← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 93

Sashe 27

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Laifina ne kenan?"

Kai ya daga mata. Dakyar sukayi sallama bayan ya mata alkawarin zai dawo gobe. Sai lokacin ya mika mata ledar da take hannun shi. Wasu takalma ne da yar ajinsu take siyarwa yayi mishi kyau, taki biyu ya sai mata kala daban-daban. Duk da batasan ko meye ba taji dadi har ranta, Bilal na da kyauta, lokutta da yawa inta juya cikin dakinta taga wani karamin abu da Bilal ya siya mata sai taji ya dan saukaka mata kewar shi. Anan masallacin unguwar su Aisha yayi sallar Magriba, sannan ya wuce gida.

*

Babu abinda Layla ta dauki gyaran da Mami take yawan yi mata kan kayan da take sakawa banda takura da rashin wayewa irin ta Mami. Ita ta kasa gane yanda duniya take tafiya da zamani yanzun sam. Lokutta da dama Mami na sakata jin daman ace ta fito a kasashen turawa ne, da yanzun ta kai shekarun da zata iya zabarwa kanta duk abinda take so, idan ma gidan zata bari tayi zaman kanta zata iya yin hakan.

Ko facebook data bude, yawancin shafukan da take bi na fina-finan kasashen waje ne, sai kuma na jaruman su. Musamman ma su Kim Kardashian, sai kuma mawaka irin su Rihanna, Drake, Chris Brown da sauran su, dan tafi son wakokin wrap. Takan ji wakokin kasashen sudan, yanayin al'adarsu na burgeta matuka. Lokutta da dama ita kadai a daki tana amfani da mp3 dinta tun kafin tayi waya ta saka earpiece tana gwada kalar raye-rayen da takan gani a fina-finai. Sosai zakayi zaton ta koyi rawa idan kaga yanda take karya gabobin jikinta.

Yanzun kuwa da tayi waya abin ba kama hannun yaro, videos ne da ita kaca-kaca, a jikinta take jin da ace tazo a kasar jamus ko amurka babu abinda zai hanata zuwa makarantar koyon rawa. Ana zuwa gasar da takan gani a fina-finai. Sosai abin yake mata kyau idan ta hasaso, musamman idan ta cire fuskar jaruman ta dora musu ta Rayyan. Wani lokaci abin na bata dariya matuka

"Hamma da rawa"

Takan fadi ita kadai, sai dai ko baiyi ba ita a kanta rawar tayi mishi kyau, musamman ace ita da shi a tare

"Perfect..."

Layla take tsintar kanta da fadi idan ta hango ta da Rayyan din, tun kafin ta gane ma'anar soyayya take kallonta a fina-finai, shisa sam bata sha wahalar gane me take ji akan Rayyan din ba, tunma kafin tasan da gaske son shi takeyi. Duk da wani lokaci yana fita daga ranta na yan dakika, wasu ranakun harna yini daya

"Mayya..."

Kalmar na bakanta mata rai sosai, kuma da gaske ne, akan shi ita din mayyar ce, kome zai mata zuciyarta har tsalle takeyi idan tagan shi, kuma bata fasa daga waya ta kira shi sai dai idan bata da kati. Ko da ace shi da Bilal basa ABU ita kam batajin zata zauna karatu a garin Kano, saboda babu yanda za'ayi abarta ta zauna hostel idan dai a BUK ko Polytechnic take. Shisa bata fadawa kowa ba sanda zata yanki jamb, zabinta na farko ABU din ta saka, tana son samun abinda ake kira "full high institution experience" a turance.

