← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 93

Sashe 79

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwai banbanci a cikin tarbiyar yaran da suke gabanka ko da suke nakane gabaki daya. Halayen su shine abinda zai banbanta wannan tarbiyar, lokacin da wani yake bukatar tattashi, nasiha da tsantsar kulawa, wani a cikin su, fada harma da duka yake bukata. Kuskure daya a cikin yanayoyin biyu zai iya kwance maka tufka ta bangaren igiyar ka, tsayin igiyar zai sa ka kasa ganin warwarewar tufkar da wuri sai lokaci ya kure maka. Hakan ya faru da ita akan Layla, yanda ta dora tarbiyar sauran yaran itama da shi tayi mata riko, soyayyarta ta rufe mata idanuwa, ta kasa gane cewa tana bukatar riko daban da na sauran.

A wasu lokuttan kuma sai ta sakarma Abbu yanke hukuncin, saboda tana tunanin nashi tunanin yafi nata. Amman kaddarar nan ta nuna mata akwai fanni na tarbiya da iyaye maza suke bukatar taimako a kai, ba wai jayayya akan hukuncin su ba, amman yin kokarin fahimtar dasu kuskuren da yake cikin hukuncin ko da rai zai baci abune da yake da matukar muhimmanci. Sai addu'a, ita ce abu daya da take da karfin sauya kaddara, ta fahimci abubuwa da dama, duk da ta fahimce su a kurarren lokaci, hakan baya nufin ba zasuyi mata amfani ba.

"Mami dan Allah ki taimaka mun"

Layla ta furta cike da bukatar neman dauki, tana sake matsawa jikin Mami, kamar zata koma cikin ta, ta boyewa duk wani tashin hankali da yake cikin kaddarar ta. Sai da Mami ta tabbatar idan tayi magana muryarta ba zatayi rawa ba sannan tace

"Ban tsaneki ba Layla, babu wani abu da zakiyi dan tsane ki, duk da na kasa hana zuciyata tsanar abinda kikayi....nima inajin akwai laifina a cikin hakan. Ba zan miki karya ba, a watannin nan da zasu zo, gabaki daya rayuwar mu babu wani abu da zaizo da sauki..."

Sai da ta numfasa sannan ta cigaba

"Ciki ko karkashin inuwar aure ne ba abu bane mai sauki balle akasin hakan. Rayuwar ki da tamu duka ce tayi sauyi na har abada, Allah Ya san dalilin hakan, shi ya dora mana, zamu karbi kaddarar da hannu biyu mu gode mishi a dukkan yanayi, sai ya taimake mu ya kawo mana saukin da bamuyi zato ba"

Sosai Mami taci gaba da tausasa Layla din, tun tana kuka har tayi luf alamar bacci ya dauketa. Kallonta Mami tayi, akwai darasin da ta kasa koya mata, akwai tarbiyar da kaddara ta gyara mata akan Layla, ta hanyar da ta zame musu darasi gabaki daya. Hawayenta ta sake sharewa a karo na babu adadi

"Allah Ka san yanda zakayi da mu, Allah Ka kawo mana sauki a cikin lamurran mu. Allah mungode maka a cikin kowanne yanayi"

Shine abinda Mami take fadi a zuciyar ta tana maimaita hadi da bin bayan addu'ar da

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Domin samun saukin da yake cikin fadar kalmomin a yayin tashin hankali.

*

Sai da ya bude gaban motar Bappa ya shiga bayan ya jefa jakar shi bayan motar sannan ya maida hankalin shi kan wayar shi yana kiran lambar Abbu daya dauka a bugun farko yana kiran sunan Rayyan din daya amsa ta hanyar yin sallama yana dorawa da

"Abbu ina kwana"

Amsawa Abbu yayi, kafin Rayyan yace

"Na shiga dakin ka naga ka fita. Daman zan kara maka sallama ne, gamu zamu kama hanya ni da Bappa"

Ta dayan bangaren Abbu ya amsa

"Ma shaa Allah. Allah ya tsare muku hanya ya taimaka. Ayita hakuri kaji Rayyan, addu'ar ka wa Bilal tafi tunanin shi yawa"

Muryar Rayyan can kasan makoshi ta fito

"In shaa Allah. Nagode Abbu"

Ya furta kafin sukayi sallama. Bappa da yake tukin shi a hankali ya juya ya kalla

"Kasan wani da yake aiki a First Bank?"

Rayyan ya tambaya, cike da mamaki Bappa ya dan kalli Rayyan kafin ya mayar da hankalin shi kan titi

"Akwai kanwata Habiba, acan take aiki"

Dan numfashi Rayyan ya sauke, tunanin yau kwana biyu yake mishi yawo akai, amman tsoron furtawa yakeyi. Sosai zuciyar shi take bugawa

"Zata iya duba mun bank statement din account haka, sai ta tura maka ka bani?"

Sai da Bappa ya sha round sannan ya amsa Rayyan din

"Ban san ya tsarin su yake ba, mu tsaya bank din mana ka duba... Kana da account da First Bank ne? Na dauka UBA kake amfani da shi"

Girgizawa Bappa kai Rayyan yayi, yana rasa ta inda zai fara fada mishi, saboda a cikin kan shi ma maganar batayi kama da ta mai hankali ba. Amman dole ya tabbatar, zaifi samun nutsuwa idan ya tabbatar, ya san menene depression, idan bai tabbatar ba tunani zai iya zautar da shi, yana bukatar ya tabbatar kafin komai ya zauna mishi harya samu ya koma dai-dai.

