← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 93

Sashe 3

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kishin da yake cinta ne yasa ta zabi daga musu hankali daga ita harshi ko zai kara saka tai gabala akan shi ya fasa auren nan, amman kullum nuna mata yakeyi asirin da su Maryama sukayi mishi mai karfine dan bazai taba iya fasa aurenta ba. Yanzun ma kallon shi take yanda yake yabonta kamar ita kadai din ta ishe shi, harya karasa cin abincin yanayin hamdala

"Sannun ki da kokari, Allah yai miki albarka"

Ahmadi ya karasa yana mikewa ya tattara kwanukan ya fita dasu dan ya taimaka mata, duk idan ta wuce da turtsetsen ciki haka, koya dawo yaga gidan qwal saiya kara jinjinawa mata, ko a tunani ya hasaso kanshi da cikin jikinta sai ya hango yanda zai wuni shame-shame a kwance, amman ita harda kokarin girki, ko da tana laulayi sai yayi da gaske take kinyin girki, koyane saita lallaba ta dafa mishi abinda zaici. Shisa darajarta a zuciyar shi mai girma ce. Ganin da yayi magriba ta karato ya saka shi daura alwala kafin ya karasa dakin yana fadin

"Bari in fita masallaci...."

Batace mishi kanzil ba, sosai yake kewar hirarrakin su da yanda halin ko in kula din da take nuna mishi yake ci mai tuwo a kwarya. Haka yasa kai ya fice daga gidan. Ko da sukai sallar Magriba nan suka tsaya da wasu cikin unguwa danjin labarin Makka daga sabon Alhajin daya dawo satin daya fita wato Sambo. Da yake Ahmadi ba ma'abocin zaman majalissa bane ba, tunda Alhaji Sambo ya dawo basu hadu ba sai yau, yakan tsaya a lokutta irin haka a gaggaisa dan karamcin mutanen unguwar ba karami bane ba. Haka Alhaji Sambo ya dinga nishadantar dasu da labarai kayatattu yana kwadaita musu zuwa aikin Hajji duk idan halin hakan ya samu.

Kiran sallar Isha'i ya tarwatsa taron nasu, inda ana idarwa kai tsaye Ahmadi gida ya wuce, yana shiga soron ya mayar da gidan ya rufe sanin ba bako zasu karayi ba, inma sunyin a kwankwasa yaje ya bude. Jin shirun gidan ya tabbatar mishi da yaran sunyi bacci, da ya shiga daki kuwa Maimuna kadai ya samu, yasan harta kaisu dakin da suke kwana ta kwantar, baisan kuka takeyi ba saida ya zauna gefenta

"Subhanallahi.... Maimuna? Lafiya? Me ya faru? Ko jikinne?"

Ahmadi yake tambaya hankali a tashe yana riko hannunta, kai take girgiza ma duk tambayoyin shi alamar a'a kafin tace

"Me yasa ba zaka rayu dani kadai ba? Me kakw tunanin Maryama zata iya baka wanda ni ba zan iya ba? Ka fadamun dan Allah kagani, Wallahi Ahmadi zan maka komai. Karka tonamun asiri ka hadani da wata...."

Kallonta yake yanda kwanaki basu wuce sittin ba suka rage a daura auren shi da Maryama, har a sujjadar shi addu'ar kwanciyar hankali da dangana yakewa Maimuna saboda kishinta ya fara bashi tsoro, sake rike hannunta yayi, cikin taushin murya ya fara magana

"Da wanne yare zan fahimtar dake ba zan kara aure bane dan in wulakantaki? Maimuna baki yarda da kalar kulawar da nake miki bane ba? Shin a duk rana bana nuna miki yanda kike da muhimmanci a wajena? Ba zai canza ba dan na kara aure"

Wasu hawayen ne suka kara zubo mata saboda yaki fahimtar tsoronta, yaki gane ba soyayyar shi bace bata yarda da ita ba, soyayyar ce batason rabawa da kowa, tsoro take kar auren nashi ya zama sanadin da za'a rabata dashi gabaki daya

