← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 93

Sashe 2

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maimunar ma inda zaka tambayeta lokacin da ta fara qin Inna ba zata iya tunawa ba, kawai ta wayi garine da tsanar yanda take ganin Inna ta saka kalar kayan da Yayya ta saka, ko kuma Baba ya siyo abu ya baiwa Inna a tsakar gida gabansu. Har ranta takanji tuquqin bakin ciki, da Inna bata aurewa Yayya miji ba, sam ba zata zo tana daga kafadu ta saka kaya kala daya da Yayya ba. Takan tuna kalaman mahaifiyarta lokacin da take da rai

"Maimuna na rasa inda kika kwaso wannan kishin naki, wallahi na rasa. Allah ya rangwanta miki shi karya zame miki matsala"

A zuciyarta bayan amin takan raya

"Ni kadai zan zauna a gidan mijina, babu macen da zata zo ana siyo mana kaya iri daya da ita"

Tun kafin tasan dadin auren kenan, ballantana yanzun da takejin kaunar Ahmadi na ratsa duk wani sassa na jikinta. Lokacin hidimar auren su da yace mata

"Kinsan Ahmadin ki na mace biyu ne ko?"

Dariya tayi sosai, duk zancen da yai mata na zama da mata biyu raha ta dauke shi, a zatonta labarin kalar kishin da take dashi yaji shisa yake zolayarta. Sai ranar daya dauketa dan suje taga ginin shi da yayi nisa ne tashin hankalinta ya fara ganin kalar tsarin ginin, a gigice suka dawo gida. Inda tai wani irin zaman dabas a kasa tana sakin kururuwar da Ahmadi yaga ko lokacin da labarin mutuwar Yayya ta riske su batayi irinta ba tana fadin

"Tozartani zakayi? Ahmadi asirina zaka tona shisa kake tunanin hadani da wata? Ashe soyayyar da kake mun duk karyace? Kulawar nan taka duk yaudara ce?"

Sosai kalamanta suka girgiza shi dan ya dauka sanar matan da yayi tun kafin auren su zai rage kadan cikin kishin daya kula tana dashi a kan shi, dan ko yan uwanshi da suke ciki daya bataso suna rabar shi. Balle kuma ayi maganar wasu can daban. Ranar ya dauka ya gama ganin tashin hankalinta, kwanaki biyu sukai cur bata bari sun runtsa ba a gidan. Shikuma lokacin ya kyalla idanuwan shi kan Maryama harma Yayanta yasan yana ciki, manya sun sani, an dai boye zancen ne saboda ya fada musu bai gama shiri ba sai ginin shi ya kara nisa za'a tsayar da zancen auren sosai.

Da yake itama Maryama duk ahalin Dikkon ne, alakarsu tafi karfi da Maimuna akan shi, tunda Kakkanin Maimuna na wajen uwa da kuma na Maryama itama na wajen uwa abokan wasa ne na kusa, ba bare bace zai auro. Yanda Ahmadi ya dauka zancen sanin kowanne lokaci zai iya kara aure shine tashin hankali mafi girma da zasu shiga dashi da Maimuna, sai da aka tsayar da ranar auren shi. Sai da Maimuna tasan wa zai aura asalin tashin hankali ya fara.

Ranar inda Allah yasota daga Khalifa har Zubaida suna gidan Yaya Ayuba. Dan ko gida bata kulle ba, kuka take wiwi, da kafafuwanta ta isa gidansu Maryama inda ta shiga babu ko sallama sai ruwan tijarar da ta sauke musu

"Ashe kasa kuke jira ta rufe idanuwan Yayya kuci amanata, tunda kuke zuwa gidana badan zumunci bane da shirin ku aurawa yarku mijina ne...me yasa duk mazan dangi sai Ahmadi na? Me yasa zakuci amanata haka?"

