← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 93

Sashe 49

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya cewa Bappa da yayi dan murmushi yana girgiza mishi kai. Kunna sigarin yayi yana shanyeta cikin yan dakika ya sake kunna wata, sai da ya sha kara biyar, amman jikin shi bai daina kyarmar da yake yi ba. Karshen daya rage ya karasa bakin kofa inda ya hango kwandon shara ya zuba, harda kwalin daya tara toka a ciki. Dawowa yayi yana kara saka hannun shi cikin jakar shi ya laluba, kafin zuciyar shi tayi wata irin dokawa da bata da alaka da su Bilal, ya manta magungunan shi, jiya bai saka a jakar shi ba

"No.. No... Please no"

Yake fadi cikin tashin hankali yana kara dubawa ko watakila bai manta din ba, amman babu su, har kayan ya fito da su yana duddubawa, kafin ya sake mayarwa yana runtsa idanuwan shi, ji yake kamar wani abune a cikin kan shi yau da yake jiran cikar lokaci kafin ya tarwatse. Juyawa yayi ya nufi kan gadon, bai karasa ba yaji muryar Bappa da shaf ya manta yana dakin ta daki kunnuwan shi

"Ka ci abinci sai ka kwanta"

Kai Rayyan yake girgiza mishi yana zama a gefen gadon saboda yanda jikin shi yake bari, sosai yanzun yake bukatar magungunan shi, badan bacci ba, sai dan mugun sabon da jikin shi yayi, jiya bai sha ba in zai tuna, yini biyu kenan bai sha ba, shisa jikin shi yake sanar da shi babu lafiya.

"Kana bukatar ka sa wani abu a cikin ka"

Cewar Bappa da ya bude ledar take away din da yayo musu a cikin hotel din, shinkafa ce dafaduka ta sha nama da kayan hadi, harda hadin salad a gefe. Yana kallon Rayyan din ya sake girgiza mishi kai

"Yunwa da withdrawal effect ba hadi bane me kyau"

Bappa ya karasa maganar yana saukowa kasa kan kafet din dakin ya ja abincin shi daya saka cokali a ciki ya fara ci. Shi din ya karanci Psychology ne a kasar amurka, zai koma yaci gaba, saboda yana son zama abinda ake kira Profiler, akwai graduate degree da zaiyi akan forensic psychology kafin ya fara aiki da hukumar tsaro ta yan sanda da yake a can kasar, yana da kokarin da yasan da wahala idan bai samu ba.

Shi din dan gidan Sheikh Abdullah Bappa ne, sunan kakan shi yaci wato Muhammad sai suke kiran shi da Bappa kamar yanda ake kiran kakan na shi, baban shi sanannen Malami ne, duk kuwa da tarin arziqin da suke da shi. Suna da dattako, ana kuma ganin girman su a garin Kano, da wahala ka kira sunan Baban shi ace an samu mutane biyar a waje babu wanda ya san shi ko yaji labarin shi. Tun da ya dauko Rayyan yaga alamun damuwa a tare da shi, karantar shi yake tayi har zuwa yanzun.

Yanayin dabi'un shi, yanda jikin shi yake kyarma da idanuwan shi da sukayi wani irin haske duk kuwa da doguwar hanyar daya sha yasa Bappa gane cewa yana ta'ammali da miyagun kwayoyi. Watakila shima Rayyan kamar sauran mutane ne masu fama da depression, daga shan magungunan da zasu taimaka sai su dinga kara daya akan ka'idar da likita ya rubuta, a hankali a haka sai abin ya zame maka shaye-shaye batare da ka kula ba. Ka kara wa kanka matsala da kanka. Rayyan kuwa shiru yayi yana tauna maganganun da Bappa yayi kafin ya kwanta yana juyawa, Bappa bai san shi ba, dan ya gane daya daga cikin matsalar shi baya nufin ya gane gabaki daya.

Amman jikin shi kyarma yake, makoshin shi yakeji kamar an zuba yashi saboda bushewar da yayi, harshen shi babu miyau ko daya a ciki. Numfashi Bappa ya sauke yana mikewa, Rayyan baiga me yakeyi ba saboda ya rufe idanuwan shi har sai da ya karaso in da yake kwance yana fadin

"Ungo"

Bude idanuwa yayi, yaga robar ruwa sai irin maganin shi guda biyu a dayan hannun Bappa, jikin shi na kara sabon bari ya mike yana karbar maganin ya watsa a cikin bakin shi hadi da lumshe idanuwan shi, kafin ya sake bude su yana karbar robar ruwan ya kora

"Ka kara mun guda biyu"

Kai Bappa ya girgiza mishi

"Zai rikeka zuwa safe"

Ya fadi yana wucewa ya koma inda ya tashi, abincin shi yaci gaba daci, Rayyan kuwa ya kai mintina talatin kafin maganin ya fara nutsar da shi, rawar jikin da yake ya bari, ya sake gwada kiran su Bilal amman shiru. Wannan karin Bappa da yake kwance akan kujerar cikin dakin yana danna waya ya kalla, a saman damuwar shi tunanin waye Bappa ya darsar mishi, haka kawai ya tsinci kan shi da son sanin waye Bappa?

