← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 93

Sashe 83

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar maganganun shi na kara tunzurata, kuka takeyi sosai, bai hanata ba, bai dai daina gaya mata yana tare da ita ba cikin wata murya da take kara karya mata gabban jikinta. Ba zatace ga iya lokacin da suka dauka a haka ba, ta dai tuna yanda ta samu dakyar tana mikewa.

"Ina tare da ke"

Da Rayyan ya fadi ce ta rakata dakinta, ya kai mintina biyar kafin shima ya iya mikewa. Idan ma bata yarda ba zaici gaba da fada mata daga nan har lokacin da zata yarda da shi. Saboda wannan zaman da sukayi kawai ya kara tabbatar mishi da ana halittar wani dan wani, dan yanajin zuciyar shi an halitta mishi itane kawai dan ta dokawa Layla ita kadai, ita din tashi ce kamar yanda yake fadi a ko da yaushe.

"Aure zanyi Bilal, har yanzun ba zaka dawo ba ko? Da gaske wannan karin ba zan yafe maka ba"

Shine abinda ya fadi bayan ya shiga daki da dukkan zuciyar shi yana fatan Bilal din zaiji shi ko ta wanne haline. Saboda kwanakin sun fara mishi tsayi.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 16, 2021.

31

"Abbu ka yafe mun, dan Allah Abbu ka yafe mun, duk ku yafe mun..."

Shine kalaman da sukewa Abbu amsa kuwwa a cikin kunnuwan shi harma da kai. Muryar Layla na zauna mishi da wani yanayi, yanda tayi maganar kamar tana saka ran fitar duk abinda yake cikinta zaizo ne da ajalinta. Da kan shi shekaranjiya bayan sun sake kwasowa zuwa asibiti cikin dare ya samu likitan yace

"Wai ba zakuyi mata aiki ku ciro abinda yake cikin nata bane? Tun da satin nan ya kama yarinyar nan take cikin wahala, dan Allah ku duba lamarin"

Murmushin karfafa gwiwa likitan yayi mishi yana kuma bashi tabbacin babu wata matsala dan wasu matan nayin haka. Ba zai manta ba, ko Mami takan yi doguwar nakuda, ta Layla din ce dai take tsaya mishi a rai fiye da duk wadanda yagani a baya. Nakudar ce saita taho mata gabaki daya sunzo asibiti sai kuma ta lafa ace ba haihuwar bace su sake kwasa su koma, yau ne karo na hudu a sati daya. Ita take ciwon amman zai iya rantsewa rashin natsuwa ya saka sunyi zuru-zuru gabaki dayan su. Yau kam ko da sunce ba haihuwar bace shikam zaice a barta a asibitin ne kawai.

Bai san akwai tsoron da zai danne na ganin jikan da zai diro ahalin su da gurbataccen asalin da bashi da masaniya a kai ba sai yau. Ko da yake zaice akan cikin Layla ya fahimci ba mata kadai ke da gulma ba, ba kuma su kadai tsegumi ya tattara ya zaunawa ba. Tun bai gane kallon da akeyi mishi a masallaci ba, da yanda har wani dan jinjina kai wasu a cikin mutanen unguwar sukeyi kamar alamun tausaya mishi duk idan sun hada idanuwa, ciki harda mutanen da gaisuwar musulunci ce kawai take giftawa a tsakanin su.

A cikin irin mutanen ne wani ya iya samun karfin gwiwar tarar shi sun fito daga masallaci yana fadin

"Alhaji ashe kuma haka wannan lamari ya faru da yar wajen ka? Allah ya kiyaye na gaba, kasan yarane yanzun ka haife su baka haifi halin su ba, kana iya kokarin ka akan tarbiyar su suna dauko maka magana. Allah dai yasa an dauki hukunci mai karfi akan yaron da yayi ta'asar"

Tunda ya fara magana kallon shi kawai Abbu yakeyi, shi da kan shi sai da ya tsargu ya fara kame-kame yana barin wajen. Amman tabbas zantukan shi sun rigada sun isar da sakon da yake son su isar a zuciyar Abbu, mutane sunyi gaskiya, zancen duniya baya boyuwa, ba kuma komai bane idan ka binne yake kwanciya lafiya, wasu hawaye yaji masu zafin gaske sun taru a cikin idanuwan shi. Da girman shi da komai, ashe kallon tausayin da kowa yake mishi kenan a cikin unguwar, kallon yanda martabar gidan shi da ahalin shi ta tabu. A ranar sai da ya kasa hakuri yake labartawa Mami abinda ya faru, sai dai murmushi tayi mai cike da karayar zuciya.

Don dai batason kara daga mishi hankali shisa bata fada mishi ya taushi zuciyar shi ba, ba zatace ga lokacin da maganar cikin Layla ta bullu a cikin dangin su ba, ko ta hanyar da hakan ya faru. Duk da tana son dora alhakin akan Anty Uwani, dan itace ta zo gidan tayi sa'ar ganin giccin Layla, duk da a lokacin akwai hijabi a jikin Layla, kuma cikin duka bai shige watanni ukku ba. Da farko bata kawo komai a ranta ba akan yawan ziyarar da yan uwa na jiki da na nesa suke kawo mata ba, sai da suka fara tambayar inda Layla take da yanda suka kwana biyu basu ganta ba, suna yin tambayar idanuwan su na yawo a cikin gidan kamar zasu iya hangota ta cikin daya daga bangwayen da suke zagaye da dakin.

