← Book details Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 93

Sashe 61

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman Naadir na zuwa islamiyya har yanzun, idan zaibi abu sau hamsin kafin ya fahimta baya gajiyawa. Yanda ake yaran suna gane Layla ta dawo har mamaki yake bawa Mami, shisa Naadir na fitowa daga kitchen din tace

"Wai ya ake kuna gane ta dawo ko baku ganta ba?"

Dariyar shi Naadir yayi

"Kamshi Mami, kamshin turare"

Dariyar tayi

"Wato ni bana saka turare kuke nufi ko menene?"

Kai Naadir ya girgiza, yana ficewa, Mamin su na kokari matuka wajen tsafta, amman turarukan da Layla take amfani da su daban ne, duk idan ka shigo zakaji su. Su suke fara sanar da kai tana cikin gidan. Sai kuma abinci da manja yawanci, su duka yaran suna so, ita kuma Mami bai dameta ba, kuma ba zata iya wahalar girki kala biyu kamar yanda Laylar takeyi ba, idan miya ce tana iya yiwa Mamin tata daban da babu manja, su kuma tayi musu mai manja. Kuma tana iya binsu a waya tana tambayar me suke marmarin ci, Mami abinda taga damar dafawa shi takeyi, ko Abbu baya mata zaben girki balle su.

Layla ma daga dakinta ta fito dan yunwa ta korota, tunda tayi azahar ta kwanta tana bacci, bata tashi ba sai da la'asar din, jikinta da yayi nauyi yasa ta watsa ruwa bayan ta idar da sallah

"Wai ina kike siyen turaren wutar da kike zuwa da shi? Yafi na nan da mukan siya dadewa a dakuna"

Mami ta tambaya

"Wajen wata Kamshi by Saffad, Anisa ce take zuwa da shi tana saka mana a daki, kamshin yana mun dadi, shine ta bani lambarta duk idan zan dawo nake siyo mana fa, kuma babu tsada Mami"

Layla ta karasa tana shigewa kitchen, sai da ta zuba abinci ta kai daki sannan ta daukowa Mami kwalbar turaren wutar tana dawowa ta kawo mata. 07010137848 Lambar wayar Mami ta duba, Layla kam yunwa takeji shisa ta koma cikin daki abinta, yau da ta tashi ji take a duniya idan bata ci miyar kifi da manja ba komai zai iya faruwa, shisa ta kira Jabir a waya tace ya siyo musu kifi. Da yake yafita kwadayi ko awa daya ba'a hada ba ya shigo dakin da kifi mai yawa, sai da ta saka wani a fridge ma. Abincin take ci tana duba text tsofin texts din su ita da Rayyan, ba sosai suke waya ba tunda ta dawo saboda Mami.

Shisa kusan wuni sukeyi suna musayar text, baya gajiya da saka mata kati ko da tace mishi tana da saura, yi yake kamar baijita ba, ta dai rasa ya zatayi da shi akan waya. Duk idan tayi mishi zancen waya sai yace ta kyale shi, ba zai barnar kudi ba akan waya. Kewar shi na danneta, in da ya siyi babbar waya zata saka shi ya dauko manhajar IMO dan su dinga video call ta nan, ta ga fuskar shi, ko hotunan shi basu kai goma ba wanda take da su, na ranar da ya gama jarabawa, sai kuma ranakun da yazo wajenta ta daga camera bai fisge wayar daga hannunta yana hada mata da rankwashi ba saboda zata dauke shi hoto.

"Ko aljanu sukan rabo a dauki hoto da su wani lokaci Hamma, amman ace kai baka da hotuna saboda Allah"

Ta taba ce mishi, murmushi yayi kawai yana girgiza mata kai, akwai hoton su ita da shi da take so, saboda ranar tayi sa'a ya tsaya sosai, kuma manyan kayane a jikin shi harda hula. Har ranta take jin Rayyan, kamar yanda har a zuciyarta take jin shine cikon farin cikin ta. Abincin ta karasa cinyewa ta dauki plate din ta mayar kitchen ta koma ta kwanta abinta. Idanuwanta take ji suna mata nauyi da alamun bacci, ba dan bata kwanciya ba, amman a yan kwanakin nan sai take ganin kamar baccin da takeyi yayi yawa. Shisa da ta idar da sallar asuba take shiga kitchen tayi abinda zatayi, saboda Mami bata tashin ta, idan tayi aiki shikenan, idan kuma bata fito ba ita zatayi da kanta.

Shekaranjiya wata irin kasala ta dinga ji har cikin kasusuwan ta, shisa ta kasa fita tayi kwanciyar ta, sanda ta tashi karfe goma na safe

"Mami baki tasheni ba, shine kikayi aikin ke kadai"

Murmushi kawai Mamin tayi mata

"Rai na son hutu Layla, kuma motsa jiki na da kyau, tunda kika zo bana wani aikin komai, sai kin shagwabani ki koma makaranta abinki"

Dariya tayi, ko da babu makaranta tasan Mami ba zata tasheta ba. Wayarta da harta fara subucewa daga hannunta saboda bacci ta dago, haka kawai sai idanuwan ta suka sauka kwanan wata, period biyu kenan batayi ba, wannan karin ma har wajen kwana takwas kenan ta kara. Farkon da sukaje makaranta, daga ita har Anisa sun sha wahala saboda infection da suka kwasa na amfani da bandakin makaranta, gara ma ita ciwon mara ya kara mata sai kuma period daya dinga mata wasa, dakyar Anisa ta samu ta sakata taje asibiti

