← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 93

Sashe 19

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta furta cikin rawar murya, idanuwanta kan rage bashi tsoro idan suka cika da ruwan hawaye haka, sai yaga sun kara sake mishi launi, sakin hannunta yayi, yana kallon yanda ta yarfe shi tana murzawa. Bude baki yayi zai magana, Maimuna da ta leqo ta gansu a tsaye tana saka shi mayar da bakin shi ya rufe

"Ina wuni..."

Layla ta furta tana kokarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta bayan ta, wata irin harara Maimuna ta zabga mata, kamar surutai taji, kuma sai muryar tayi mata kamar ta Rayyan, shisa ta leqo, sanin in dai surutun shi ya yawaita to da Bilal ne. Zaka iya kirga maganar shi, itama a fuska da yanayi zakaji yanda yake yinta kan dole. Yana iya bata maka rai kayi shiru ka kyale shi, sai da gabanta ya fadi da ta gan shi tsaye da Layla, sai taga kamar data fito yana rike da hannun Layla din, daga ranar farko da ta dora idanuwanta kan Layla bata kaunarta ko kadan, kuma ta tabbatar da Layla ta san haka.

Ko tare suka shigo da su Haris sai ta koreta, itama Layla din a nata bangaren hakane, Ayya na daga cikin jerin mutanen da bata kaunar gani, da hankalinta ita ce ta farko da ta kirata da mayya. Gashi ko a hanya suka hadu cikin gidan sai ta bita da harara, tana gaishe da itane saboda Abbu, dan a yanda taki jinin Ayya ko Mami bata isa tasa ta gaisheta ba, darajar Abbu take ci, dan tana jin shi har ranta, batayi wayan sanin iyayenta ba, gara mahaifinta zata iya tuna fuskar shi, sai kuma tsillin hotunan da Mami ta samo mata nashi bayan ya rasu sanadin gajeruwar rashin lafiya.

Na rana daya Abbu da Mami basu taba bari taji maraici ba, komai da take so Abbu yana mata, a fuskar shi ma bai taba nuna cewa ita din ba daga jikin shi ta fito ba. Haka dakin Maimuna banda ita da Rayyan duka suna zaune lafiya da sauran yaran, babu mai nuna mata tsana ko wariya. Gara ma Intisar wasu lokuttan takan mata magana taqi amsata. Shisa bata damu dan bata amsa gaisuwar ba yanzun, juyawa tayi zata tafi abinta, muryar Rayyan ta katse ta da fadin

"Na ce na gama magana da ke?"

Tsaye tayi cak, Ayya da take kallon su da mamaki bayyane a fuskarta ce tayi magana

"Rayyan..."

Ta kira cike da mamaki, idanuwan shi ya dauke daga kan Layla yana mayarwa kan Ayya, jin tayi shiru yasa shi cewa

"Ayya"

Cike da mamaki har lokacin tace

"Me zatayi maka?"

Dan ita batasan lokacin daya fara magana da Layla haka ba, zata tuna lokacin kuruciya da, har saida ta fara jin wani iri kan yanda Rayyan din ya addabi yar mutane, haduwa goma zasuyi sai ya kwada mata mari, akwai tabon da har yanzun yana gefen goshinta inda Rayyan din ya hankadeta ta fadi, ranar ita kanta Ayya hankalinta ya tashi, dan bayan Maryama ta dauke Layla sai da ta daki Rayyan din. Hakan ba yana nufin taji kaunar Layla ko kadan a ranta bane, yanzun da suka fara tasawa, inba Abbu ya aiko Layla ba, yarinyar bata fara shigo mata daki.

Ta san dai Bilal ne da babu yanda zatayi da shi akan nacin Maryama da yakeyi, bata da matsala da yaran Maryama din, Haris ne daman, kuma shekarun nan sun sa yaran ya shiga ranta, da wahalar gaske ma kayi zaman awa daya da Haris bai shiga ranka ba. Wani lokaci anan falon ta yake cin abinci. Sauran yaran ne in dai tasan abu daga bangaren Maryama ya fito bata bari suci, Bilal ne kawai yake shigo mata da shi har daki kuma ya zauna yaci. Tama gaji da magana tunda dariya yakan yi yace

"Ayya..."

Da yanayin nan nashi da yakan yi duk idan tayi mishi maganar za'a barbada mishi wani abu a abincin. Kamar bai yarda yana iya faruwa ba. To tasan yana magana da Layla, ko tace Laylar ta nace mishi, kwanakin baya har zancen tayi mishi

"Bilal kaima ka fara koyon taurin kai, idan nayi magana ma ba jina zakayi ba. Banason yarinyar can tana naniqe maka, kafin ta lashe maka kurwa... Ko dan Maryama ta fara lashewa, ragowa ce Layla zata samu, kaga saika hada kayan ka gabaki daya ka koma can, in rasaka hankalin su ya kwanta ita da uwar rikon ta"

Dariya Bilal din yayi kamar a duk ranar babu wanda ya fadi wani abu da ya saka shi nishadi irin maganganunta

"Dan ubanka sai kaje kayi ai, tunda kaga ka fini tsayi, ka rainani ai"

Yana dariyar yace

"Yi hakuri, haba Ayyata, ni na isa"

Harar shi tayi tana wucewa abinta, haka ya bita yana mata hirar shi har saida ta huce. To batajin tana da matsala da Bilal, kowa ma kulawa yakeyi shi, kusan halin shi na mata shige da Haris, bambanci shine zakagani a fuskar Haris idan ka mishi abinda baiso ba, Bilal kam ko kayi tunanin ka bata mishi rai sai dai yayi dariya kawai. Amman Rayyan, zuciyarta rawa takeyi mata, saboda Rayyan daban ne, su Rukayya ma baya magana dasu mai nisan da taji yanayi da Layla din. Yanda ya tsare yarinyar da idanuwa yake yanzun yasa ba zuciyarta ba har kafafuwanta ma rawa taji sunayi.