"Tana lafiya. Alhamdulillah"

Shine amsar da suke samu, sai ko murmushi mai ciwon gaske daga wajen Mami din, tana so tace musu Layla tana makaranta ko dan gujema tarin tambayoyin su, shisa a irin lokuttan take zabar ta mike ta kawo musu abin sha ko ta kawo wani zancen da zai sa su kyaleta, amman sai sun san yanda sukayi suka dawo da zancen akan Layla. Tun tana kuka bayan tafiyar kowanne a cikin su har zuciyarta ta bushe. Duk zuwan bai musu ba sai da suka dinga turo yaran su 'yan matan suna kusan yini a gidan. Haka makota ma da suka fara mata zarya, har mutanen da bata taba sanin da zaman su a cikin unguwar ba.

A lokacin ma cikin Layla ya shiga wata na bakwai, sun fita kenan zasuje awo, ita da Layla da Jabir da zai kaisu, basu karasa fita kwalta ba Layla ta zage gilashin bangarenta tana zura kanta saboda amai daya taso mata. Hakan yasa dole Jabir din yayi parking a gefe ta fito, wahala ma tasha dan batayi aman ba. Sai ruwa da Jabir ya dauko mata na roba ta kuskure bakinta tana kuma wanke fuskarta. Mami ma hankalinta yana kan Layla da ta jigata, tun da rabonta da wasu amai tun cikin na karami, taji Jabir yace

"Da kin karaso ai saiki fi ganin mu da kyau"

Hakan ya sata daga kai ta sauke shi kan matar da bata ga fuskarta ba sai bayanta saboda ta wuce da sauri har tana tuntube, kai kawai Mami ta jinjina suka shiga mota suna tafiya. Har suka kai Jabir na kwashewa matar albarka

"Aikin banza, shisa rayuwar turawa tayi wallahi, babu wanda ya damu da kai ballantana"

Ita dai batace mishi komai ba saboda jikinta da yake a sanyaye. Haka mutane suka dinga shigiwa gidan, wasu da uzurin an kwana biyu ba'a gaisa ba, ko zasu wuce shine suka biyo. Murmushi Mami takanyi, tasan gulmace da tsegumi kawai ya shigo da su, idan basu ga Layla ba ta boye tana daki, lokaci zaizo da zasu shigo gidan kukan duk abinda zata haifa in dai ya taka duniya zai tabbatar da zargin su idan tantama sukeyi. Ta jima da daina gujema kaddarar da ta same su, idan tana boyewa babu abinda zai karawa Layla sai tarin damuwa fiye da wadda take ciki.

Ga duk zuwa awon da zasuyi sai likita ya kara musu kashedi kan kwantar mata da hankali saboda jininta da ya hau, abinda ba'a so a tare da mai ciki. Yan uwanta ma gulmar sukeyi, dan wasu yan unguwa sunyi bata ga laifin su ba, masu dalilin da zasuyi mata uzuri ma basuyi ba, kowa dan yatsa ya daga ma kaddarar da ta same su kamar su din sunfi karfin hakan, kamar su din suna da dabarun kaucewa abinda ya sameta. Dan akwai matar da tana shigowa gidan sun gaisa ta zauna sai ga Jabir shima ya shigo ya gaishe da matar yana wucewa kitchen.

Kallon sani Mami takeyi mata, amman ta rasa inda tasan ta

"Nasan baki gane ni ba ko? Matar Balarabe ce da muka zauna nan baya"

Kai Mami ta jinjina, shekaru wajen tara ba wasa bane ba, kuma ko da can din da suka zauna anan unguwar tasu in ba jaje ko barka ba, babu abinda yake hadasu

"Allah Sarki, shekarun ne da yawa shisa, duk ina yaran, ya wajen Salamatu"

Wata yar dariya matar tayi

"Kowa lafiya, na shigo unguwar ne nake jin rasuwar Bilal, nace aikam zan shigo in muku gaisuwa. Allah yayi mishi Rahma"

Bayan Mami ta amsa tana shirin mikewa kenan dan ta kawo mata ruwa tace

"Allah dai ya kara karemu, ashe haka abubuwa duk suka faru, ga yar wajen ki din nan da akace kina riko ya take da suna ita kuma ta dauko magana, abin ya bani mamaki kwarai..."

Kallonta Mami takeyi, kafin ta iya yin wani tunani Jabir ya fito yana fadin

"Menene abin mamaki?"

Ko ina na jikin shi bari yake da bacin rai, sosai yanzun mutane suke bashi mamaki, yana kuma sake jinjina ma Rayyan da tun da wuri ya gane halayen mutane ya nisanta kan shi da su. Shima abinda yakeyi kenan yanzun, saboda su din basa gajiya da yin abubuwan da zakayi komai dan ka gujewa zama jinsun su

"Jabir"

Mami ta kira, kai ya girgiza mata yana fadin

"Layla! Layla!!"

Yana kallon matar da take ta kifkif da idanuwa cike da tarin rashin gaskiya

"Layla!"

Jabir ya sake kira lokacin da yayi dai-dai da fitowar Layla da take rike da bayanta, idanuwanta na fara sauka akan Jabir da yake takawa ya karasa inda take yana kamo hannunta, bin shi take cikin rashin fahimta harya zo da ita tsakiyar falon yana tsayar da ita a gaban matar

"Ki daina mamaki yanzun, ki gani da idanuwan ki, saiki fita ki sake tabbatar musu idan akwai mai sauran mamaki ya bari, idan suma zasu shigone su ganta su shigo"
Chapter 83 · 0% Book details