"In dai ba wahayin auren nan akayi maka ba dan girman Allah, dan datajar Ma'aiki da iyayen mu kayi hakuri"

Hannunta ya saki, duk hakurin da yake a kanta ya fara gajiyawa, tanayi kamar bata taba ganin an kara aure ba, kiriri kiriri take nuna kamar haramci yake son aikatawa ba abinda musulunci ya yarje mishi ba

"Maimuna kinga gara ki kwantar da hankalinki ko zamu samu zaman lafiya tunda auren nan ba fasawa zanyi ba"

Hawayenta ta share tana saka idanuwanta cikin nashi

"Tunda an shanyeka daman ya zaka iya fasa aure?"

Rai a bace yake kallon ta shima

"Wacce irin maganace wannan? Ba zaki daina baiwa sh Gwaggo damar darsa miki wasu zantuka marassa kan gado a rai ba ko?"

Kada kai Maimuna tayi cikin zafin rai

"Babu wasu maganganu da ake darsa mun a rai sai gaskiya. Yanzun daga ina kake tunda ka fita? Adalcinne kake son gwadawa bayan tun safe ka fice daga gidan nan, dan lokacin naka da zan samu ma tun kafin ka aurota sai ka raba mana tare"

Kai Ahmadi ya dafe yana rasa ta inda zai fara shawo kan wannan al'amarin

"Idan nace miki ba wajen Maryama naje ba zaki yarda?"

Yanda take kallon shi ya sakashi dorawa da

"Tunda nai maganar kara aure kike neman laifina a duk wani abu da zanyi, karyatani kike ko gaskiyata na fada miki. Halayen nan babu inda zasu kaiki Maimuna, karki rage kimarki a idanuwana wallahi"

Yanda ya karasa maganar yasa wani abu tsinkewa a cikinta, da gaske an asirce mata Ahmadi, in har da bakin shi yake furta hango raguwar kimarta a idanuwan shi an asirce shi

"Ashe kimata zata iya raguwa a idanuwan ka? Kaga dalilina na gudun aurenka ko? Kaga abinsa suke sa kana fadamun tun kafin ta shigo, wanne irin wulakanci zan gani kenan nan gaba?"

Take maganar tana wani irin kuka da yakeji har ranshi shisa ya mike saboda bayason biye mata, bayason bata mata rai fiye da yanda yake a bace ko dan cikin jikinta. Kuma da a karo na farko ya zanta sirrin gidan shi da babban abokin shi Nasiru saboda tsoron kalar kishin Maimuna daya gani shawara ya bashi mai kyau, kalaman Nasiru sun zauna mishi sosai

"Su mata ba'a biye musu, hakuri ake da halin su saboda wasu lokuttan kamar yara haka suke da karancin tunani. Laifine kayi mata da kara aure dole kuma tayi kishi, na kula shi kishin nan ya bambanta a tsakanin mata, kowacce da kalar nata. Kayi hakuri da duk wannan tashin hankalin da takeyi, da anyi auren zata hakura. Gani take kamar intaci gaba da daga maka hankali zaka hakura ka fasa. Kai dai karka biyeta, in ranka ya baci kabar mata gidan saika huce ka koma gudun biyewa zugar shaidan"

Aikam shawarar Nasiru ta mishi amfani wajen kaucewa rikicin rashin dalili da Maimuna kan takale shi da shi. Yanzun ma dakin yaran yaje yana samun tabarma ya shimfida kusa da yar katifar su da suke bacci a kai ya kwanta. Yasan halin Maimunar shi, duk fadan da zasuyi bata iya bacci ba'a kusa dashi ba, da almatsutsan kishin nata sun sauka da kanta zata zo ta neme shi. Dan haka ya lumshe idanuwan shi yana musu addu'ar tabbatar alkhairi a wannan auren da zaiyi da kuma zaman lafiya bayan yin shi.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:05 PM - 111: Nov 1, 2020

2

May 1985, Kano.