Duk yanda suka so ta kwantar da hankalinta fur taqiya. Kuka take musu tana surutai harda zagin da batasan lokacin da taji shi kwakwalwarta ta nade mata su ba. Sai da kowa a gidansu Maryama yai tunanin ko Maimuna tana da iskokai da ba asan dasu ba. Duk da akance kowacce mace nada nata, dalilin bayyana ne wasu da yawa basu samu ba. Sai da aka kira Gwaggon Maimuna din Bare da take aure nan kasa dasu, tukunna ta samu ta fitar da Maimuna daga gidan tana janta zuwa nata gidan.

"Gwaggo auren cin amana zasuyi, Maryama fa suke neman aurawa Ahmadi na"

Lallashinta Gwaggo takeyi sosai kafin ta kara fada mata maganganun da suka sake firgitata

"Waye baisan Karime da shige-shige ba? Kaf dangi fa kowa yasan gidansu da bin bokaye. Kina ganin ita taki barin kishiya ta zauna a nata gidan. Biyu fa ta fitar, wallahi idan akace miki Ahmadin ma basu kyale shi haka ba ba'a musu. Babu wanda bai shaida kaunar da take tsakanin ku da Ahmadi ba..."

Ai sai Maimuna ta kara dora hannu a kai tana rushewa da wani sabon kukan, sai yanzun take gane menene firgici

"Na shiga uku ni jikar Hanne... Gwaggo karsu fitar ni daga gidana, karsu rabani da Ahmadi..."

Kara riketa Gwaggo tayi

"Ki share hawayenki, wacece Karime ballanta Maryama, ke kinsan in ba anbi ta karkashin kasa ba, mai Ahmadi zai da wata Maryama....yarinya duk ta gandame a gida ba mashinshini. Karki damu akwai Malamina dana aminta dashi, shine yaimun aikin wannan yarinyar da aka hada da baqar iska..."

Hannu Maimuna tasa tana share hawayenta, dan indai Malamin da Gwaggo take magana shiyai mata aiki ya raba babbar yarta da bakar iskar da aka tura mata har tayi aure, to aikin shi naci. Dan tunda suka tashi tasan duk sa'annin yar Gwaggon suna da yara wajen hurhudu a dakunan mazajen su, a tarihin ahalin Dikko matansu da wahalar gaske su cika shekaru sha biyar ba a dakin mazajan su ba, wasu ma tun suna shekara sha uku, lokacin da za'ayi shabiyar din da goyon yaro. Amman yar Gwaggo takai shekara ashirin da bakwai kafin tayi aure.

Bata bar gidan Gwaggo ba saida kwarin gwiwar Malamin Gwaggon zai mata maganin matsalar auren nan da Ahmadi yake so ya jajibo musu. Dan ko da ya dawo gidan ya rufeta da fadan da tunda suke duk tarin laifukan da takeyi bai taba mata irin shi ba akan zuwan da tayi gidan su Maryama hakuri ta bashi. A ranar kuwa ta kwana tayi juyi tana zubar da hawaye, tana kara tabbatar da asiri akayiwa Ahmadi, inda babu asiri shidin bazai taba daga mata murya akan wata mace ba.

Ba'a cika sati biyu ba Gwaggo tazo gidan ta kawo mata magunguna da rubutun da zata sha ta shafe jikinta, sai maganin kuma a barbada a abincin da Ahmadi zaici.

"Kinji asiri ne ko? Turaren ne ta goga tazo nan gidan dashi, har a kofar gida tayi miki barbade ya tsallaka"

Kada kai kawai Maimuna tayi, mutum ba abin yarda bane, shisa kawarta daya Khadi tun tasowar ta, saboda rashin yardar da take da ita. A shekarar da ta wuce Maimuna ba zata manta ba, wajen sau hudu Maryama na zuwa gidan da sunan zumunci, ashe duk karyace, mijinta take kokarin aurewa. Wasu cikin kudaden da Ahmadi kan bata da ba wani abu take siye ba dan shidin mai kyautatawa iyalin shine ta diba tabawa Gwaggo dan ance gaba harda na tsari za'a karo mata da wanda za'a turo aljanin da zai katange gidan ko da su Maryama zasu gwada wani asirin.