*

Sama-sama yake jin shi, iskar da yake shaka da fitarwa ma kamar an daureta da zaruruwa haka take shiga kofofin hancin shi. Jin shi yake kamar a cikin wani mugun mafarki da zai farka daga shi ko yaushe. Sai dai kamar ya farka kusan awa daya da ta wuce ko fiye da haka, babu agogo a hannun shi balle ya duba lokaci, ba shi da natsuwar kiyastawa kuma. Amman tabbas ya farka daga abinda ya tabbata ba mafarki bane ba, dumin jikinta ya fara tabbatar mishi da ba mafarki yake ba, kafin ya kara ware idanuwan shi akan fuskarta, wani irin mikewa yayi yana hankadeta gefe tare da fadin

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

A matuqar razane, kan shi ya kalla da yanayinta itama kafin komai ya dawo mishi, ba Aisha bace ba, Layla ce, Layla ce. Wata murya a cikin kan shi take fadi tana maimaitawa. A matuqar gigice ya suturta kan shi, baisan abinda ya kamata yayi ba banda kokarin ganin ta tashi, dabarar ya shafa mata ruwa bata zo mishi ba, haka yaci gaba da jijjigata a gigice har Allah ya dawo mata da hankalinta ta bude idanuwanta akan shi

"Layla ki tashi, dan Allah ki tashi ki karyata mun abin nan, ki ce mun karya ne, ki ce mun ko a mummunan mafarki ba zai faru ba..."

Bilal din yake fadi a gigice, yana girgiza ta, sai da ta kama hannun shi ta ture, jinta take kamar tana yawo a saman gajimare, dakyar taja jikinta tana mikewa, numfashi dakyar take fitarwa lokacin da ta kama skirt dinta tana saukewa, idan tace ga abinda take ji karyane, a fadin duniya babu wasu kalamai a cikin kowanne yare da zasu taba yiwa halin da take cikin adalci wajen fassara shi. Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon, tana mikewa taji wani irin abu ya tsirga mata, amman bata da lokacin ririta kowanne ciwone yake taso mata, dakin kawai take son bari

"Layla..."

Bilal ya kira, amman bata kula shi ba, dankwalinta ta dauka tana daurawa. Ta dauki jakarta da mayafi

"Layla..."

Ya sake kira ganin tana shirin nufar kofa a halin da take ciki. Shirun tashin hankalinta yake karanta da yake kara bugun zuciyar shi. Bashi da karfin motsawa balle ya hanata ficewa daga dakin. Tun fitarta bai motsa daga inda yake ba, sai yanzun daya samu yaja jikin shi yana dora kan shi a jikin katifar, idanuwan shi ya lumshe kamar hakan komai daya faru yake jira ya dawo mishi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ya furta daga wani lungu na zuciyar shi jikin shi na wani irin bari

"Me zan cewa Abbu? Me zan cewa Abbu..."

Yake fadi kamar wanda ya sami tabin hankali, har lokacin so yake ya tuna lokacin da Layla ta shigo dakin, so yake ya tuna yanda akayi ta hau kan gadon shi, yanda akayi wannan kaddarar ta same su, ko tabin hankali ya fara bai sani ba, tunda ance in kana hauka baka sanin abinda yake faruwa. Saboda in ba hauka yake ba babu yanda za ayi ace wani abu ya faru a tsakanin shi da wata mace daban da igiyar aure bata kulla su ba, balle kuma Layla. Yana da yakinin ko mazinaci ne shi ba zai bi Layla ba, yana mata son da ba zai yarda su kasance a irin wannan yanayin ba.

Hannun shi daya dora kan katifa yaji kamar ya taba wata lema-lema, ba shiri ya dago kan shi yana kallon wajen da hannun shi, abinda yagani na kara gudun zuciyar shi, baisan yanda ciwon bugun zuciya yake ba, amman tabbas yana gab da kama shi, saboda abinda yake gani na kara tabbatar da ko ciwon hauka yake, to tabbas a cikin wannan ciwon ya kasance tare da Layla. Wannan gaskiya ne ko da hankalin shi yabar jikin shi. Wata irin mikewa yayi yana kama zanin gadon ya yaye shi daga kai, fita yayi daga dakin kamar sabon mahaukaci.

Bokitin daya fara cin karo da shi ya saka zanin fadon a ciki ya koma daki ya dauko omo, ya nufi bokitin da sukan tara ruwa ya bude ya diba, kallo daya zakayi mishi da yanda yake wanke zanin gadon kasan ba a cikin hayyacin shi yake ba, yayi mishi wanki yafi biyar kafin ya shanya. Ruwan ya kara diba ya shiga wanka, sai dai ya kai awa daya tsaye a cikin bandakin ko kayan shi bai cire ba, kalar wankan da zaiyi yake tunani, idan ya saka sabulu ya fito tabbas zai fito da daudar da yake ji har cikin ruhin shi.

Idan kuma yayi wankan da zai tsarkake daudar wajen shi baisan yanda zaiyi da ta ciki ba, kuma wankan zai tabbatar mishi da abinda yake so ko yayane tunanin shi ya karyata mishi. Bashi da wani zabi daya wuce yin wankan tsarki ya daura alwala ya fito zuwa daki, kaya ya sake yana fita da wanda ya cire kamar suna tare da wata dauda da ta girmi idanuwa ya saka su a bokiti, dakin dai ya sake komawa ya dauki darduma ya shimfida, har ya kabbara sallar azahar da yake tunanin ta wuce shi, saboda sanda ya fita yaga kamar yamma tayi sosai, komai bai kwance mishi ba sai da yayi sujjada, sai da ya dora goshin shi a kasa ya kara jin yanda bashida wata hijabi tsakanin shi da Ubangiji sannan sauran nutsuwar da yake tare da ita ta kwance.

Maimakon karatun sujjada sai

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Chapter 49 · 0% Book details