Sashe 80
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rayyan yake fadi zuciyar shi na cigaba da dokawa. Bappa bai ce mishi komai ba, baiyi magana ba, haka har suka isa garin Kaduna Rayyan na duba wayar kamar yana tsammamin Bilal zai iya fitowa daga cikinta, lokaci zuwa lokaci yakan juya yace ma Bappa
"Bilal ya cire kudi"
Ko kuma
"Kasan shine yake cire kudi haka kadan-kadan har fada muke saboda ina ganin wahalar da yakeyi, sai yace mun idan ya ciro da yawa zai dinga siyan abubuwan rashin dalili"
Haka yaita surutai, Bappa bai dai tanka mishi ba har sai da suka shiga cikin gidan su suka zauna sannan yace
"Rayyan"
Kallon shi Rayyan yayi, yanayin da yake ji babu wani abu da zai misalta shi, a jikin shi ya dinga jin yanda Bilal bai bar shi ba, daman yasan Bilal ba zai barshi haka ba.
"Zai iya yiwuwa an tsinci ATM dinne, ka bude zuciyar ka da yiwuwar hakan"
Kai kawai Rayyan ya jinjina ma Bappa yana mika mishi wayar shi ya mike. Ban daki ya shiga da nufin watsa ruwa. Yaga kudin da ya rage account din Bilal din dubu takwas ne, shikam akwai kudi da yawa a account din shi, ga na bautar kasa da aka basu, ga wanda Abbu bai daina tura mishi ba, sannan inda suke bautar kasar ma suna biyan su albashi me kyau. Da murmushi a fuskar shi yayi amfani da wayar shi da ya shiga bandaki da ita yana turama Bilal din kudi ta bankin shi.
"Na san ba zaka barni ba Bilal"
Ya furta yana shafa screen din yar karamar wayar ta shi, yana jin kamar Bilal din yana tare da shi, ba zai sake zancen nan da Bappa ba, ba zaiyi zancen da kowa ba kuma. Saboda ba zasu yarda ba, zai bar abin a ran shi, shi kadai har sai Bilal din ya dawo sun gan shi. Lumshe idanuwan shi Rayyan yayi
"Kar tafiyar taka tayi tsayi, ka waiwaye mu da ka samu nutsuwar da kake bukata"
Ya furta a zuciyar shi, kafin ya bude idanuwan shi, da tunani kala-kala a cikin kan shi, hannun shi yakai kirjin shi yanajin kamar an fifita mishi ciwukan da suke ciki, saboda komai yayi wani irin shiru, ciwon da yake ji kamar anyi ruwan shi an dauke.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 12, 2020.
30
Dan ware idanuwa Bappa yayi, yana sake kallon farantin da yake gaban Rayyan a ajiye
"Meye wannan Rayyan?"
Ya bukata, Rayyan din na dan juya idanuwan shi, yasan sarai Bappa ya gane plantain ce, tunda suka kwaso ta da dankalin turawa, sau biyu yaga Bappa ya soya. Abin a ido kamar ba zai wahala ba, sai da yazo tun daga yankawar ya gane aikin ba karami bane ba, da yake man yayi zafi sosai sanda ya zuba kafin ya juya wata, wata ta kusan konewa, gabaki daya sunyi baki, har cikin makoshin shi yana jin daci-dacin da sukayi. Sai dai yunwa yake ji da yake ranar ta zo musu a karshen mako, Bappa din kuma ya fita, yana jin kwiyar zuwa ya siyo wani abu.
"Da me yayi maka kama?"
Rayyan ya amsa tambayar Bappa din da wata tambayar, yana sake saka cokali mai yatsu ya caki guda biyu ya saka a bakin shi yana taunawa kamar babu dacin da Bappa yasan zatayi, dariya Bappa yayi
"Ka tashi mu fita, nima ba abinda naci"
Kafada Rayyan ya makale, bayajin zuwa ko ina
"Me yasa bakayo mana take away ba? Dole sai ka dawo ka fitar da ni"
Tunanin ne bai zo ma Bappa ba sam, saboda yasan halin Rayyan din, bakomai na waje yake ci ba, idan suka fita tare saiya zaba da kan shi, ba'a cika yi mishi gwaninta ba.
"Ka tashi dan Allah, ba kana maganar waya ba? Sai mu biya ka duba"
Dan jim Rayyan din yayi, da gaske yana son siyan babbar waya. Saboda yanzun sukanyi kwanaki har biyu ko fiye da hakan ma tunda ya dawo basuyi waya da Layla ba. Sukan yi musayar text dai, ta cikin su yakan fahimci kamar yanzun tana rasa abinda zatace mishi, idan suka gaisa sai ya jima yana kallon wayar yana jiran yaga amsarta, sai yake tsintar kan shi da tunanin ko tana lafiya ko akasin hakan. Idan ya kira ma wasu lokuttan bata dagawa, ba ko yaushe take biyo kiran ba sai dai idan ya sake gajiya ya kara kiranta.
Yasan zai iya zuwa gida idan yana so, Bappa da wahala yayi kwana biyar bai shiga Kano ba, yawon shi har mamaki yake bama Rayyan din, gidane bayason zuwa, tunanin ya shiga dakinsu babu Bilal yana mishi wani iri. Duk da akwai damuwar da ta daga a kirjin shi baya nufin baya kewar Bilal din, ba kuma ya nufin tafiyar da Bilal yayi bata mishi ciwo, yana dannewa ne
"Zaiyi sauki, In shaa Allah komai zaiyi sauki"
Bappa kan yawaita fada mishi haka kawai idan yaga yayi shiru yana kallon bango. Baya amsawa, baya tunanin Bappa nayin maganar ne dan yana jiran ya amsa mishi. Kawai yanayine saboda yasa shi yaji kamar wani ya damu, kamar yana kula da yanayin shi. Kuma yanaji din, har cikin zuciyar shi yanajin kulawar Bappa da baiyi tunanin wani bayan Bilal da Layla zasu gwada mishi ita ba. Su Ayya iyayene, bayajin akwai zabi a tasu kulawar, kamar da haihuwar shi da yanda kula da shi ya zame musu tilas ko da basa son hakan, ko da ta takaitaccen lokaci ce.
