← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 93

Sashe 58

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai saboda ganin Layla ya nutsar da ita, amman akwai wani yanayi da zuciyarta take ciki wanda ta kasa fahimtar shi, watakila yana da alaka da kalar rashin tarbiyar da ta dinga cin karo da shi tunda ta shigo makarantar, yarane kala-kala, wasu matan kallo daya zakayi musu daga fuskar su ka gane yaran hausawa ne kuma musulmi, amman shigarsu tayi hannun riga da wannan, ga shi sai rike juna suke da maza kamar hakan bakomai bane ba, ga gungun dalibai duk an jera an taho tare anata hada kafadu da sunan za'a tafi aji. Addu'ar duk da tazo bakinta yinta takeyi, bataje jami'a ba, tana jin labari kala-kala da yake tattare da jami'a dai.

Amman taga yaran da suka shiga cikinta suka fita kalau, yaran da suka tsallaka kasar ketare sukayo karatun su batare da tarbiyar su ta sami tangarda ba, hakan baya nufin kowa ma zai kasance a haka, idan babu rashin ji kacokan na yaro, akwai mugayen abokai da tasirinsu mai girma ne. Illar jami'a zatayi dai-dai da rashin illarta idan ma illar batayi rinjaye ba kenan.

"Allah ya shirya mana, Allah ya tsare mana"

Shine abinda taita furtawa sanda suke hanya. Kusan har karfe shidda suna garin Zaria. Sosai Mami taso tafiya da Layla, amman taqi

"Nafa ji sauki Mami, kuma mun kusa fara jarabawa mu dawo gida hutu gabaki daya"

Abbu kuma ya goya mata baya da fadin

"Nan da kwana biyu sai mu kara dawowa mu kara duba su"

Zuciyar Mami ta kasa nutsuwa, Ayya ma dakyar Abbu ya rabota da asibitin bayan sunje daukarta. Can ma suka sami Aisha da wata kawarta sun zo duba Bilal din sunyo abinci sun kawo. Abbu najin labarin Aisha a wajen Ayya, amman yaune ya fara ganinta, yarinya ba dai kunya ba, dan dakyar ta gaishe da su, ko sallama batayi ma su Bilal ba suka fice suka tafi. Sai da suka jira ta karbi lambobin abokan Bilal din, tana tunawa Mami da cewa itama zata saka Layla ta tura mata lambar Anisa. Haka suka bar garin Zaria da rashin nutsuwa daban da wanda suka shigo garin da shi.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 17, 2020

22

"Shiru-shiru halina ne Bilal, shisa naka yake mun yawa a kwanakin nan"

Rayyan ya fada mishi, yasan baiyi maganar dan yana jiran amsa ba, ya fadane kawai saboda abinda yake ran shine. In da ya tsammaci amsa ne Bilal din bashi da abin cewa, shiru-shirun da yakeyi ba zabi bane ba, dole ce ta saka mishi. Ya kanji mutane sunyi maganar tsoro, sunyi maganar kwana cikin firgici, yanzun ya gane ma'anonin kalaman su, baccin kirki baya samu sosai. A tsorace yake al'amuran shi, ko kallon shi yaga Rayyan ya cikayi sai yaga kamar yana zargin akwai abu mai girma da yake boye mishi, kamar yana so ya gane cewa yaci amanar shine.

Sanda duk zaiyi waya da Abbu sai zuciyar shi ta doka, muryar Abbu yanzun batayi mishi komai sai kara gigita mishi lissafi. Hirar su da Abbu batayin tsayi, saboda a kagauce yake daya sauke wayar kafin ya fadi abinda baiyi niyya ba. Yana fadama kan shi maganar da Malamai da yawa sukayi a kaine na boye zunubi irin wannan, saboda bayayin komai sai yada rikici da haifar da shakku a zukatan mutane, in dai har ranka zaka tuba saboda Allah, zaka kiyaye sharuddan tuban, to kayi shiru shine mafi alkhairi, Allah ya sirranta zunubinka ne saboda dalilai da dama. Har wa'azin ya lalubo ya saka a wayar shi ko zai saukaka mishi jin nauyin amanar daya ha'inta da yakeyi.

Kwanan shi biyu a asibiti aka sallame shi, duk yanda Rayyan yayi mishi maganar ya huta kafin ya koma makaranta sai ya kasa. In ya zauna baya komai sai tunani, zuwa makarantar na rage mishi tunani, yakan yi kokari sosai wajen mayar da hankalin shi kan lissafin da akeyi. Sai da aka hada sati daya a hakan, kafin ya dauki wayar shi yaga shigowar saqo, ya dauka Aisha ce, dan itace comfort din shi a wannan lokacin, har tausayin damuwar da yakan gani a cikin idanuwanta yakeyi, damuwar da yake da yakinin shine silarta

"Nawan wani abu na damun ka, nasan zaka fada mun inda zaka iya. Amman bana so wallahi, ko menene yake damun ka yana mun ciwo a zuciyata saboda bansan me ya kamata inyi in taimaka maka ba"

Murmushi ya iya yi mata, duk wani abu da zatayi domin shi tana comforting din shine, a lokaci daya kuma tana saka shi jin yanda da duk dakika bai kyauta mata ba itama. Kamar yaci amanar duk tarin kaunar da takeyi mishi. Shisa yake ta wasa da wayar a hannun shi, bai bude ba, jiya ya kasa zuwa ya ganta, ta kira shi da daddare bai daga ba, kuma baibi kiran ba da safiyar ranar, sai ya dauka itace tayi mishi sakon a lokacin, ya fi mintina goma yana tararrabin budewa, sai daya duba yaga sunan Layla sannan wani abu ya tsirga mishi. Tun da akayi abin bai yarda ya sakata a idanuwan shi ba, baisan ta inda zai fara ba.

