← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 93

Sashe 5

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmadi ya furta da murmushi a fuskar shi kafin Maimuna ta sami damar fada mishi, yanajin dadin kusancin da makotakar su da Yayan shi ta wanzar tsakanin yaran su. Shi kanshi ma yanzun ma sai sukai karfe tara a waje da Yaya Ayuban suna hirar su wasu lokuttan. Hakan ba karamin dadi yake mishi ba, a lokuttan da Maimuna ta hada mishi zafi sai yaji zuciyar shi ta sanyaya idan sunyi hira da Yayan. Duk da bayason rage mutuncinta a idanuwan dan uwan nashi, shisa ko da wasa bai taba gwada fadar laifinta ba ballantana ya nemi shawara.

Duk fadan da zasuyi, sukan shirya, kuma yana yafe mata ko da bata nemi hakan ba, son da yake mata mai girmane. Yana gudun kar ya fadama Yaya Ayuba wani laifin Maimuna din, shi yazo ya yafe mata, Yaya Ayuban na kallonta da abin, sam ba zaiji dadi ba. Kankanar ya raba gida uku, ya dauki kashi daya ya saka a ledar, yanda yake jin wata irin gajiya jar a kasusuwan jikin shi yau zaiso ace zai iya baiwa Maimuna kankanar dan ta mikawa Maryama. Amman mitarta zatayi karshe harda rashin kunyar da ta koyi yi mishi tace ba zata kai ba. Shisa ya mike da kan shi yana kuwa cin sa'a Maryaman ta fito rike da buta a hannunta, murmushin nan nata tayi mishi

"Maryama..."

Ya furta cike da jin dadin ganinta, yana mika mata kankanar da ta ajiye butar hannunta tana dan tsugunna ta saka hannuwa biyu ta karba cike da girmamawa

"Allah ya saka da alkhairi. Sannu da kokari"

Murmushin shi Ahmadi ya kara fadadawa

"Ya zazzabin? Yayi sauki ko?"

Ya tambaya kamar dawowar shi bai dubata ba, kulawar shi daban take.Kai ta daga mishi cike da jin nauyi, tunda taga har wannan watan bata ga al'adarta ba, ta tabbatar da zarginta na cewa ciki take dauke dashi, ba wani canji takeji a jikinta ba, banda yawan kwadayin abinci mai manja, sai zazzabi da takan kwana dashi wani lokacin, amman lafiya kalau take jinta, wasu amaye amaye ko tashin zuciya duk Allah bai daura mata ba. Tana taso ta fadama Ahmadi zargin da takeyi amman nauyin hakan takeji sosai, banda yau da kishi yasa tayi ma Maimuna burga da cikin, ita kadai tasan da abinta.

"Sai da safe, kisha maganin da na siyo indai kinji ya dawo, da safe sai mu fita a dubaki asibitin wajen aikin mu"

Kai ta iya jinjina mishi

"Allah ya hutar da gajiya"

Ta furta tana juyawa daki, labule kawai ta daga ta ajiye ledar kankanar ta dawo ta dauki buta, kasala takeji yau sosai, dan tun taliyarta data dafa da manja ce da tayi saura taci da daren nan. Kan kunnenta aka kira isha'i tana kwance tana juye-juye a daki sai yanzun Allah yai mata fitowa. Alwala ta daura ta koma daki abinta. Ahmadi ma dakin Maimuna ya koma, yana karbar Rayyan daya saka babban yatsan shi a baki yana ta tsotsa

"Gaka da alamomin hakuri amman sai rikici ko?"

Ahmadi yai maganar kamar yaron zai fahimci me yake cewa, Maimuna da ta sakko kasan itama ta dauki wuka tana karasa gyara kankanar daya yanka, ta dauka tana mika mishi, hannun shi ya duba saboda yayi gaishe-gaishe da mutane

"Ban wanko hannu ba"

Dan kara matsawa tayi tana fara zare kwallayen jikin kankanar ta mika saitin bakin shi daya bude ta saka mishi a ciki, taunawa yayi yana jinjina kai

"Wai... Daman yace mun me kyau ce wallahi, dana sani kwallo biyu na siyo..."

