenan Mami ta shiga rike da Layla tana fadin

"Dan Allah kayi musu magana ko zasu jika, kayi musu magana kafin mu suja mana magana..."

Yanayin muryarta da yake cike da tsoro da karaya yasa Abbu tambayar

'Su wa? Lafiya? Me yake faruwa ne Maryama? Layla me ya faru?"

Ya karasa maganar yana mikewa, Layla da take kuka Abbu take kallo

"Dan Allah Abbu kayi hakuri, ba zan kara ba, ba zamu kara ba"

Saboda yaune karo na farko da tsoro matsananci ya cika mata zuciya haka. Kaunar da takewa Abbu mai girma ce, bataso yayi fushi da ita

"Wai me ya faru?"

Abbu ya sake tambaya dan duk zuciyar shi dokawa takeyi, Mami dakyar ta iya fadin

"Rungume na gansu ita da Rayyan"

Maganganun na fito mata da wani irin nauyi na tashin hankali. Wani sarawa Abbu yaji kan shi yayi kafin maganganun Mami su zauna mishi, ma'anar su da tashin hankalin su ya zauna mishi yana wujijjiga duk wani zaman lafiya da yake tare da shi. Marainiya, amanar da suka dauka shi da Mami, ai baisan kafafuwan shi sun taka ba sai da yaji shi a waje, kan shi tsaye bangaren su Rayyan din ya nufa yana kuwa hango shi a tsaye, suna karasawa hannun shi Abbu ya daga yana saka Rayyan lumshe idanuwan shi, saboda a karo na farko yau yayi tunanin hannun Abbu zai sauka a jikin shi. Bai bude idanuwan ba sai da yaji ya kama hannun shi.

Lokacin da Ayya ta zo wajen, saboda Huda taje ta fada mata ga Mami can tana dukan Layla yanzun ta gansu wajen dakin Rayyan din, kuma ta ga Rayyan a tsaye a wajen. Shisa Ayya ta taso ta fito a bazame, ganin Abbu rike da hannun Rayyan ya sata fadin

"Lafiya? Me ya faru?"

Tana sauke idanuwan ta akan Mami da Layla da ta kara boyewa bayan Mami tana tsiyayar hawaye saboda kallon da Ayya ta watsa mata

"Me ya faru wai?"

Mami ce ta kalli Ayya tana amsawa da

"Me yasa ba zaki tambayi dan ki ba?"

A fadace Ayya ta kalleta

"Da yai uwar me zan tambaye shi? Maryama kinga ki kiyayeni..."

Sun kwana biyu basu shiga harkar juna ba, tunda Mami ba biye mata takeyi ba, amman yau ranta a bace yake matuqa, abinda duk Ayya taje ji itama tana dai-dai da ita

"Idan ban kiyayeki ba me zai faru? Maimuna ki fadamun abinda zai faru yau idan ban kiyayeki ba, kuma wallahi kija ma danki kunne, ya kyalemun yarinya, domin amana ce a wajena"

Da tashin hankali Ayya take kallon Mami jin maganganun ta, ta bude baki Abbu ya kalli su biyun

"Maryama ki wuce ki koma ciki"

Akwai wani yanayi a muryar shi da yasa Mami juyawa, Layla zata bi bayanta Abbu yace

"Ke ki tsaya..."

Sosai Ayya ta kalli Abbu

"Ahmadi ban..."

Wani irin kallo yai mata

"Kema ki wuce Maimuna"

Bata taba ganin shi a yanayin da take ganin shi ba yanzun shisa ta kama hanya tana wucewa cike da son sanin abinda ya faru. Sai da tabar wajen sannan Abbu ya kalli Layla da take ta tsiyayar da hawaye

"Kar in sake ji, kar kuma in sake gani..."

