← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 93

Sashe 28

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shine maganarta da wani irin sanyin murya daya taba shi. Layla tayi murna kamar zata goya Abbu. Neman hutun kwana daya yayi a wajen aiki da lokacin jarabawar nata yazo, da kanshi ya dauketa suka tafi har garin Zaria, kwana daya sukayi ta zana jarabawar suka dawo. Ya fadawa Ayya zaije Zaria, dalilin ne bai sanar da ita ba, saboda bai jima da sukayi rikici akan karar Rayyan da Layla ba, idan taji zataje Zaria karatu wani sabon tashin hankalin da bai shirya ba za'ayi a gidan.

Cikin ikon Allah Layla ta ci jarabawar inda ta sami gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello. Ba ta da kalaman da zata dora farin cikinta a kai ranar, Abbu da kanshi yaje Zaria ya amso mata admission letter dinta, kuma a hankali ita da Mami suke shirin tafiyar tata, tana kokarin ganin duka ranakun batayi wani abu da zai bata ran Mamin ba, kananun kaya ma ta daga musu, dogayen riguna take ta fama dasu.

Abbu kuwa aikawa yayi aka kira mishi Bilal ranar daya amso admission letter din Layla. Yana shigowa bayan sun gaisa ya zauna, Abbu ya mika mishi takardar, amsa Bilal yayi yana dubawa, duk kuwa da Layla ta fada mishi, yayi mata murna sosai da sosai

"Nagani Abbu, ta fadamun..."

Dan lokacin da ta gaya mishi inda ta cika a jamb dinta ta dora da

"Babu wanda na fadawa fa, kai kadaj na gayawa"

Cikin idanuwa ya kalleta

"Me yasa?"

Ya tambaya cikin son sani, dan daga mishi kafadu tayi, kawai saboda shi dinne, saboda tasan zai goyi bayanta, zai tayata son abinda take so, zai karfafa mata gwiwa

"Saboda kawai kaine"

Ta karasa maganar tana saka shi furta

"Hmmm"

Cikin rashin sanin abinda ya kamata yace, lokutta irin haka sai ta saka yaji kamar yana da wani muhimmanci mai girma a rayuwarta. Sai ya ganta tare da Rayyan take karyata mishi hakan. Sai da Abbu ya gyara murya tukunna yace

"Layla kanwa ce a wajen ka, ko bance ka kula da ita ba zakayi. Amman ina so da bakina in roki alfarmar nan, Bilal ka kula da ita, dan Allah ka kula da ita, kudin amana ne a wajena, akan Layla ina so in raba amanar da kai"

Wani irin nauyi Bilal yaji kalaman Abbu sunyi mishi, nauyi sosai

"Ka kula da ita kamar yanda kake tunanin zan kula da ita, a zaman da zatayi a Zaria ka kareta daga dukkan abinda zaka iya kamar yanda kake tunanin ina kare ku, alfarma ce nake nema a wajen ka"

Wannan karin dakyar Bilal yake fitar da numfashi saboda nauyin da kalaman Abbu sukayi mishi, abinda yake roko a wajen shi abune mai girma, amana yake bashi, ya kuma san daraja da hukunci hakan a matakin addini

"In shaa Allah Abbu zanyi kokari"

Ya furta muryar shi can kasan makoshi, kai kawai Abbu ya jinjina, dakyar Bilal din ya iya tashi dan duk gabban jikin shi a sanyaye yake jinsu, har yakai kofa Abbu yace

"Bilal..."

Juyowa yayi

"Ka kula da Rayyan, ka kula da Hamman ka"

Ya karashe maganar cike da roko a idanuwan shi, bai taba cewa Bilal din ya kula da Rayyan ba, saboda yana ganin yanda yake wannan kokarin a duk rana, ya kuma sha jin Ayya nawa Bilal din wannan rokon, yau din Abbu wani irin rauni yake ji naban mamaki, shisa kalaman suka subuce mishi, kai kawai Bilal ya iya daga mishi, da nauyin zuciya ya fice daga dakin Abbu yana nufar bangaren su, inda ya hango Layla ta dora hannunta akan kafadar Rayyan da alama akwai abinda take fada mishi, tureta yayi yana fadin kalaman da Bilal baiji ba, yana kallo Layla ta juya, Rayyan din na kamo hannunta ya dawo da ita.

Lumshe idanuwan shi yayi zuciyar shi na wani irin dokawa, ta ina zai fara? Wanne alkawari ne ya dauka mai girma haka? Ya daukar wa Abbu alkawarin zai kula da Layla kamar yanda Abbun zai kula da ita, idan tana matsayin yar shi, idan tana matsayin kanwar shi bayason tana rungumar namijin da ba muharraminta ba kamar hakan ba komai bane ba, bayason ta kusa da Rayyan, Abbu yace ya kareta daga dukkan abinda zai iya. Abbu ya kara da fadin ya kula da Rayyan, akwai tarin ma'anoni da yake tattare da kalmar "kulawa"

Ta ina zai fara kare Layla daga dukkan abinda zai iya?
Ta ina zai fara idan abin farko da yake son kareta daga shi Rayyan ne?
Ta ina zai fara kula da Rayyan idan bai hana shi daukar ma kan shi zunuban da suke tattare da wannan rungume-rungumen da sukeyi ba?
Ta ina zai fara hana shi abinda ya shafi Layla?
Ta ina zai fara kula da su idan matakin farko ya hada da rabasu da junan su?