Kallon shi Maimuna takeyi

"Da zaki? Naga batai ja ba sosai"

Ta karasa tana sakawa a bakinta itama, sake gyara wata tayi tana kara ba Ahmadi

"Aikam da zaki..."

Cewar Maimuna, kafin Rayyan daya fara mutsilniya a jikin Ahmadi yana kwakkwabe fuska yasata furta

"Wallahi karka dagamun hankali, na rasa inda ka kwaso rigima"

Dariya Ahmadi yayi

"Me kake nufi?"

Ta furta tana kallon shi, kai yake girgiza mata yana kawo bakin shi ganin ta gyara kankanar da ke hannunta, a nata bakin ta lunkuma

"Ka wanko hannuwanka ka sha da kanka, so kake kace ni ya biyo da alama"

Dariya yake sosai, dariyar da ta kwana biyu bata gani ba, gyara Rayyan yayi yana amfani da dayan hannun shi ya riko nata da take kokarin kwacewa tana dariya. Yayi kewar wannan rahar a tsakanin su, yayi kewar matar shi, kallonta yake da wani yanayi a fuskar shi

"Nayi kewar ki"

Cikin idanuwan shi ta kalla, ita kadai ce macen da take iya hada idanuwa dashi kai tsaye haka, har maza kance yana musu kwarjini, ko Maryama bata iya kallon shi haka. Maimuna kance

"Kai din nawa ne, nawa ne ni kadai Ahmadi"

Kuma ya yarda shi din nata ne, duk da bai kasance nata ita kadai ba kamar yanda taso, amman natan ne

"Kaji ka, abinda muna tare a gida daya ko da yaushe, me yasa kake magana kamar ka dade baka ganni ba?"

Numfashi mai nauyi ya sauke

"Dan Allah mu daina fada, ki daina mun rigima, mu koma zaman mu kamar da"

Murmushi tayi kawai, murmushin da yake ganin kamar yana da wata manufa data wuce nishadi. Haka suka kasance daren kamar satin amarcin su, har wajen biyun dare, da Maimuna lafe a jikin shi suna bacci. Da yake shi bamai nauyin bacci bane, kwakkwaran motsi ma yakan ji, cikin baccin yake jin kakarin aman da ya sashi bude idanuwa yana saurarawa, sosai yake jin ana kakarin, yaso zame Maimuna a hankali ba sai ta tashi ba dan ya fita ya duba, amman itama din ba nauyin baccin gareta ba

"Ina zaka je?"

Ta furta muryarta cike da bacci tana murza idanuwa

"Kamar Maryama ke amai, bakiji bane ba?"

Ya amsa kasa-kasa saboda dare, tsaki Maimuna taja

"Munafuncine kawai, dan Allah ka koma ka kwanta"

Da mamaki yake kokarin ganin idanuwanta saboda duhun da yake dakin. Rigar shi da yake tunanin tana ajiye wani waje kan gadon yake lalube har ya samota, kokarin sakawa yake a jikin shi Maimuna ta tashi zaune

"Fitar zakayi kenan?"

Ta bukata a harzuqe, hakafa kwanaki ta fito tana wannan kakare-kakaren, Ahmadi ya kwana zarya yana fita dubata. Shine yau daga dawowar shi dakinta zata sake bullo da wannan sanaben

"Kasan dai yau kwanana ne ko? Halin matane baka sani ba Ahmadi? Munafuncine ba wani abu ba"

Kai kawai ya girgiza yana sauka daga kan gadon

"Bari in dubata...."