Saboda yana ganin dana sanin da yake shimfide a fuskarta, ga kuma tsoro, ko da nasiha ko fada zai mata babu wanda zata fahimta a halin da take ciki. Kai kawai take daga mishi tana share hawayenta da bayan hannun, ganin yaja Rayyan zasu wuce ya sata fadin

"Dan Allah Abbu karka dake shi, baiyi komai ba shi"

Numfashi Abbu ya fitar da kalaman ta yana girgiza kai kawai saboda baisan inda zai dauke su ya ajiye ba, dakin su Rayyan din yaja shi saboda gani yake kafin su koma bangaren shi kalaman da yake ta hadawa sun bace mishi, gefen gado yaja Rayyan da bai musa ba ya zauna. Tsugunnawar da yaga Abbu yayi yasa ka shi jin wani irin abu ya tsirga mishi cikin kai. Ga wajen da Abbu ya rike mishi hannu kamar an kona shi yake ji, radadi wajen yake mishi ba fitar hankali.

"Rayyan..."

Abbu ya kira zuciyar shi na wani irin ciwo, yau so yake yaji matsalar yaron na shi, amman yaki yarda su hada ido, gabaki daya iskar dakin tayiwa Rayyan kadan

"Rayyan dan Allah yau ka kalli idanuwa ka fadamun matsalar ka, ina so in sani. Idan da yanda zan taimaka maka zanyi, wallahi zanyi komai in taimaka maka, amman hakan ba zai yiwu ba sai ka mun magana"

Kan shi Rayyan ya kara sunkuyar wa kasa, kirjin shi kamar zai kama da wuta saboda iskar da bata kai mishi inda ya kamata. Baison magana da Abbu, bayason ganin shi, bayason jin muryar shi duk da yasan yana cikin jerin mutanen da ya kamata ace yana jin kusanci da su, ya kamata ace yana so

"Kayi mun magana"

Abbu ya sake fadi, ya kai mintina kusan goma a tsugunne yana so ko idanuwan Rayyan din ne ya saka cikin nashi amman hakan ya gagara. Numfashi Abbu ya sauke kirjin shi na mishi zafi

"Idan son ta kakeyi ka fadamun, itama zan tambayeta sai in muku aure..."

Sai lokacin Rayyan din ya dago yana saka idanuwan shi cikin na Abbu

"Kana son ta?"

Baisan dalilin shi na girgizawa Abbu kai ba, shi bai san me yasa kowa yake tsallen yanke mishi hukunci haka ba akan Layla. Baisan me yasa ba zasu barshi ya dora sunan akan alakar da take a tsakanin su ba, amman yanzun da Abbu ya tambaya sai yake ganin kamar a cikin idanuwan shi yana so amsar ta kasance eh, dalilin da yaji ya dauki Layla ya jefa can wani waje a bayan zuciyar shi, yanayin da baisan ya zai tsaida faruwar shi ba. Numfashi Abbu ya sake saukewa

"Amana ce ita din a wajena, rokon ka nakeyi ka rufa mun asiri, idan baka tayani kare martabar ta ba, karka taba ta, dan Allah Rayyan a karo na farko kayi abinda nace, badan ina so ba, sai dan shine dai-dai"

Shiru Rayyan yayi yana kara sadda kan shi kasa, dakyar Abbu ya iya mikewa, har jiri yakeji yana daukar shi sanda ya kai bakin kofa saboda kan shi da yake sarawa, har lokacin jin shi yake kamar yana yawo a duniyar mafarki

"Abbu..."

Yaji Rayyan din ya kira, da babu taimakon kofar da Abbu ya dafa tabbas da kafafuwan shi sun kasa daukar shi, rabon da yaji sunan shi a bakin Rayyan tun yana dan karami. Na rana daya ya kira shi haka bai taba ba

"Yaa Rabb"

Abbu ya fadi a cikin zuciyar shi, yana jin ko addu'o'in shi akan Rayyan dinne suka fara karbuwa, juyawa yayi yana kallon Rayyan da yake yawata idanuwan shi akan fuskar Abbun, akwai tarin abubuwa da yake so ya fadama Abbu amman kamar an shaqe shi haka yake ji. Idan bai fadi sauran da baisan ta inda zai fara ba, yana so ya fada mishi yanda tunanin zai taba martabar Layla yayi mishi ciwo sosai, yana kuma so ya tambaye shi ko shima a tsakanin shi da na shi mahaifin yana jin irin wannan abin da yake ji.
Chapter 41 · 0% Book details