Sashe 70
Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taji shi, ko karfin kirki bata da shi balle tayi motsi, hannunta ya kama yana dagata, batayi musu ba ta mike. Janta ya farayi, suka wuce Mami da take zaune a kasa kan kafet, sai da ya kaita dakinta sannan yace
"Kinyi sallah?"
Kai ta girgiza mishi batare da ta kalle shi ba
"Tun dazun kina waje Layla? Baki tashi ba? Anan kika zauna rana ta kare akan ki? Baki da hankali ko?"
Idanuwanta taji sun kara cika da hawayen da ta dauka sun kare mata da fadan Jabir din
"Ki wuce kiyi sallah"
Batayi mishi musu ba ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito, tana cikin sallah taji shigowar Jabir din kafin ya ajiye kofi yana sake ficewa. Sai da ta gama gabatar da sallolinta duka, zuwa lokacin an kira isha'i shisa tayi, bakinta yayi nauyi, bata san kalar addu'ar da zatayi ba. Dan sallar ma sai take ganin kamar ta makale ne a wani waje, kamar ba zata isa inda za'a karba ba, saboda cikin da yake jikinta, saboda daudar da take ji a tattare da komai nata. Kofin da Jabir ya ajiye ta dauka, shayine mai kauri ya hada mata, sai taji cikinta yayi wani qugi da yunwar da take tattare da ita, ga zazzabi ya sake saukar mata.
Tana kurbar shayin hawaye na zubar mata, batama gama sha ba taji muryar Mami a saman kanta
"Abbun ku yana kira"
Mami ta furta tana juyawa, dan shayin da ta samu ya shiga cikinta taji yana barazanar dawowa saboda tashin hankali. Shisa ta dade a zaune kafin ta iya mikewa. Kara hautsinawa cikinta yayi da taga Rayyan din, gefen Mami ta zauna, tana kokarin ganin idanuwan Rayyan ko yayane, amman a tsaye yake ya jingina bayan shi da bango, kan shi a kasa. Wani irin shiru ne a cikin daki da kowa yake ji a jikin shi kamar bargo, ganin Yaya Ayuba bashi da niyyar cewa komai yasa Abbu yanke hukuncin yin magana, ya dauka zai saukaka mishi komai ta hanyar yi ma su Mami bayanin shawarar da suka yanke.
Ya bude bakin shi ya kai sau biyu yana rasa ta inda zai fara ko abinda zai fada din
"Rayyan zai auri Layla"
Ya furta, maganar na zuwa kunnen shi da wani irin yanayi. Sai lokacin Rayyan ya dago ya kalli Layla, zuciyar shi ciwo take cikin yanayin da bai taba tunanin zatayi ba, ita ma so yake taji abinda yake ji, musamman da ta dago tana sauke nata idanuwan cikin na shi, yau tashin hankali ya korar mishi tsoron idanuwanta da yake ji. So yake taji ciwon da yake ji, taji rabin abinda ta saka yake ji, batare daya dauke idanuwan shi daga cikin nata ba yace
"Ba zan aure ta ba Abbu"
Karar rushewar wani abu Layla taji cikin kunnuwanta, amman ta rasa daga inda take fitowa, tashin hankalin da take ciki yanzun yafi duk wani tashin hankali da ta taba cin karo da shi a baya. Dan bata san lokacin da ta kai hannuwanta tana jijjiga Mami da take zaune kusa da ita ba, hawaye ne masu zafi wani nabin wani suke zubar mata
"Mami ba zai aure ni ba... Hamma ba zai aure ni ba Mami"
Layla take fadi tashin hankalin duniya yana tarar mata waje daya, yanayin yanda take fadar maganar tana fitar da numfashin da take kokawa da shi da yanda take jijjiga Mami shi Ayya take kallo, kafin ta dubi Rayyan da idanuwan shi suke kafe akan Layla kamar kukan ta baya taba zuciyar shi. Namiji kenan, daga randa Abbu ya hada soyayyarta da ta Mami tasan da gaske baka shaidar namiji, shikenan fa, ya gama da Layla, yana da damar da zaici gaba da rayuwar shi kamar komai bai faru ba, surutun da mutane zasuyi ma da wahala ya bi takan shi. Zai dauki lefin yin cikin da yake jikinta ne kawai.
Abinda Ayya take da yakinin ba zai hana shi auren yarinya kimtsatsiyya ba, amman ita Layla zai hanata auren namiji kamili, ko da ta samu, surutan dangin shi zasuci gaba da binta har karshen rayuwar ta, yaji mata ciwon da samun saukin daukar tabon shi na tare da auren shi ne kawai. Duk da shima din babu tabbacin ba zata fuskanci wulakanci a wajen shi ba, musamman yanzun daya furta ba zai aureta ba. Bata son yarinyar har yanzun, tunaninta a tare da Rayyan na saka cikinta kullewa, amman bai hanata tausaya mata ba, bai kuma hanata tsanar son kan da Rayyan yake sonyi ba.
"Wacce magana kakeyi Rayyan?"
Kawu Ayuba ya tambaya yana kallon Rayyan din, shima kallon shi yayi
"Ba zan aure ta ba, bana son ta Kawu"
Ya karasa yana jin zuciyar shi na ihun karyata kalaman, a hade da hakan yana jin ciwon da takeyi mishi
"Bana son yi maka baki Rayyan... Bana..."
Abbu ya fara, Bilal yana katse shi da fadin
"Abbu..."
