← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 93

Sashe 75

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da tarin burin da take da shi na auren Rayyan bai ruguje ba. Da bata ga tsanarta a cikin idanuwan shi ba. Abbu ya kara hargitsata da furucin shi, saboda idan duniya duka zata hade da ita a waje daya bata hango yanda zata fara zaman aure da Bilal ba. Ko na minti daya zuciyarta bata taba doka mishi ta wannan fannin ba, yanda zata fara kwanciya ta tashi da shi karkashin inuwar aure da sanin ya rabata da komai da take takama da shi, banda Martabar ta harda Rayyan, harda Hamman ta. Ba laifi take kokarin dora mishi ba, amman zata iya farawa idan suka kasance inuwa daya.

Tashin hankali ne shimfide take hangoma rayuwarta da ta birkice cikin kankanin lokaci. Da tunani kala-kala a ranta har gari ya waye, da tayi alwalar asuba ma sai da ta koma ta dan kwanta saboda sanyin da ta dinga ji da yake akwai zazzabi a jikinta. Ta samu bacci ne ba jimawa, dan ji tayi kamar tana bude idanuwanta ta mayar da su ta rufe ne taji kamar an fasa kuka, yanayin da ya sakata bude idanuwa babu shiri, ba kuma karya kunnuwanta sukayi mata ba, kuka ne, dakyar ta iya saukowa daga kan gadon, da yake window din dakinta ta wajen harabar motocin gidan ne, zagayawa tayi ta leka ta hango kusan kowa na gidan a wajen. Kafin kunnuwanta su tsinto mata

"Bilal ya rasu"

Cikin muryar da bata san ko waye bama, bangon wajen ta dafa tana runtsa idanuwanta, duniyar na wulwula mata kafin wani abu ya tsirga mata a ciki yana saka bayanta amsawa. Babu shiri ta durkusa saboda azabar da ta dirar mata ga kidimar mutuwar Bilal da take mata kamar almara, sunan Allah duk wanda yazo bakinta shi take kira, tana dafe cikinta da kamar ana tsinka wani abu a ciki, kafin wasu irin hawaye kamar an kwance wani abu a cikinta su fara zubo mata. Sai a cikin kwanakin mutuwar washegari ta fara jero neman gafarar Allah saboda sabon da tasan ta dinga yi na yanda za'ayi Bilal ya rasu.

Kafin wani matsanancin tsoro ya tsirga mata na yanda zai fara amsa tambayoyin shi a kabari, tunanin ko abinda ya gifta a tsakanin su zai rushe tarin ayyukan shi. Ranar bata iya runtsawa ba, gani take kamar da ta rufe idanuwanta itama mutuwa zatayi gaba da ita. Kuma tana jin daudar da take da ita tafi ta Bilal, duk laifukan shi ba zasu wuce abinda ya gifta a tsakanin su ba. Amman ita kam duk wani karami da babban laifi haka ya dinga gifta mata a rai yana kara hautsina mata lissafi.

A cikin sujjadar duk sallolin ta na farilla a kwanakin nan yafiya take rokawa Bilal, ko da basu da bayanin da zasuyi akan abinda ya faru, zunubin dayane dana wanda suke da bayanin yi. Amman Allah Mai Rahma ne, tana kuma da yakini mai girma akan hakan. Yau kwana biyar, amman ko motsi taji sai ta dauka shine zai shigo, sai taji kamar wani ne a cikin gidan ya zo ya karyata labarin mutuwar. Zuciyarta tayi wani irin nauyi na ban mamaki, ga zazzabin da take kwana tana yini da shi. Yau ne ma ta balli Panadol ta sha.

Ita kadai take kukanta, Mami bata mata magana balle tasa ran zata lallasheta, ko ta gaisheta sama-sama take amsata. Haka zata sha kukanta ta kuma bama kanta hakuri, ta daina kokarin kiran Rayyan tunda baya dagawa, ta dai fada mishi duk wani abu da yazo kanta ta text. Tun tana duba wayarta ko zai amsa harta daina ma. Wani irin kadaici take fama da shi na ban mamaki, sai dai inta rage volume din wayarta sai ta saka karatun Qur'ani, takan ji nauyin da kirjinta yayi mata yayi sauki lokutta da dama, ko yau da ta tashi ta gwada shiga wajen hotunan wayarta ta ga na Bilal, amman yanda zuciyarta take dokawa sai ta kasa.

Sai dai rashin ganin hoton bai rage mata zafin rashin Bilal ba, bai kuma hana mata ganin shi a cikin idanuwanta ba, ko suna rufe ko suna bude. Yanzun ma hannunta ta dora saman cikinta tana shafawa a hankali. Tudun shi na tabbatar mata da yana nan, da dane yake girma a cikinta, abinda har yanzun ya kasa samun wajen zama a kwakwalwarta. Gyara kwanciyar ta tayi, tana jin hawayen da ta saba dasu yanzun suna silalowa ta gefen idanuwanta zuwa kan filon da take kwance a kai. Akwai tarin abubuwa da har yanzun basu gama zauna mata ba, taji ciwon su harta san yanda zata fara jinyar ciwukan balle kuma ta fara hango ranar warkewar su.

