← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 93

Sashe 38

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilal ya fadi, yana kallon yanda lokaci yasa labban Rayyan har sun fara duhu saboda hayakin da yake bukama cikin shi, yau ma tunda sassafe da sigarin ya karya. Allah ne shaidar Bilal har a sallah yanzun addu'ar barin shan yake wa Rayyan. Kara daya ya zaro yana sakawa a bakin shi kafin ya mayar da kwalin aljihun shi, ya dauko lighter ya kunna. Sai da ya zuqa ya fitar da hayakin sannan yace

"Ka barni Bilal, bana jin dadi"

Numfashi Bilal ya fitar

"Sai aka ce sigari ce jin dadin?"

Kara sauri Rayyan yayi yana cigaba da zukar sigarin cike da kwarewa

"Allah ya kyauta"

Cewar Bilal da zuciyar shi take kara yin zafi. Kafin su kai gida sai da Rayyan din ya sha kara hudu na sigarin. Shayi suka sha da cin cin din da Layla ta kawo musu. Bilal na daukar takardun shi ya fice daga dakin dan karatu zai koma cikin makaranta yayi, tsallaken kwana daya yake da shi kafin jarabawar shi da ita kadai ta rage a zangon. Rayyan kwanciya yayi yana runtsa idanuwan shi da suka fara nauyi da alamun bacci, duk da yamma tayi. Idan baccin ya kwace mishi yasan sai dai wani ikon Allah zai samu ya runtsa da dare. Kuma kwakwalwar shi na bukatar hutun. Akwai tarin abubuwan da yake bukatar saka mata na jarabawar shi ta gaba.

A hankali bacci ya dauke shi da mafarkin Layla kwance a gefen shi da baisan dalilin da yasa ta kutso mishi cikin mafarki ba. Duk da yana wata duniya daban bai hana shi furta

"Mayya..."

Cikin kan shi a duniyar ba.

*

Rayyan suka tsaya jira su dukkan su, shine karshen gama jarabawa, duk sun riga shi. Aisha ma da aka kirata a gidan su dan azo daukarta ca tayi musu zasu taho tare da su Bilal, da yake babu wanda bai san shi ba a gidan, babu kuma wanda bai aminta da shi ba sai suka amince. Ran safiyar asabar duka suka shirya. Bilal yaje ya dauko motar daga gidan abokin Abbu, dan ran juma'a yaje yakai an duba lafiyarta ya kuma zuba mai. Daga gida da suka dauki kayan su makaranta Bilal ya nufa. Yana kallon Rayyan daya bude gidan baya ya zauna, baice mishi komai ba.

Dan tun jiya rabon da suyi magana, daya gaishe shi da safen nan kai kawai ya daga mishi, yan shiru-shirun sunzo fiye da kowanne lokaci, yakan dade Bilal bai gan shi a yanayin nan ba. Yasan ko me zai fada asarar bakin shi zaiyi, ba amsa zai samu ba. Abinda bai sani ba shine rabon Rayyan da ko gyangyadi kwana biyu cur, baccin ranar daya kan samu ya neme shi ya rasa. Duniyar a cunkushe yake jinta. Ga shi jiya ma bai samu ya ga Layla ba sam-sam. Ta zo ma gidan nasu da bata gan shi ba jiya batayi ba, ya sa ran zai ganta.

Watakila fushi take yi mishi tun shekaranjiya, ba zai iya tuna kan me yai balbaleta da fada ba, fadan kawai yake iya tunawa. Har waya da safen nan ya dauka da niyyar kiranta yaji ko ta gama shiryawa sai kuma ya fasa. Zai ganta babu jimawa, a bakin kofar hostel kuwa suka same su ita da Aisha suna ta hira. Bilal ya fita ya saka jakunkunan su a bayan mota. Aisha tsaye tayi cikin rashin sanin inda ya kamata ta shiga ta zauna ganin Rayyan din a baya, ta dauka ita da Layla ne zasu zauna a gaba. Layla ta samar mata mafita da ta bude bayan motar tana shiga. Hakan ya sata bude gidan gaba ta zauna, Bilal ma ya shigo yaja motar.

Sun gaisa dashi da safe, kara gaishe da shi Aisha tayi tana juyawa tace

"Hamma ina kwana"

Kai kawai Rayyan ya daga mata, da yake ta fahimci halin miskilancin shi da mutane da yawa zasu iya dauka wulakanci sai ta juya kawai. Layla kallon shi tayi, yayi kyau sosai sosai cikin farin yadi da ya saka. Yau harda hula, bawai baya saka manyan kaya bane kwata-kwata, yakan dai kwana biyu bai saka ba. Ga dinkin rigar dogon hannune mai links, ta kasa daina kallon shi, kyau yayi mata yau fiye da kowanne lokaci, zuciyarta har wani kumbura take da tarin soyayyar shi da batasan yawan ta ba. Amman inda take Rayyan bai kalla ba, asalima kan shi ya jingina da kujerar motar yana lumshe idanuwan shi.

"Hamma..."

Ta kira, muryarta iya kunnuwan shi, jiya fushin da ta kwana tana yi mishi bai yini ba, son ganin shi ya danne mata komai. Yanayin da har ya saka tunanin ko da gaske ne? Maitar da Mami take karyata cewa ta gada ta bangaren mahaifiyar ta, duk da zuwa yanzun shi kadai dinne yake kiranta da

"Mayya..."