Ganin kamar baiji ba yasa shi kara fadin
"Abbu..."
Cikin yanayin da yasa hankalin kowa ya koma kan Bilal, wannan abin da yake faruwa yanzun ne yasa ba zai bari Rayyan ya dauki wannan laifin ba, ba zai bari su Abbu su fadi maganar da zasuyi dana sani akanta ba kan laifin da baiji ba bai gani ba. Ga kukan da Layla takeyi ya kara daga mishi hankali, shi ya sakata a cikin wannan tashin hankalin, shi ya shiga tsakiyar su ita da Rayyan, abinda bai kamata yayi ba tun daga farko, ko zuciyar shi data doka mata ya dade da sanin bai kamata tayi mishi wannan rashin adalcin ba. Amman cikin watanni kalilan ya fahimci rayuwa bata san wani abu adalci ba, da basu zo inda suke ba yau.
"Ba shi bane Abbu, dan Allah ku saurareni... Layla kiyi magana ke zasu jiki, ki fada musu ba Hamma bane, ki fada musu bashi bane"
Bilal ya karasa yana kallon Layla da kukanta ya tsananta, kai take girgiza mishi, tana rokon shi a zuciyarta da karya karasa datse sauran igiyar da ta rage a tsakaninta da Rayyan din, shima rokonta yakeyi
"Shirun mu ba zai canza komai ba, dan Allah ki saukaka mana, ki fada musu bashi bane ba"
Zaninta Ayya ta tattaro tana goge fuskarta da take jin kamar alamun zufa, saboda yanayin maganar Bilal din bata nuna alamar wasa ko son daukar laifi ba. Abbu ma kallon Bilal yake da sabon tashin hankali, kafin daga kasan makoshin shi yace
"Bilal"
Abbu ya kalla yana riko hannun shi
"Ni ne Abbu, ba Hamma bane ba... Ni ne"
Ya karasa wasu hawaye masu zafi na zubo mishi, komai na jikin Abbu bayason yarda da maganaganun Bilal din, shisa ya kalli Layla duk kuwa da kukan da takeyi tana girgiza mishi kai
"Layla ki mun magana dan Allah, ku fadamun abinda zan iya dauka"
Kuka takeyi kamar zata shide, bata roki Bilal komai ba sai shirun shi, bayan duk abinda ya faru. Ya kawota inda ba zata iya juyawa ba, Abbu da kan shine yake rokon ta, a hankali ta daga mishi kai
"Ba Hamma Rayyan bane"
Ta iya furtawa dakyar tana kwantar da kanta a jikin Mami hadi da sakin wani kuka da ko sautin shi baya fita
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Yaya Ayuba ya furta, ba zaice maganar bata dake shi ba tun daga farko. Amman yanzun jijjiga shi tayi tana dagawa ta buga da kasa. Yasan Bilal, ko a yaran shi babu mai natsuwa da hankalin Bilal, babu mai sanin ya kamatan shi. Ya sha aiken Bilal kan abubuwa masu muhimmanci saboda ya aminta da nutsuwar shi. A mafarki idan aka fada mishi Bilal zaiyi abinda yake cewa da kan shi yayi zai karyata, idan ya tashi kuma zaiyi addu'a harma da sadaka. Abbu ya kasa cewa komai, kan shi yayi wani shiru na ban mamaki. Akan Rayyan ya yarda da zancen Ayya, akwai sakacin shi a ciki, akan Bilal fa? Me zaice? Me zata ce ita ma?
Kallon ta yayi, hargitsi ne bayyane akan fuskarta, yaronta take kallo, Bilal dinta take kallo tana yarda da akwai kaddarar da bata da kalaman misaltawa, yanda yake saka hannu yana share hawayen da sunki daina zubar mishi yana saka nata idanuwan cika da hawaye. Abinda yake damun shi kenan, damuwar da yake ta boye mata a watannin nan kenan ashe, bata taba daukar zata yiwa wani uzuri kan lamari irin haka ba sai yau. A tare da Bilal bata bukatar wani bayani, koma meye ya faru kaddara ce, ko menene ya gifta tsakanin shi da Layla tsautsayi ne.
"Bilal"
Mami da ko kukan ita ta kasayi ta kira, so take ya kalleta dan ta tabbatar da shi dinne, kallon ta yayi, ta kasa tambayar shi, duk da tana son jin bayanin shi kafin ta yanke mishi hukunci, saboda Bilal ne, idan za'a tambayeta shaida akan shi zata fadi cewa duk yanda tasan Ayya tayi kokarin ganin yaran bai kulla alaka da ita ba ya tsallake, baya shakkar dukan da zai sha a hannun Ayya a gabanta yake gaishe da ita, a lokutta da dama ta sha ganin Bilal din ya mata murmushin ban hakuri duk idan Ayya ta sauke mata wata masifar da bata san dalilinta ba. Da yayi hankali har daki yakan bita yana fadin
"Dan Allah Mami kiyi hakuri, karki sa abin a ranki. Ayya bata nufin duka abinda ta fada, kinsan idan ranta ya baci"
Ba dan Abbu ba, saboda Bilal ma ta sha kauda kai kan abubuwa da yawa da Ayya zatayi mata. Shisa take son jin bayani daga bakin shi, take son sanin me ya faru, sai dai kafin yayi magana Ayya ta riga shi
"Karku dora mishi laifi, dan Allah kar kuce wani abu, kuskure ne, Bilal ka fada musu kuskure ne, ni nasan kuskure ne, in dai da gaske ne kuskure ne"