Tunanin Rayyan ne ya kara dirar mata, yana saka hawayenta cigaba da gudu. Rayyan da ya samu dakyar ya raba jikin shi da gado ya fito yana nufar bangaren Ayya dan ya dauko ruwa, babu wanda yayiwa magana ya wuce Kitchen ya dauki ruwan ya sake ficewa. Ayya ma da take zaune kan kujera bin shi tayi da kallo. Rukayya take ce mata ruwan saura leda biyu ajiye a kasa, na cikin fridge din kuma wasu duk sunyi kankara, batama iya amsa Rukayya ba, wayarta da take gefe ta janyo da nufin ta kira Bilal tace mishi ya kira yan gidan ruwan kai tsaye yaji idan zasu shigo yau suna so. Da yake nan makotan su ta gefe matar na siyar da ruwa, zobo da kunan Aya.

Harta dauki wayar ta cire daga key zuciyarta tayi wata irin dokawa, komai na dawo mata. Tana tunanin yanda zata fara rayuwa babu Bilal a ciki, babu yaronta. Saboda bata hango ranar da komai zai dawo mata dai-dai ba. A rayuwar ta gabaki daya ko a mugun mafarki batayi hasashen daya daga cikin yaranta zasu barta ba, duk yanda takan hango rayuwa mai karewa ce, ita take ganin zata mutu tabar su, kamar yanda nata iyayen suka mutu suka barta. Sai dai mutuwa ba zabe takeyi ba, lokaci me kawai abinda take dubawa, babu ruwanta da yanda makusantan wanda ta dauka zasu kasance cikin jimami da radadin rashi.

Da mutuwa na duba wannan da tabar mata yaron ta. Yanzun ta dandani zafin rashi na daban, ta san yanda kakeji idan ka rasa danka. Sai dai bakowa bane zai fahimci yanda kakeji idan kayiwa dan da aka fada maka ka rasa batare da kaga gawar shi ba kuka. Saboda bata jin har abada wani bangare na zuciyarta zai aminta da ta rasa Bilal, zataci gaba da kallon kofa, da tsammanin shigowar kowa a matsayin danta, saboda bata ga gawar shi ba, bata kalle shi a shimfide a gabanta ba. Shisa mutuwar shi take mata wahalar dauka.

Jiya ma Abbu sai da ya fara mata wani wa'azi da bata fahimta, tace mishi

"Ahmadi ba ganewa zanyi ba wallahi, ka kyaleni inyi kuka ko zuciyata zatayi mun sauki..."

Kyaleta din yayi kuwa. Yanzun ma hannu ta saka tana goge hawayen da suka tarar mata a gefen idanuwanta. Hakuri ya zame musu dole ta sani, amman yanzun zatayi kuka, zataji ciwo, hakurin zai biyo bayan su. Wayar da ta ajiye ce ta dauki ruri, ta dan kalleta, ganin Hajiya Dije rubuce a jiki ya sakata daukar wayar, cikin sanyin murya tayi mata sallamar da ko amsawa batayi ba

"Ya karin hakuri Maimuna?"

Numfashi Ayya ta sauke, kiran na tuna mata da sau daya Hajiya Dije din tazo mata gaisuwa. Abin na kara bata mamaki duk kusancin su.

"Alhamdulillah"

Ayya ta sake amsawa har lokacin muryarta a sanyaye

"Ina ta so in shigo dan mu samu mu zauna. Ranar naga ga mutane ga shi kuma rasuwa na tabaki"

Shiru Ayya tayi tana jin Hajiya Dije ta cigaba da fadin

"Wallahi sai kin tashi tsaye sosai. Kinga me nake fada miki ko? Haka ake so a kada miki kan yaran duk su cimma ajalin su. Kudi zaki turo inje miki wajen Sharu dana samo kwanaki"

Dan dafe kai Ayya tayi, tana mamakin hali irin na Hajiya Dije da yanda akayi bata ga kuskuren da yake tare da duka shawarwarin da take bata a baya ba. Danta ya mutu ba zata ko barta taji da abinda yake damunta ba, tana son nuna mata cewa mutuwar Bilal din ma ba daga Allah bane ba. Bata ce babu sihiri ba, amman duk abinta tasan abubuwa da yawa daga Allah ne. Da Malaman na da amfani da sun hana ma Mami aure mata miji, sun taimaka mata ta fitar da ita daga gidan. Amman da yake abin duk bigene ga Mami nan zaune daram a cikin. Ita da suna wani aiki duk bugun kasar da sukayi mata da sun hango mata kaddarar Layla da Bilal.

"Ba wannan bane a gabana Hajiya Dije. Banda duk wannan lokacin yanzun"

Ayya ta furta wani abu na tokare mata makoshi

"Bangane baki da wannan lokacin ba? Kar dai an saka miki shashatau ni Dije..."

Dan karamin tsaki Ayya taja a cikin ranta

"Wai ke babu wani abu da zai faru da ba asiri bane ba? Idan ma shine na bar mutum da Allah. Dan Allah ki kyaleni inji da abu daya"

Bata ma jira Hajiya Dije ta amsata ba ta katse kiran. Tana jan tsaki a fili, kawai sai taji ranta na baci da abinda Hajiya Dijen tayi mata. A lokaci daya hawaye masu zafi na zubo mata. Bilal da zai mata hirar shi sai ya ga tayi dariya ma baya nan. Mikewa tayi ta shige daki, ta dan fito ne ko zata sami saukin abinda take ji daman.

*

Ruwan ya ajiye a gefe, tun jiya da dare ya kare mishi. Haka ya dinga juyi a gado, ya tashi yaje ya dauko abin na mishi wani iri. Guda daya ya fasa ledar ya dauka, anan tsayen ya shanye, yana jin muryar Bilal kamar yana dakin

"Ba kyau shan ruwa a tsaye, ka samu waje ka zauna, ka juye a kofi"
Chapter 75 · 0% Book details