← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 93

Sashe 52

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ta sauke wayar daga kunnenta take cikin tashin hankali, har ciwon kai ya taso mata. Tunda akayi wayar hannu, ko tace tunda Bilal ya mallaki tashi wayar, ko suna gari daya sai yayi mata kira fiye da hudu a rana. Duk a cikin yaranta Bilal ne zai fita fiye da awa biyu ya kirata ya tabbatar mata da cewa yana lafiya, ko da kuwa ya sanar da ita cewa zai wuce awa biyun. Shakuwar da take tsakaninta da yaranta, gabaki dayan su Rayyan ne kawai bata kira a waya, sai ta jima bata kira shi ba saboda ranta kan baci idan bai daga ba, gara ta kira Bilal taki ya yake.

Amman ita ko su Rukayya sukaje makaranta tana iya musu kira goma-goma kafin su dawo. Ko muryoyin su taji sun sauya sai ta gane. Shisa tun da safe da bataji Bilal ba ta kasa samun natsuwa, ko da yana lakca zai mata text ya fada mata, yana kuma fitowa zai kirata. Ko Abbu bata waya dashi yanda takeyi da Bilal, wani sim Bilal din ya siyo musu ya bata guda daya, duk wata yake tura mata kudi sai su dauke, haka zasuyita labari ba kama hannun yaro. Kwanaki Khalifa daya sameta sunata waya bayan sun gama yake cewa

"Hajiya Ayya da Danta"

Dariya tayi

"Ko katin ku ma bakwaji, ni da nake saka katin ma ba'a kirana haka"

Dariyar ta sakeyi sosai

"To dan ubanka kafin ka samun kati sau daya mijina ya sakamun sau hamsin... Kuma wannan layin Bilal ne ya siyo mana shi, ba'a daukar kudi, duk wata ake saka ko dari shida ne"

Khalifa yayi dariyar, takan ga mamaki a fuskar yaran nata kan kalar shakuwar da take tsakanin ta da Bilal, har tsoro takan ji wata rana kar abin ya darsa kishin Bilal a ransu, amman ko na rana daya bata taba gani ba, suna kaunar shi kamar daga cikinta ya fito, ko dan Bilal dinta haka yake. Da wahala ka zauna da shi baka kaunace shi ba, ko dan yanda zai dinga kaffa-kaffa da bacin ranka, a duk gidan daga shi sai Haris zata yiwa wannan shaidar, dan ko yanzun duk a cikin yaran Maryama babu wanda take ji a ranta kamar Haris.

Shi ka daine yake kiranta kullum su gaisa harma suyi labari, ko yanzun da akayi maganar auren shi da yar wajen Yaya Ayuba, kudi na nan tana warewa da zata bashi gudummuwar ta, so take tayi hidimar auren yaron kamar yanda zatayi ta su Bilal. Yanzun wayarta tabi da kallo da ta sake kiran Bilal amman wannan karin a kashe ma taji wayar tashi, abinda ya kara daga mata hankali matuqa. Ta kara kiran Rayyan har sau hudu bai daga ba, tasan yana Bauchi. Yanzun take tunanin yanda in har Bilal ya daga waya zata saka ya tura mata lambar abokan shi guda uku ko fiye da haka yanda zata kira su duk idan bata same shi ba a duba mata a gani ko lafiya.

Tayi tunanin kiran Abbu, amman bata son daga mishi hankali, gara ta bari ya dawo, tunda ya kai wannan lokacin bai dawo ba tasan wani abin mai muhimmanci ne ya tsayar da shi. Nata hankalin dai yaki kwanciya, ga yaran duk suna gidan Yaya Ayuba, shiru sai ita kadai a falonta. Ta saka wannan ta kwance, sallama taji, sallamar da sai bayan ta amsa sannan muryar ta karasa kwakwalwar ta da wani yanayi da ya sata daga kai ta kalli kofar inda Mami take tsaye a tsorace. A nata bangaren ita tun cikin daren jiya ta farka da faduwar gaba, haka ta karasa daren cikin salloli, to tunda gari ya waye kuma jikinta yake a sanyaye, rabonta da yanayi irin wannan tun rasuwar mahaifiyarta.

Addu'a ta dingayi, sam hankalinta bai kai kan Layla ba sai da tayi mata kira ya kai goma da safe bata daga ba. A yinin ranar in ba wayarta aka duba ba, ko ta Layla babu yanda za'ayi a gane yawan kiran da tayi mata. Har dubawa tayi ko ta ajiye lambar Anisa da Layla ta taba kiranta da ita, tana fada mata dakin su daya da Anisar, amman bata ajiye ba. Kusan duk wata baquwar lamba da ta iya gani a wayar saida tabi ta kira cikin son gano lambar Anisa, amman bata samu nasara ba. Idan ta kira wani cikin yaran tabbas hankalin su zai tashi, shisa ta kira Bilal, shima sau hudu bai daga ba, kuma tasan in dai yagani to zai kirata, haka kawai ta kasa samun natsuwa.

Musamman ba jimawar nan da ta kira Bilal din taji wayar shi a kashe, haka ta Layla. Sosai zargin ko lafiya da takeyi ya tabbata, tasan ba shiri sukeyi da Ayya ba, na rana daya basu taba shiri ba, duk kuwa yanda taso hakan ya faru, amman akwai lokutta da dama da suka ajiye rashin jituwar da yake tsakanin su sukayi maganar fahimta, musamman lokuttan daya kasance ya shafi wani a cikin yaran su. Ko kwanakin baya da Haris ya sami hatsari, Ayya ce kiran shi na karshe, dan haka ita aka kira da wayar shi, bata ma kira Mami ba sai da taje asibitin wajen Haris, sannan tunanin yazo mata, shima Haris ya bata lambar Mami, dan bata taba sanin yanda lambar take ba.