Ranar jikinta har bari yake da Ahmadi yakai lomar abinci, sai tashi tayi tabar mishi dakin tana wucewa bayi ta kulle, inda tai zaune tana garzar kuka, sai takejin kamar taci amanar zaman su, kamar bata kyautawa kaunar da Ahmadi yake nuna mata ba da ta barshi yake aikawa cikin shi abincin da yasha garin magunguna har kala biyu, ga lamurje da ta hada mishi da ruwan rubutu.

"Kaga abinda hange-gangen ka ya janyo mana ko Ahmadi?"

Ta furta tana wani irin kuka mai taba zuciya, sai takejin kamar ta tsallaka wani waje yau mai wahalar komawa baya. Sai dai me babu abinda ya canza, da duk rana da yanda maganar auren Ahmadi take kara kusantowa. Maganar tashin hankalin da Maimuna take ciki ba'a fadi. Ga laulayin ciki daya sakata a gaba lokacin, kalar kulawar da Ahmadi yake mata na kara hura wutar kishin shi, ko rufe ido tayi ta kwatanta raba kaunar shi da wata Maryama sai zuciyarta tayi kamar zata tarwatse. Sai yanzun take ganin gaskiyar Khadi, take ganin wautar da tayi wajen kokarin hanata shiga Malamai saboda rashin kyawun hakan a addinance.

Khadi itace ta ukku a wajen mijinta, shigarta sai da tayi nasarar fitar da ta biyun daga gidan. Bayan fitarta ne yai dai-dai da rabon cikin da Khadi din ta samu, dan ta fadawa Maimuna cewa Malamanta sunce mata kishiyarce ta qulle mata mahaifa. Da tana ganin kamar haihuwa nufin Allah ne, sai yanzun ta gasgata zancen Khadi, kishiya ba abinso bace ko da ta batumbatumi ce. Ranar da kanta ta sami dan aike har gidan Khadi tace inta sami dama ta leqota. Kwanaki biyu tsakani kuwa Khadi tazo gidan.

Kuka sosai Maimuna ta tusa mata

"Khadi ki taimakeni, Malaminkin nan da yayi miki aiki kije mun wajen shi ko zai taimaka mun akan Ahmadi, dan Allah Khadi, wallahi ya kara auren nan zuciyata bugawa zatayi"

Dariya Khadi tayi har tana saka Maimuna jin haushi

"Ai gara da kika farka, idanuwan ki suka bude... In anyi duniya da Manzo kin kawo kukan ki inda za'a share miki"

Wannan maganganun sun kara karfin amintakar da take tsakanin su. Kudade Maimuna ta baiwa Khadi masu yawan gaske, dan idanuwan ta sun rufe da zafin kishin da bata tunanin addu'ar neman sauki akan shi, ta saki Allah ta komawa yan tsubbun da ta aminta sune kadai maganin matsalar da take fama da ita yanzun. Sai dai wani sabon tashin hankalin ta shiga dan Malamin Khadi ya hango dole sai Maryama ta shigo gidan sannan zata iya nasara a kanta

"Da ayaba akayi mishi wannan mallakar, da ace baki ma farga da wuri ba da yanzun sun shiga tsakanin ki da Ahmadi, dole sai ta shigo gidan za'a san yanda za'a karya sihirin..."

Ya kuma tabbatar mata dole saita kara jajircewa daga ita har yaranta. Kullum cikin boye-boye magunguna take da take bankadawa ma cikinta da yara a matsayin karya tambaya da kuma kaikayi koma kan masheqiya. Wasu da inta jika Ahmadi yagani sai tace mishi maganin shawarane da Gwaggo ta hado mata, wani lokaci harya karba kanshi tsaye yasha shima, tunda ta gano wannan hanyar cewa bokon shi bata rabashi da magungunan gargajiya ba take bashi wasu kanta tsaye da sunan maganin Basir ko shawara ko sanyi.
Chapter 2 · 0% Book details