"Kar kai mun wa'azi Bappa, kar kai mun wa'azi ina so in tabbatar da wani abune, ina bukatar in tabbatar da wani abu"

Murmushi Bappa yayi

"Banyi alkawarin ba zan maka wa'azi ba"

Dafe fuskar shi Rayyan yayi da hannuwan shi biyu, kafin ya furzar da numfashi yana bude su

"Account din Bilal ne"

Yayi maganar cikin karamar murya

"Rayyan..."

Bappa ya fara, amman kai Rayyan ya girgiza mishi

"Dan Allah Bappa, kar kace mun komai tukunna, idan akwai yiwuwar ta duba mun, ka taimaka mun, ina so in tabbatar, tunanin banga gawar shi ba yana mun wahala, mutuwar Bilal ta kasa zauna mun inda ya kamata ta zauna, kafin ka fara na kalli abin ta fuskar likitanci, ina so in tabbatar"

Numfashi Bappa ya sauke yana dan rage gudun motar kafin ya kalli Rayyan yana sake mayar da hankalin shi kan titi

"Zan kirata, yanzun zan kirata, amman zan fada maka gaskiya ko baka son ji. Ba lallai sai kaga gawar Bilal bane zai zamana ya rasu, akwai dubban mutanen da labarin mutuwar su baizo ma ahalin su ba, amman sun musu zaman makoki... Ka saka kanka a matsayin su, kuma sun hakura, hakurin nan ba zabi bane ba Rayyan, dole ne, na san me kake ji, naga gawar Mama da ta kowa, amman kullum na shiga dakinta sai naga kamar zan ganta..."

Gyaran muryar Bappa yayi kafin yaci gaba da fadin

"Zan maka karya idan nace har yanzun babu wani bangare na zuciyata da bayason tashi da safe yaga komai ya kasance mafarki. Ka yarda dani zaka hakura a hankali, ciwon ba zai taba bari ba, amman zaiyi sauki, zaka koyi zama da shi yau da gobe... Idan duba bank statement din Bilal zai baka yardar da kake nema shikenan"

Tunda ya fara maganar shiru Rayyan yayi yana jin shi, kuma zantukan na zauna mishi, dan sun tokare mishi makoshi har wani daci-daci yake ji a cikin shi, yana ganin Bappa ya sauka daga gefen hanya a hankali yayi parking, sannan ya dauki wayar shi da take ajiye akan cinyar shi yana danne-danne. Sai da ta fara ringing sannan Rayyan yasan kira ne Bappa yayi, kuma ya saka ta a speaker. Har ta kusan yankewa sannan aka daga da sallamar da Bappa ya amsa

"Ya Bappa, ina dan aikine haka..."

Kai Bappa ya jinjina

"Habiba ko zaki dan taimakawa abokina ki duba mishi bank statement din shi, ya yarda wayar shine haka, to sim din da yake ganin alert yana ciki, kafin yaje yayi swapping idan babu matsala, da zamu shigo bankin tare da shi, amman bamu samu dama ba, muna hanyar Kaduna"

Ta dayan bangaren Habiba ta amsa da

"Na dauka sai da yamma zaka wuce ai... Ya fadi account number din na shi da email sai in tura mishi"

Kai Rayyan yake girgizawa Bappa, bayason yin magana kar taci, amman so yake yace a tura ana Bappa

"Wayar ce bai siya ba tukunna, idan babu damuwa ki tura a nawa, barin miki text din account number din da email din"

Wani irin numfashi mai nauyi Rayyan ya sauke jin tace babu matsala. Wayar Bappa ya mika mishi bayan sun gama. Da kan shi ya rubuta account number din Bilal da kuma sunan shi cikakke. Sannan ya mikama Bappa wayar ya saka email din shi yana turama Habiba, ya sake mikawa Rayyan din wayar, ya tayar da motar suna hawa titi sosai. Bappa najin da shi kadai ne zai saka karatu ko waka yanaji, amman shi din mutum ne da yasan hakkin mutane, zai iya tambayar Rayyan din ko zai iya kunnawa, amman yaga baya cikin hankalin shi, saiya hakura.

Shisa yake mamakin mutanen da zasu kasance daki daya da wani, ko a makaranta sai su kunna kida ko karatun Qur'ani ganin duk dakin musulmine batare da tunanin ko wani a ciki baya jin yanayin sauraren wani abu ba. Shisa idan bashi kadai bane yakan zabi yayi amfani da earpiece, to yanzun wayar da zai saka a jiki tana wajen Rayyan da ya tattara hankalin shi kacokan ya mayar kan wayar, lokaci zuwa lokaci yakan dangwala yaga ko sako ya shigo shine bai gani ba. Har suka fita daga cikin garin Kano bai daina dubawa ba, ko da suka shiga inda babu network ma haka, har ya dawo sannan yaga sako ya shigo.

Jikin shi har kyarma yakeyi, da yake yasan lambobin sirrin bude wayar Bappa din, da hanzari ya danna yana budewa, kai tsaye email din ya bude yana dudduba kwanan watan da kudi suka fita, zuciyar shi na wani irin bugawa kamar zata fito ta hau titin da suke tafiya a kai ganin ko jiya an cire dubu daya a account din Bilal din, sai da ya hada kan shi da gaban motar yana wani irin maida numfashi, dariya ce ta kwace mishi a lokaci daya kuma wasu hawaye masu zafi na digowa suka sauka jikin motar, dan ya gansu, kokarin mayar da su yakeyi, jikin shi babu inda baya kyarma.

Yanda zuciyar shi take bugawa ne yasa shi kasa cigaba da duba wayar sai da yaji ta dan nutsu tukunna, a kwanakin bakwai an cire kudi sau hudu, dago kan shi yayi yana kallon Bappa

"An cire kudi, Bilal ya cire kudi Bappa.... Bilal ya cire kudi"
Chapter 79 · 0% Book details