Batason sa idon Mami, rayuwar jami'a take son barjewa yanda ya kamata. Ta kuma yi sa'ar samun 181 a jamb din, ta tsallake dakyar. Tasan me take so, fannin turanci ne ta zaba saboda tana son samu aiki da wata babbar jarida ko gidan radio. BBC ne harinta, ko ba komai watakila tana da rabon zuwa kasar waje. Shisa ta gama tsara yanda komai zai fito, bata shiga tashin hankali ba sai lokacin da aka fara saida fam din jarabawar tace daliban da zasu sami gurbin karatu. Saboda gefe Mami ta koma tana fadin

"Duk makarantun da suke garin Kano? Sai kinje Zaria? Zubaida data gama karatunta kinga tabar gari. Khalifa kan shi cikin garin nan yayi nashi karatun, babu inda zakije, gara ma kiyi magana da Abbunku a sama miki gurbin karatu ko a legal ne idan BUK din ba zata samu ba"

Kuka tayi ranar kamar idanuwanta zasu tsiyaye, dan kiri kiri taga Mami na neman ruguza mata tarin burin da take da shi, a tsayin zamanta da Mami bata taba jin maraici ba sai ranar, watakila inda iyayenta suna raye zasu taimaka mata wajen ganin ta cika burinta ba suyi kokarin zame mata katanga a tsakaninta da abinda take son zama ba. Da Abbu yasa aka kirata ma kuka ta fashe mishi da shi

"Abbu dan ina mace bazan iya tafiya wani waje karatu ba? Dan ina mace bani da 'yan cin zabi? Me yasa Mami ba take son hanani? Karatu ne fa ba wani abu marar kyau ba. Ita ya kamata ta karfafa mun gwiwa in cika burina"

Ta karasa tana wani irin kuka, sosai yake kula da duka yaran. A duk gidan kuma daga Layla sai Jabir ne sukayi wata irin wayewa, rayuwar turawa ita suka saka a gabansu, garama Layla ba sosai takan nuna ba, amman Jabir sai da ya tabbatar har turancin shi ya gyara shi yanda idan yana magana zaka rantse da Allah ba'a kasar najeriya yayi karatu ba, to Layla ma yaji haka take lankwasa harshe

"Jabir turai"

Shine tsokanar da yakan yiwa dan nashi idan yaji yana magana wani lokacin, ko Layla yakan tsokaneta

"Ke da Jabir sai kun tauna harshen ku wata rana"

Kuma da gaskiyar shi, Jabir shine ya fara sakata son gyara turancin ta, haka suke zama kullum tsayin shekara uku suna wannan wahalar, Mami idan tagan su takan ce

"Ikon Allah, lallai sa kai wanda yafi bauta ciwo, da Qur'ani ne kukewa wannan nacin, ba'a kasar Kano ba, har zagayen Najeriya sai an san da zaman ku"

Dariya kawai sukanyi dan a ganin su ita ba zata taba ganewa ba. Ko Jabir din "Languages" yake karanta a BUK, kuma yanzun da yake shekara ta biyu, a tarihin department din ba'a taba samun dalibi mai kokarin shi ba. Abbu ma kance

"Da alama Jabir zaka samu gwamnati ta dauki dawainiyar karatun ka zuwa kasar waje in har kaci gaba da tafiya a haka"

Itama Layla wannan burin take da shi, amman Mami na neman hanata. Shiru Abbu yayi dan baisan me ya kamata yace ma Layla din ba. Har ran shi yana son su da karatu, a matsayinta na 'ya mace musulunci yayi mata wata daraja mai girma, suma kuma ya basu 'yancin kareta da dukkan karfin su. Ya fahimci Mami tunda sunyi zancen tun kafin yasa ta turo mishi Layla

"Kana kallon yanda nake fama da Layla kan wannan rayuwar turawan data dorawa kanta... Ina ga ta bar inda babu idanuwan kowa?"