Kaddarar su mai girma ce
Kaddarar su ta fara tun kafin sanin su.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 23, 2020

11

Kallon Abbu takeyi, bakin shi motsi yakeyi, da alama magana yakeyi, sautin maganar tashi ce bata karasawa kunnuwanta. Sosai take kallon shi tana kokarin fahimtar sauran zantukan da yakeyi tunda ta daina ganewa daga

"....Tare da Layla zasu koma Zaria, itama ta sami gurbin karatu acan..."

Duk abinda ya fada kafin wannan kalaman batajin suna da wani muhimmanci a wajenta, abinda yake fada bayansu kuwa bata ma ji ba sam-sam. Ko bayan nashi bakin ya daina motsi, ta bude nata yafi sau biyar tana rufewa cikin rashin sanin abinda ya kamata ta fadi. Tashin hankali take ciki, irin wanda bata taba hangowa ba, a gaban idanuwanta abinda take tunani ba matsala bane yake zame mata katuwar matsala.

Wanne irin Malami ne wannan mai zafi Mami take da shi, zuwa yanzun Ayya zata iya rantsewa duk wani sirri nata a hannun Mami yake. In ba haka ba, babu yanda za'ayi data like wata kofar sai Mami ta sake huda mata wata. Duka yaushe ta samu kan Rayyan din haka, yaushe ta samu harya dauki waya ya kirata. Wannan zuwan ne har sau biyu da kan shi ya sameta yana gaisheta. Kuma ita da idanuwanta bata ganshi tare da Layla ba, har wani bacci takeyi mai cike da natsuwa a tsayin hutun nan da su Rayyan din sukayi.

Saboda tana ganin duk kudadenta da ta bawa Malam basu tashi a banza ba, aiki yaci. Ashe tana bacci Mami nacan tana wargaza mata abinda ta kashe maqudan kudi wajen ganin ta kulla. Ta rasa kalar bala'in nan, ta kuma rasa yanda zatayi da karan tsaye da Mami tayi mata a makoshi.

"Layla naji kace zataje Zaria... Ahmadi Layla..."

Cewar Ayya tana kallon shi kamar wadda bata cikin hayyacinta, wannan rikicin da yake gani cikin idanuwanta shi yake gudu yasa bai fada mata maganar tafiyar Layla Zaria ba. Wani zaiyi tunanin yana tsoron rikicin Ayya ne, kuma ba haka bane ba, yana gudun abinda zai bata mata rai sosai da sosai. Saboda yasan matar shi, kusan tare da juna suka mallaki hankalin su, babu kalar rikici da shirmen ta da baigani ba tun kuruciya. Ta rigada ta sakama kanta tunanin cewa Mami na bibiyarta, abinda duk zai fada mata kuwa ba sauraren shi zatayi ba, ya sani.

In ba ranar da Allah ya nuna mata tagani da idanuwanta cewa Mami bata bibiyarta ba, ba zata taba cire wannan tunanin daga ranta ba. Shisa ya kasa samun kwarin gwiwar fada mata Layla zataje Zaria. Yasan tunanin farko da zata fara bana cewa Layla da kanta ta zabi Zaria bane, sam Ayya ba zatayi wannan tunanin ba, idan yace mata bada son ran Mami za'ayi tafiyar ba zai ja musu wata matsalar, kishin shi zaisa ta dauka yana kokarin goyon bayan Mami ne, yanzun dole ya nuna mata yana tare da ita dari bisa dari ko dan a samu zaman lafiya

"Eh, ta samu gurbin karatu a can, tana son karantar bangaren yaren turanci"

Abbu yai maganar cikin taushin murya, kallon shin dai Ayya takeyi, kafin wata dariyar ta kwace mata

"Idan dole ya zame mata sai tabar gari zatayi karatu, duk garuruwan da suke cikin Najeriya sai Zaria? Kuma kana kallo kabarta? Me yasa sai Zaria idan ba Rayyan take son tabi can din ba. Na rokeka, Ahmadi na rokeka daka raba Maryama da yarana, na kara rokon ka daka ja nata kunne ta kyalemun ahalina amman kayi biris dani"

Ayya take fadi tana haki saboda bacin rai

"Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Maimuna"

Wani irin kallo ta watsa mishi

"Gayamun kake in kwantar da hankalina? Ka damu da kwanciyar hankalin nawa ne? Ka damu dashi? Da ka damu da kwanciyar hankalina da baka bar Layla ta bimun yaro har Zaria ba... Wallahi sam abin nan ba zai yiwu ba..."

Ayya ta karasa muryarta ba karyewa saboda wasu hawayen bakin ciki da taji sun cika mata idanuwa, hannunta Abbu ya kamo cikin sigar lallashi, ta fisge tana mikewa

"Na gaya maka ka ja mata kunne bakayi ba, na fada maka... Karka ga laifina idan zaman lafiya yayi karanci a cikin gidan nan"

Cewar Ayya tana wucewa ta fita daga dakin, yanda ta doko kofar saida Abbu ya runtsa idanuwan shi. Wannan abin shi yake gudu shisa ya zabi yau daren tafiyarsu Rayyan din tukunna ya fada mata. Ko rikici zatayi bayaso tayi a gaban yaran, duk da in dai ana sabawa da rigimar Ayya, to zai iya cewa duk wanda ya ke kwana yana tashi a cikin gidan ya saba. Amman wani lokaci sai tasan yanda tayi ta fada maka maganar da zata zo wuyanka tayi tsaye. Shi jiya ma da yaje wajen Yaya Ayuba yake bashi shawara tunda dai yana da rufin asiri, kuma yana da hali ya kamata ace ya sami yar karamar mota an ba su Bilal, saboda zirga-zirga.
Chapter 28 · 0% Book details