Watakila Bilal na kula da shi saboda su din yan uwane, Layla kuma dan tana son shi. Kusan suma zaice basu da zabi, amman Bappa na da zabi, sai ya zabi kula da shi, ya zabi yi mishi karamci duk da shi din bashida wani abu da zai iya mayarwa Bappa da shi
"Zama da kai ba abu bane mai sauki Hamma"
Bilal ya taba fada mishi da sukayi wani rikici, kuma yasan gaskiya ya fada. Amman Bappa na zaune da shi kamar hakan abune mai sauki. Bappa ya bashi abinda bai taba tunanin zai samu ba a rayuwar shi, ya bashi abota. Satin su biyu da dawowa Kaduna aka koma makaranta, da yake akwai kanin Bappa a ABU din shisa ma Rayyan yasan an koma. Rana daya ya tambaya a wajen da suke serving aka kuma bashi, da yacewa Bappa zaije Zaria da mamaki ya kalle shi
"Me yasa yau? Ka bari sai weekend mana mu shiga tare"
Kai Rayyan ya girgiza mishi
"Akwai abinda zanyi yau din shisa"
Yana jin dadin da bakomai Bappa yake tsaurara tambaya a kai ba. Fatan alkhairi kawai yayi mishi dana Allah ya tsare hanya. Dan da yace ya kai shi tasha yace zai hau mashin. Abinda duk yake bukata yana cikin yar jakar shi daya goya a baya yana ficewa daga gidan zuwa ta sha. Saura mutum biyu motar ta cika sanda ya shiga, aikam yana zama ana kara samun wani, sosai yaga saurin saukar su, ko dan tunanin da yakeyi ne. Kan shi tsaye makaranta ya wuce, abinda bai taba tunanin zaiyi ba shi yayi, har Office din wasu cikin Malaman shi dan ya tambayi abinda yake bukata din.
Sun kuma karbeshi a mutunce haka amsar duk tarin tambayoyin da yayi. Kananun kayane a jikin shi, rigar mai dogon hannu, shigar da baka raba Bilal da ita. Bai taba tsintar kan shi a yanayin da yake ji ba yau, musamman da ya kasa tuna wanne kalar passport ne Bilal ya manna a jikin takardun su, ko kamannin su sun fito ko basu fito ba. Sauran semester daya Bilal ya kammala karatun shi, yana ji a jikin shi zai dawo, yana kuma fata da addu'ar dawowar ta zamana a kusa, ya iya kalar signature din Bilal, dan ya ko shi Bilal yakan yi mamaki
"Dan dai kana zane ne, shisa bai maka wahala ba"
Cewar Bilal wani lokaci can baya, bai sha wahalar tsayar ma da Bilal karatun ba, yayi amfani da uzurin rashin lafiya ne. Kusan rabin rana yana abu daya, dan akwai kudin da ake biya kafin a iya. Wajen uku saura ya samu ya kammala komai, saiya tsinci kan shi da samun wata natsuwa da baisan daga inda ta fito ba. Baisan kafafuwan shi na daukar shi zuwa gidan su ba sai da ya gan shi a kofar gida, akwai mukullin daki a jakar shi, dan haka bai sha wata wahala ba daya shiga, ya daiyi mamakin yanda jikin shi ya dinga bari wajen budewa.
Yaji dadi sosai da bai samu kowa daya sani ba harya shiga. Dakin zaka rantse anyi watanni ba'a shiga ba saboda kurar da yayi. Sai yaji zuciyar shi ta matse a kirjin shi, tsaye yayi a tsakar dakin yana ganin rayuwar da sukayi a cikin shi kamar an kunna film, yana ganin Bilal a ko ina na cikin daki, yana jin shi a ko ina na zuciyar shi da take wani irin ciwo da baiyi tsammani ba. Ba zaice ga lokacin daya dauka a tsaye a wajen ba, wayar shi da ta fara ihu a aljihun shi ce ta katse mishi tunanin da yayi zurfi a ciki, ko dubawa baiyi ba bayan ya dauka ya daga kiran, karawa yayi a kunnen shi
"Hello..."
Ya fadi muryar shi na fitowa daga can kasan makoshi
"Rayyan"
Yaji muryar Haris cikin kunnen shi da ta saka shi yin gyaran murya saboda yanayin da yake ji
"Hamma"
Ya iya fada, muryar shi na fitowa a shake
"Kana ina? Me ya faru?"
Haris ya tambaya cike da kulawa, yanzun da ya dawo kamar kowa yake jin yanda bai cancanci tarin kaunar da yan uwan shi sukeyi mishi ba, saboda sam bai tuna wani lokaci daya nuna musu ko da kadan a cikin kalar kaunar da sukeyi mishi ba. Amman yana tuna yanda duk ture sun da yayi bai hana su kokarin kusantar shi ba. Kaunar su daban take, kaunar su na da alaka da jinin shi da yake yawo a nasu.
"Rayyan kayi mun magana dan Allah"
Numfashi ya sauke
"Zaria, ina Zaria Hamma"
Haris ya dan jima kafin yace