Saboda idan har da gaske bata kasance mayya ba ya kamata ace zuciyarta ta hakure da shi, ya kamata ta sama musu sauki su duka biyun, sai dai kamar yanda batasan lokacin da ta fara son shi ba, haka bata san ta inda zata fara dai nawa ba. Idan ma yaji bai nuna mata alamar hakan ba, son jin muryar shi takeyi da dukkan zuciyarta

"Hamma"

Ta sake furtawa, tana dan kallon su Bilal, hira suke sosai, da alama hankulan su baya kanta. Sake kallon Rayyan da bai motsa ba har lokacin tayi, tun kiran farko da tayi mishi yaji ta, asalima tun daga nesa ya hango ta, ta saka material ruwan toka, sai farin mayafi, yau idanuwanta ya fara hangowa zuciyar shi na tsinkewa, sai dai yana dauke idanuwan shi daga kallon nata ya mayar dasu kan yanda tayi kyau sosai, sai yaji yanayin daya kwana biyu baiji ba, riketa yake so yayi, wani kusanci yake son samu da ita komin kankantar shi. A kwanakin nan biyu da yayi su a hargitse ganinta ya saka shi jin kamar daya riketa koyayane wani abu zai natsa mishi.

Dakyar ya raba idanuwan shi daga kanta yana kallon Bilal da suka hada ido ta mudubin gaban motar, kai Bilal din ya girgiza mishi a hankali, kamar yana san abinda yake tunani, kamar yana son fada mishi karya fara aiwatarwa. Wani irin yanayi zuciyar shi ta shiga lokaci daya, idanuwan shi a bude suke, kuma safiya ce, baisan me yasa yake ganin duhu ba. Tana zagayo ta shigo ya zabi ya rufe idanuwan shi, har wani dumi jikin shi yake dauka da son rike ko da hannunta ne. Ya rasa kalar sabon da yayi haka da haduwar da jikin su yake yawan yi.

Jin Layla tayi shiru yasa shi kara runtsa idanuwan shi yana kokarin fitar da numfashi a tsanake, ba lokaci yake gani ba, banda sautin karar mota da yake nuna alamar sun dauki hanya babu abinda yake ji, sai numfashin Layla da baisan ya akayi kunnuwan shi suka tsinto mishi shi ba, kusan yanajin bugun zuciyar ta ta hakan. Kafin yaji dumin hannunta cikin nashi da yake akan kafar shi. Kamar hannun na da ikon kan shi na budewa ta saka yatsunta a ciki tana dumtsawa, yanayin da yaji har kasan zuciyar shi

"Nagode..."

Ya furta a hankali yana kara dumtsa hannunta, saurin kallon fuskar shi tayi, sai taji kamar godiya yayi mata, amman bata ga alamar ya motsa komai a fuskar shi ba. Da badan wasa da yake da hannunta da ta saka a cikin na shi ba sai ta iya rantsewa da cewar bacci yakeyi. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tana jin kamar yau akwai abinda yake damun shi fiye da kullum, watakila kuma tunaninta ne kawai. Aisha bacci tayi dan ita sai dai in iskar mota bata fara kadata ba. Ta mudubi Bilal yake kallon su, da alama Rayyan ma bacci yakeyi, Layla kuma ta kwanta a kujerar ne tana fuskantar shi, idanuwanta akan shi kamar a duka duniya babu wani abu da ya taba daukar hankalinta irin Rayyan din yana bacci.

Yanayine da ya sa na wasu dakika Bilal ya manta da tuqi yakeyi saboda zafin da kirjin shi ya dauka. Yana kallo Layla ta daga hannunta da nufin taba fuskar Rayyan din, duk daukarta bacci yake, kamar zare ta gani a gefen fuskar tashi kan kasumbar da ta sha gyara, lokacin da yai saurin damkar hannunta da dayan hannun shi, lokacin kuma da Bilal ya taka motar yana kaucewa karawa wata mota da ta ke tahowa, B Rayyan ba hatta Aisha sai da ta bude idanuwanta tana fadin

"Subhanallah..."

Shima Bilal din duk wata addu'a da tazo bakin shi yi yake. Sun kusan mintina biyu kafin ya samu natsuwa dan ya rage gudun motar sosai. Rayyan kuma hannun Layla daya damqa ya saki yana kokarin saka idanuwan shi cikin nata duk da yanda zuciyar shi tayi wata irin dokawa

"La hawla wala quwwata ila billah"

Ya furta a cikin kan shi ganin kamar ya hada idanuwa da mage, kwayar ce kawai da ta Layla take a zagaye, ta mage kuma a tsaye. Dan runtsa idanuwan shi yayi, yana komawa cikin kujerar ya kwanta yana bata damar sauke nata, tana kula da yanda ba kullum yake kallon cikin idanuwanta ba. Kamar yasan duk idan yayi sai taji wani abu yana fisgarta a cikin su kamar igiyar ruwa. Bata da wasu kalamai da zasu fassara asalin yanda take ji duk idan ya kalleta, ta sha kallon mutane sun nitse a cikin ruwa a fina-finai daban-daban, takan kuma ji a labaran yau da kullum. Bata taba hasaso yanda yanayin yake ba sai lokacin farko da ta fara mallakar hankalinta, lokacin da Rayyan ya saka idanuwan shi a cikin nata.

Sai taji ta tsundum cikin ruwan da batasan da bata ganin farkon shi balle karshen shi, take numfashi ya soma mata barazana, yau ma hakan take ji, dan har bakinta ta dan bude tana fitar da iska daga cikin shi. Zuu din wayarta ya dan taimaka mata sosai, da alama sun dan sake shiga wajen da network ya dawo, dan daga fuskar wayar tayi tana saurin mayar da ita ta kife, ta kalli Rayyan taga ya mayar da kan shi, idanuwan shi a rufe suke kuma, duk da haka zuciyarta kamar zata fito saboda bugun da ta kara, sakonnin duka daga group din

"Sirrin ma'aurata zalla"
Chapter 38 · 0% Book details