Kuma sai Mamin bataje ba, tabar Ayya da Haris din da yake tace mata ba wasu ciwuka yaji ba, ya bugune harya suma, kuma ya dawo hayyacin shi ana mai dinkine, ana gamawa aka basu magunguna suka tafi gida. Shine karo na farko da Ayya ta dinga jera kwanaki tana shiga bangaren ta tunda can Haris yake wuni, ba kulata takeyi ba, zata duba jikin shine, ta dan zauna suyi hira, da aka kwana hudu ma sai Haris din ya dinga wuni a falon Ayya din. Shisa yau take da yaqinin Ayya zata kulata indai zancen yarane, duk kuwa yanda tasan bata kaunar Layla, duk a cikin gidan ita da Layla ta dauki tsanar duniya ta dora musu.

"Maryama?"

Ayya ta kira cike da alamar tambaya, saboda sai da taji kanta ya kara sarawa, tasan akwai dalili babba da zai shigo da Mami bangaren ta, cikin rawar murya Mami tace

"Bansan ko kinyi magana da su Bilal ba, dan Allah zanji ko Layla tana lafiya ne, tun safe nake kiran wayarta ba'a dagawa, yanzun kuma a rufe, Bilal ma na kira shi bai dauka ba, yanzun da na sake gwadawa shima tashi wayar a kashe..."

Mami ta karashe maganar muryarta na karyewa, cikin tashin hankali Ayya tace

"Nima inata kira ba'a daga din ba, yanzun nake so Abbun su ya shigo... Bana so in kira in daga mishi hankali"

Kai Mami ta jinjina

"Allah ya sa dai lafiya. Na kasa samun natsuwa wallahi..."

Numfashi Ayya ta sauke, sam Mami ba zata gane yanda take ji ba, saboda watakila ita Layla kan yini basuyi magana ba, saboda haka rashin wayar su yau ba abin da zai daga hankali bane ba. Amman tasan ko a cikin yaranta ta fadawa wani duk yau tun safe batayi magana da Bilal ba hankalin su zai tashi, zasu san ba lafiya ba. Suna nan tsaye Rukayya ta karaso ita kanta mamakin ganin Mami tsaye a bakin kofar su tayi

"Mami... Lafiya dai ko?"

Cewar Rukayya, Mami din na matsa mata ta shiga cikin dakin, Ayya ta kalla

"Me yake faruwa?"

Ta sake tambaya gabanta na faduwa

"Babu komai"

Mami da Ayya suka amsa a tare, suna saka Rukayya kallon su cike da rashin yarda

"Me yasa zaku amsani a tare idan babu komai? Me ya faru? Ina Abbu? Abbu bai dawo ba?"

Rukayya tayi maganar da wani irin tashin hankali da yasa Ayya fadin

"Dan ubanki karya zamuyi miki to?"

Idanuwan Rukayya har sun fara tara hawaye, saboda tasan abinda duk zai hada Ayya da Mami waje daya haka, suna tsaye hayaniya bata tashi to mai girmane, kuma tafi kawowa ranta cewa Abbu ne, ganin yanda hankalinta ya tashi shisa Mami tace

"Ke ba wani abu bane bafa, Layla ce ban samu a waya ba tun safe, shine nazo amsar dayar lambar Bilal in kira dan ya duba ta"

Numfashi Rukayya ta sauke wani abu yana natsawa a zuciyarta jin ba Abbu bane ba

"Nima na kira bata daga ba, ta saka hoton wasu takalma jiya sai nayi mata magana tace kawarta take siyarwa, to ina so in tura kudin, na dauka ko tana lakca shisa... Nasan lafiya in shaa Allah... Watakila wayar ta fadi ko ta ajiye wani waje"

Kai Mami ta jinjina, ita sam batayi wannan tunanin na cewa zai iya zamana wayar Layla bace ta fadi, ko aka sace, sai taji ta dan samu natsuwa

"Allah yasa lafiya dai... Sai anjiman ku, zanci gaba da kara gwadawa"

Cewar Mami tana juyawa, har tayi taku biyu Ayya tace

"Maryama..."

Juyowa Mami tayi

"Idan na same su zan aiko Rukayya ta fada miki"

Kai Mami ta jinjina, haka kawai kwalla na cika idanuwanta. Shisa ta kasa cewa komai ta tafi kawai, akwai wani abu a cikin idanuwanta da yasa taba zuciyar Ayya din, tasan yanda tashin hankalin tararrabi akan ko yaronka yana lafiya yake. Shisa ma ta ajiye kishi da tsanar da tayiwa Mami din a gefe yau. Suna nan zaune tana dan amsa Rukayya dai-dai cikin tsegumin malaman makarantar su da kuma rashin mutuncin su da takeyi mata dan ta dan rage damuwa Abbu ya shigo, suna gaisawa da Rukayya ta tashi tana barin dakin, da yake girkin Mami dinne. Ta so yaci abinci tukunna ta fada mishi, amman yasan ta, ya karanci damuwa a fuskarta

"Lafiya dai Maimuna?"

Kai ta girgiza a hankali

"Duk yau tun da safe banyi magana da Bilal ba, inata kiran wayar shi ba'a dauka, sai babu jimawa kuma Rayyan ya kirani yana tambayar ko nayi magana da Bilal din, kaga kenan shima basuyi magana ba..."
Chapter 52 · 0% Book details