Tana can tana tsoron Layla karta lashe kurwar Bilal, ashe lallabowa tayi wajen Rayyan, shiru yayi yana kallonta

"Tambayar ka nake kana jina"

Yanda yakan yi duk idan bayason yin magana an saka shi yayi dole shi yayi da fuskar shi yanzun ma

"Ina magana da ita ne Ayya..."

Ya amsa, yana saka kirjinta wani irin lugude, ko ita Rayyan baya tsayawa yayi wata magana da ita. Bilal ma ta kanga yana bin Rayyan din idan yana son magana da shi. Asali yaune rana ta farko tun tasowar shi da taji yace yana magana da wani har ya tsayar dashi dan basu gama ba

"Rayyan..."

Ayya ta kira wannan karin da bayanannen tsoro a muryarta

"Idan nagama zan shigo"

Ya fadi yana dauke idanuwan shi daga kan Ayya. Hannun Layla ya kama yana fisgarta cikin yanayin da yasata binshi dole, suna barin Ayya tsaye ta saki baki cike da mamakin abinda ya faru a gaban idanuwanta. Cike da ta'ajjabin da gaske a gabanta Rayyan ya damki hannun Layla batare da tunanin abinda yayi ba dai-dai bane a tafarkin addini idan bai guji bacin ranta ba, idan ma ji yake dan in aka bibiya ta wani bangaren ya hada jini da Layla, kuma sun taso gida, ai hakan baya nufin ita din muharramar shi ce.

Bayan wannan ma, yaushe Rayyan ya fara magana da Layla, yaushe ya sakata cikin jerin mutanen da yake kulawa, harma kusancin su ya kai na ya damqi hannunta ya jata subar waje kamar akwai zancen sirrin da sukeyi da bayaso ita taji. Rayyan fa, Rayyan dinta da take daukar kafafuwanta, ta karya matsayinta na mahaifiyar shi mai cikakke iko da hakki a kan shi ya taso yazo har inda take ya gaisheta, taje dakin su dan kawai ta saka shi a idanuwanta. Shine yau take ganin kusancin da tayi shekaru tana neman ta samu a tare dashi yana nunawa akan Layla, akan mayyar yarinyar da taki jinin ta wayi gari ko a tunaninta tajita, balle kuma ta saka ta a cikin idanuwan ta

"Bayana kike son gani Maryama... Sakani raba Ahmadi dake bai isa ba? Kassarani kike neman yi shisa kika kawo wannan mayyar..."

Ayya take fadi muryata na rawa, cikin tashin hankali kamar wadda ta samu tabin kwakwalwa. Gabaki daya hankalinta idan yayi dubu kowanne a tashe yake

"Tafdin... Na rantse da Allah ba'a isa ba...ina tunanin wuta a makera ba zanji tashin ta a bayan gari ba"

Duk tsoronta akan Rayyan, duk tunaninta akan halayen shi ta alakantasu ne da abinda tayi kuskure ya sha, sanadin da kawancen su da Khadi bai koma kamar da ba, saboda tayi da ita su koma wajen Malam taqi, sai tama dinke mata, sam ta daina labarta matsalolinta da ita. Gwaggo ce a lokacin kafin rasuwarta, idan ta matsa sai tace mata tana karbo taimako a wajen Malamin Khadi. To dan Rayyan ne ta dinga amso karya tambaya, da yana yaro in ta danne shi tana samu ta dura mishi, daga baya ba zai sha ba, banda abinci sai ruwan leda, ko ya tarya a fanfo, ko zobo ta hada Rayyan baya sha sam.

Bata san ba abinda yasha bane yake dawainiya da shi sai yanzun, bata dauka Maryama na bibiyarta da yaranta ba har yanzun sai yau

"Minna, Neja da Bidda ma ubansu yayi kadan wallahi, balle kuma wata yar banufiya da uwar rikon ta..."

Cewar Ayya, bacin rai da tunanin barkatai na maye gurbin tsoronta, tana murna yaronta ya sami gurbin karatu a jami'ar da ake ji da ita a fadin Najeriya, kuma Abbu sai alfahari yake da fannin da zai karanta shine ake neman kassara shi

"Wallahi da sake..."

Ayya ta furta tana samu taja kafafuwanta da sukai mata mugun nauyi tana komawa daki, kanta harya fara sarawa da tashin hankalin da take tunanin ya kunno mata kai.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 14, 2020

08

Da wani yace mishi zai iya shekara daya a wani gari daban, nesa da Bilal, nesa da Layla da bai taba tunanin kewarta zata danne shi haka ba zai karyata. Dare da yawa ya sha farkawa ko shan ruwa da yakan yawan yi ko kuma wani abu daban ya tsinci kan shi da kasa komawa bacci, saboda kawai yana tunanin Layla. Yana tunanin ko tana kewar shi ko batayi, ranar da zai tafi bata neme shi ba sam, yafi mintina talatin a tsaye kofar daki yaki fitowa yana jira ko zata shigo tayi mishi sallama, amman shiru, sai da ya taka ya sameta har bangaren Mami, duk da bai shiga ba a bakin kofa ya tsaya yana kwala mata kira, ko da ta fito sai ya rasa abinda zaice mata.
Chapter 19 · 0% Book details