Mami din ta fadi muryarta na karyewa, har ranta tana tsoron barin Layla Kano. Karatu duk inda kake zakayi. Shima kuma ya aminta da abinda tace din, amman yanda Layla take kuka a gabanshi ya karyar mishi da zuciya

"Abbu idan kaima ka hana zaku sakani yin wani tunani daban"

Layla ta furta tana tashi tabar shi anan zaune. Ya jima shiru, maganganunta sun jefa shi wani tunani daban, harga Allah yafi basu kulawa ita da Bilal sai Haris da yanayin shine son kulawar. Amman ita da Bilal na minti daya bayason suji rashin iyayen su, yasan zafin maraici duk da yayi wayon sanin nashi iyayen, su da basuyi wannan wayan ba baisan abinda sukeji ba, yana kokarin ganin basuji komai ba. Bayason Layla taji kamar dan bata fito daga jikinsu bane suke son zama katanga tsakaninta da burinta.

Yana ganin tayi yarinta ta fahimci cewa basa nufin komai a kanta sai alkhairi, komai da zasuyi dan su kareta ne badan komai ba. Abin ya dame shi, kwana yayi yana juyi, washegari kam yana tashi daga aiki saida ya biya wajen abokin shi Nasiru dan ya nemi shawarar shi, bai boye mishi komai ba

"Ina tsoron tafiyar ta karatu wani gari, har raina ina tsoron hakan saboda ita macece"

Murmushi Nasiru yayi

"Kai kasan indan tani ne yara mata ba zasu wuce matakin sakandire ba, Allah yasan Nabila tayi karatune saboda miji bai fito ba sanda ta gama, Zainabu fa? Ita da kanta ta zabi auren da miji ya fito, sakandiren ma bata samu gamawa ba"

Kai Abbu ya jinjina mishi, duka shine shaida, yanda Nasiru yasan sirrikan shi, haka shima, suna neman shawarar juna a dukkan lamurran su

"Meye muke gudu Ahmadi? Lalacewar yaran ce abin gudu, gani muke idan suna gaban idanuwan mu zamu fi kare su yanda ya kamata. Ni ma tunanin da nakeyi kenan yasa nake son nisanta matan da zurfin karatun boko...sai dai rayuwa ta koyamun ba dabarar mu a tarbiyar yara... Ka duba Bashari, a gaban idona tarbiyar tashi take ta tabarbarewa, duka, zagi babu wanda bamuyi ba, yanzun ba addu'a muka koma ba? Shine aka fara samun dan cigaba"

Numfashi Abbu ya sauke

"Hakane, kana ganin in barta ta tafi?"

Kai Nasiru ya girgiza mishi

"Ba ina cewa kabarta ta tafi bane kai tsaye, ina fada maka karka labe a bayan gudun lalacewar tarbiyya wajen hanata zuwan. A gaban idanuwanka abinda kake gudu zai iya faruwa, kai dai kayi iya yinka wajen tarbiyar, ka kuma roki Allah ya kare abinda idanuwanka ba zasu gani ba..."

Maganganun Nasirun sun kara daure mishi kai, duk yanda yaso ya furta da bakin shi cewa yabar Layla ta tafi Zaria yaki, shawarar shi duka akwai kofar zabi daya barma Ahmadin. Haka Yaya Ayuba da ya same shi da zancen

"Ba gari ba, kaga Nadiya Madina tayo karatunta, duk kuwa da tarin surutun da akai tayi a kai. Gata ta kammala ta dawo lafiya tana dakin mijinta. Kamar yanda kace Nasiru ya fada maka ne, tarbiya iya yinka zakayi, sauran da yafi karfin ka ka hada da addu'a. Karka barta ta tafi sai kana da yakinin duka zuciyarka ta amince maka da tafiyar, idan baka aminta ba hakurin zaifi zama alkhairi. Idan bata fahimce ka ba yau, wata rana zata fahimce ka"

Akan shawarwarin nasu yaita tunani har kwana biyu kafin ya natsu da barin Layla ta tafi, ranar har tsakar dare ya tashi yayi sallah yana rokon Allah daya kare mishi yaran shi, ya rabasu da abokai gurbatattu. Dakyar ya shawo kan Mami

"Shikenan, Allah yasa hakan ya zama alkhairi"
Chapter 27 · 0% Book details