Da gaskiyar iyaye da kance kukan yaro yafi komai daga hankali, har kasan ranta take jin kukan Rayyan, a gaggauce ta karasa wankan, sabonta ne sai ta saka hijabi idan ta daura zani sannan take fitowa daga wanka, kamar yanda takan shiga da ita. Amman yanzun kam haka ta fito, hijabin ma a bandakin ta baro ta. Ganin ta lallaba Rayyan din yayi bacci shisa ta lallaba tadan watsa ruwan ta fito, ashe ba nisa baccin yayi ba. Tana daga labulen gabanta nayin wata irin mummunar faduwa ganin Maryama data mika hannu tana shirin daukar Rayyan

"Me kike kokarin shafa mishi?"

Ta furta tana karasawa da sauri ta hankade Maryama da take tsaye. Sallar la'asar ta idar, tana zaune tana jan casbi kamar yanda takan wuni tanayi, ko karanta wani littafin da take tunanin zai amfani rayuwarta tunda ta shigo gidan. Da yake da ta gama firamare tayi makarantar kwana har aji uku, da maganar auren su da Ahmadi a kanta ma ta karasa aji ukkun. Bata tsammaci tarbar kwarai a wajen Maimuna ba, amman tayi mamakin kalar kiyayyar da take nuna mata kamar itace mace ta farko data fara shiga gidan aure a matsayin mace ta biyu. Ba zata manta ranar da aka shiga da ita dakin Maimuna watanni ukku da suka shige dan karrama Maimuna a matsayinta na uwargida kamar yanda tsarin al'ada yake.

Sam bata ga fuskar Maimuna ba tunda kanta a rufe yake kasancewarta amarya. Kalaman Iya Asabe da take fadin

"Wanda duk yake a dakin nan yasan halin da kike ciki, dan kishiyar nan anyi mana, wasun mu fiye da daya. Sai anyi hakuri, ko da babu tsira mai nisa tsakanin ki da Maryama kanwa ce a wajenki a gidan aure. Saboda haka ga amanar ta..."

Iya Asabe bata karasa maganarta ba Maimunar ta katse ta da fadin

"Iya ki takaita kalamanki, indai amanar Maryama ce ban dauka ba, karku doramun nauyin da ba zan sauke ba..."

Daga inda Maryama take zaune tana jin salallamin da duk wanda yake cikin dakin yakeyi cike da mamaki

"Inda amana ba zaku rako Maryama dakina ba wallahi, ba zaku dauketa ku liqawa Ahmadi ba..."

Ba zata manta yanda taji takun tafiya ana barin dakin daya baya daya ba. Har Iya ta kamata suka fice saboda yanda Maimuna sam taki sauraren nasihar da Iya taso tayi mata, tana barinta da furta

"Allah ya saukaka"

Kafin su fita daga dakin. Maimuna bata canza kalamanta ba ko bayan da Ahmadi ya hadasu da sunan yi musu nasiha

"Ka dauki matarka ku fitar mun daga daki Ahmadi, ku fita ba sai kun haskamun yanda zaku kasance da juna tsayin daren yau ba, wallahi hakurina yana gab da karewa..."

Maimunar ta karasa maganar da rawar Murya alamar kukan da take kokarin tarbewa. Ita kam zatace firgicin da ta tsinci kanta ya girmi wanda kowacce mace take tare dashi a darenta na farko. Daga ranar kuwa har yau babu wata magana ta arziqi data hadata da Maimuna, banda mugayen kallo da takan watsa mata duk idan ta wuce, tana jin labaran kishi, amman na Maimuna daban ne, ga yan uwanta da taga alama wajen zaman jegon Rayyan suna tayata.

Ba tsoron biye rigimar da Maimuna takan takaleta da ita a duk rana takeyi ba, kalaman Ahmadi ne suke tausarta
Chapter 3 · 0% Book details