Jikin shi na rawa ya bude

"Bansan me zance ba Hamma, bansan me zan fada maka ba, har raina ina so in dora laifin komai a kanka ko zan samu sauki, amman na kasa, saboda kana daya daga cikin mazan da suke a rayuwata da nake da tabbacin ba zasu taba cutar dani ba. Har yanzun ina cikin rudani, ban san ko abinda zan fada ya kamata ba, ina so in roke ka, dan Allah karka fada idan kayi niyya, sirrin mu ne mu biyu, kowa zai iya zabar abinda zaiyi da na shi nasani, amman shirun ka shine kariyar karshe da zaka bani. Martabata ce akan layi idan kayi magana, mu manta idan zamu iya, dan Allah ina rokon ka. Ka goge idan ka karanta"

Ya karanta yafi sau goma, yana shirin gogewa ne wani sakon nata ya shigo

"Zamu raba laifin abinda ya faru Hamma, karka dauka duka kai kadai"

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke da baisan daga inda ta fito ba, duk da bata sauke nauyin da yake ji a kirjin shi ba, ta bude wasu hanyoyi da suka toshe mishi. Ya kasa bata amsa daga lokacin har zuwa yanzun, ya dai goge sakonnin kamar yanda ta bukata. Bashida kwarin gwiwar hada idanuwa da ita, har yanzun idan ya kwanta bai daina addu'ar farkawa ya ga komai ya kasance mafarki ba. Sai dai da duk ranar da zata wuce da yanda gaskiyar komai da ya faru yake kara zauna mishi.

Babu abinda yake kara mishi nauyi sai kallon Rayyan a duk rana, musamman yanda yake ganin damuwa a idanuwan Rayyan din, sosai yake son ya koma dai-dai, ya manta abinda ya faru, amman ta ina zai fara idan yanajin amanar mutanen daya kamata ya roka gafara tana danne shi? Idan yana jin kamar yana yawo da hakkin da zai iya mutuwa da shi rataye a kai a kowanne lokaci? Gabaki daya dan karfin da ya rage mishi ne ya tattara akan karatun shi ko zai sami sauki. Musamman yanzun da aka fara jarabawa, sosai karatun yake zamar mishi wata hanyar da zaiyi amfani da ita wajen kaucewa wasu tunane-tunane.

Yau dai tazo mishi daban, bashi da jarabawa, shisa yace zai kai Rayyan din Kaduna inda aka kaishi don fara bautar kasa. Tunda yake shiri sai ranar take ta dawo mishi da abubuwa da dama, kamar ranar da Rayyan zai tafi Bauchi haka yake jin shi. In da duk yayi nan Rayyan da yake zaune yake bin shi da kallo. Tun suna asibiti yake kula da Bilal din, kamar akwai abinda yake damun shi fiye da jinyar da yakeyi

"Tunanin me kakeyi? Menene? Bilal jinin ka ya hau... Me ka sa a ranka da ban sani ba"

Ya tambaye shi, amman shiru Bilal yayi yana kasa hada idanuwa da shi

"Aisha ce?"

Ya sake tambaya, kai Bilal ya girgiza mishi, ganin kamar a takure yake sai ya kyale shi. Saboda yana ganin bashi da lafiya, bai kamata ya takura shi da yawa ba. Ya yarda da Bilal, ya kuma san halayen shi, idan har ya kamata ya sani zai fada mishi. Sai dai kwanaki sunata tafiya, damuwar Bilal din kuma gani yake tana kara yawa, har makaranta ya shiga yaje department din su Bilal yayi tsaye a bakin ajin su, da yaga ya fito sai da dariya mai sauti ta kwace mishi

"Me nake tunani?"

Ya furta yana girgiza kai, nan ba sakandire bace ko ma yace firamari da zaiyi tunanin ko wani ne yake takurama Bilal din harya shiga damuwa. Amman ya rasa me ya kamata yayi tunani, abin na damun shi. Haka suka jera tare suka koma gida, kowa da tunanin da yakeyi a ran shi. Yana kallon Bilal, kusan shi kan shi a darare yake da Bilal din, ko abinci ya karbo musu wajen Aisha, ko shi Layla ta kira shi yaje ya karba in ya kawo sai ya taba Bilal sau goma kafin su gama ci saboda yanda yake tafiya duniyar tunani, kamar yakan manta cewa yana cin abinci ne sai ya tuna mishi.

Layla ma yana ganin kamar akwai abinda yake damun ta, baya jure kallon idanuwanta ne, a yan lokuttan daya kalla din, a kasa tsoron da suke bashi akwai damuwa shimfide a cikin su, sai yake ganin kamar harda tsoro da wani abu da ya kasa fahimta. Randa yaje ganin ta, sosai zuciyar shi take cike da soyayyar ta, haka yasa shi kai hannu don ya taba fuskarta, ba dan yana son tabata din ba, so yake yaji ko da sauran zazzabi su koma asibiti, amman yanda ta janye jikinta tana kallon shi da wani irin firgici shi kan shi ya tsorata

"Ina so inji ko da zazzabi ne a jikin ki har yanzun"

Ya fadi da sauri, amman zai rantse jikinta bari yakeyi, yaso ya rike ko da hannunta ne ko zata natsu, amman kai take dinga girgiza mishi

"Naji sauki, babu zazzabin Hamma, babu"

Ta furta, kai ya jinjina yana kallon ta, har sai da yaga ta dan nutsu tukunna

"Menene?"
Chapter 58 · 0% Book details