Itama saukowa tayi, zuwa lokacin idanuwanta sun saba da duhun tana dan ganin shi, aikuwa hannu yaji ta riko mishi

"Babu inda zakaje fa, kanajin ma kamar ta koma daki. Wannan ai shiga hakki ne"

Fisge hannun shi Ahmadi yayi

"Me yake damunki ne wai? Ina tausayinki ya tafi? Ko ta tafi daki bazan duba yarinyar mutane bayan naji sarai amai tayi ba? Kinga Maimuna ki fita idona kafin in saba miki"

Ya karasa yana fara tafiya zuwa hanyar kofa, yanajin ta biyo shi, baibi takanta ba ya fice daga dakin, hasken farin wata ya haske tsakar gidan, ko takalma bai saka ba ya nufi bangaren Maryama, yana shiga ya sameta a zaune da fitilar kwai a dakin

"Maryama? Jikin ne?"

Kai ta girgiza mishi

"Aa wallahi. Amai ne kawai, inajin kankanar dana sha na kwanta ce ta juya mun ciki"

Kuma da gasken take, dan karatun littafin tarihin Annabi (SAW) Kamalalle takeyi bacci ya dauketa anan kasa inda ta saka filo, kawai farkawa tayi tana zufa, kafin taji wani amai ya taso mata, dakyar takai tsakar gida. Duk wani abu da yai saura a cikin nata kuwa saida ta fitar dashi, kuma garas take jinta banda yar galabaita da tayi. Ahmadi bai yarda da ita ba, tsugunnawa yayi yana saka hannu ya taba wuyanta ko da zazzabi, amman lafiya kalau yaji jikinta

"Sannu..."

Murmushi Maryama tayi

"Yawwa... Kaje ka kwanta, kaga da safe zaka fita, gara ka huce gajiya"

Kallonta yakeyi yana son tabbatar da lafiyarta

"Babu wani abu da yake miki ciwo dai ko?"

Kai ta jinjina mishi

"Kin tabbata? Ki fadamun dan Allah"

Murmushi takeyi sosai

"Allah babu inda yake mun ciwo...dan Allah kaje ka kwanta"

Numfashi Ahmadi ya sauke

"Shikenan, Allah ya kara lafiya, idan da wani abin dai kizo ki tasoni kinji ko? Allah ya tashe mu lafiya..."

Kai Maryama ta jinjina mishi, tana kara ganin dalilin da yasa kaf dangi kowa yakejin daman yar shi ce a gidan Ahmadi, ba zata gaji da godewa Allah da wannan damar da ta samu ba, har zai fita ya kara juyowa

"Ko in miko miki ruwa?"

Kai ta girgiza mishi tana nuna kwanon sha da yake a rufe

"Kagan shi nan na dibo fa tun dazun..."

Sannun dai ya sake yi mata kafin ya fita, ya gyara mata labulen dakyau saboda sauro. Kafin ya wuce inda ya samu Maimuna a bakin kofar dakinta tsaye

"Idan cin amana dai kasa a gaba babu inda zai kaika wallahi"

Ta karasa maganar ranta na suya, sai takejin kamar kamshin turaren da Maryama kan hayaqa a zuwan turaren wuta a jikin shi. Watakila wata sa'ar Malamin ta ya bata na fito da Ahmadi tsakiyar dare ta goga mishi wannan shu'umin turaren

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Dan girman Allah Maimuna ki saka ma ranki salama"

Ahmadi yai maganar cike da gajiya, yana mamakin kishi irin nata, wani lokacin yana jin daman ya hakura sun rayuwa su kadai kamar yanda taso, daya kaucewa duk wannan rigingimun

"Ta ina zan fara sakama raina salama bayan baka bani wannan zabin ba? Bance maka munafunci bane, kawai bata kaunar ganin na kebance dakai saita tsiri wani abin da zaka ha'ince ni"

Rabata yazo yi, gara ya wuce ya kwanta, inya tsaya biye mata zaiyi. Kamar ba ita bace tagama mishi alkawarin zasu zauna lafiya dazun nan. Amman sai ta tare kofar, wani irin kishine turnuke da zuciyarta, kamshin turaren Maryama da hancinta yake jiye mata sai take ganin kamar wani abin sukayi a yan mintina daya dauka a dakin nata da sukai mata nisan awanni, tare mishi hanya tayi

"Ka koma dakin nata mana, ka koma inda ka fito Ahmadi tunda haka kake so tun daga farko"
Chapter 5 · 0% Book details