"Ni fa in zan shekara banga period ba zaifi mun, Allah ya kawomun saukin wahala ne"

Har duka Anisa ta kai mata tana fadin

"Ke daman ai baki da hankali"

Amman da gaske takeyi, babu wani ciwo da yake bata wahala banda period, har zullumi takeyi idan taga tsakiyar wata ya kusa, tana hasaso kalar wahalar da zata sha. Shisa yanzun ma bata damu ba, daman Anisa na mata fadan ta dinga tafiya da tsintsiya bandaki, ta wanke wajen kafin ta tsugunna, shisa rashin period din bai wani dameta ba, tasan ba zai wuce infection din da har a asibiti aka fada mata idan bata kiyaye ba zai iya dawowa, saboda babu matsalar da take damun mata irin wannan, babu kuma abinda yake da wahalar sha'ani kamar shi. Idan ta koma makaranta sai ta sake zuwa asibiti, zuwa yanzun kam zata shana abinta.

*

Fitowa tayi daga bangaren ta, tana jin Intisar na fadin

"Ayya ko ina ne fa babu network din glo, ga nawa ma ya dauke"

Bata bi ta kanta ba, cigaba tayi da tafiya tana daga wayarta, sai kuwa ga tsinke daya ya kawo ya sake daukewa, a ranta take fadin

"Ga shi na fara zuko sji, amman yaran nan sai suce maka ai ko ina ne babu network"

Bilal take ta kokarin kira tunda ya fita, sai take ganin kamar ya koyi yawo yanzun, duk da yakan ce mata wajen tirenin din kwallon kafa yake tafiya, ko wajen Aisha. Fitar tashi tana mata yawa, sam baya son zama a gida kamar yanda sukan yi, ta kira MTN din shi bai daga ba, tasan karamar wayar na tare dashi, nan ne kuma glo din su yake, dabarar ta gwada kiran shi da wata lambar bata zo mata ba sam. Intisar da taso fada mata zagi ta sha, sai tayi shiru tana dariya. Harabar gidan ta fita sosai, kamar daga sama taga giccin Layla, yanayin da ya sata raba idanuwanta da wayarta tana kallon yarinyar.

Ba cika kallonta tayi ba saboda yanda bata cikin yan kayanta, amman yau wani irin bugawa taji zuciyarta nayi, fara ce dan fara, Layla na da hasken fata kamar su Rayyan, amman sai taga ta kara yi mata wani sanannen haske, hasken da bata fata ya kasance tare da budurwa kamar Layla. Sosai zuciyarta take bugawa, musamman yanda Layla ta dawo ta wuce cikin wani irin rashin kuzari da ba nata bane, ita din mai kazar-kazar ce, bata san kiyayyar da takewa Maryama bata mamaye dukkan zuciyarta ba sai yau, sai yanzun da ta tsinci kanta da furta

"La hawla wala quwwata ila billah"

Tana saurin kauda zargin da yake son darsuwa a cikin zuciyarta. Kafin ta dora da addu'ar neman tsari daga shaidan da kan jefa zato kala-kala a zuciyar dan adam. Tsoron da taji ne ya mantar da ita neman Network din da ta fito yi tana komawa ciki. Duk surutun da Intisar takeyi mata bata jiba balle tabi ta kanta, sam zuciyarta ta kasa samun natsuwa, ko dan kacokan rayuwarta akan yaranta ne? Takan san basu da lafiya kafin ma su farga da basu da lafiya, ko jikin Rukayya ya taba nata takan gane idan zafin jikin dai-dai yake ko akasin haka

"Ayya lafiyata kalau fa, ina ga gajiyar makaranta ce"

Rukayya kan fadi wasu lokuttan idan tace mata ta sha ko panadol ne, sai ta barta, karshe da safe zaka ji tana cewa

"Kinga zazzabi ya dameni ko Ayya?"

Harararta takan yi ta share, sai ta fara dariya, a cikin yaranta kaf Rayyan ne kadai bata gane wani abu a kan shi. Shisa yanzun tasan akwai abinda yake damun Bilal da yake boye mata

"Akwai wanda zai san damuwar ka idan ban sani ba Bilal?"

Ta bukata bayan ya dawo da kwana biyu, amman murmushi yayi mata

"Bakomai Ayya, idan akwai zan fada miki kinsani"

Kai ta jinjina, bai saba mata karya ba, a yanda sautin muryar shi ta fito tasan karya yakeyi. Bata ja maganar bane saboda batason ta saka shi sake yi mata wata karyar akan wadda yayi mata. Fatanta matsalar kar ace daga wajen Aisha ne yake fuskantar ta, saboda damuwa ba abokiyar Bilal bace ba, banda ita Rayyan ne kawai take tunanin zai san damuwar Bilal, shikuma ba zai taba fada mata ba. Addu'a kawai takeyi Allah yasa ba wata damuwa bace mai girma. Shisa take son yakice Layla da ta tokare mata makoshi daga ranta, saboda bata bukatar wata damuwa ta rashin dalili a kwanakin nan.

Har dare ma bayan tayi isha'i taci abinci nan falon tayi zamanta tana kallon wata dirama a tashar Dadin Kowa. Amman hankalinta rabi ne a kai, rabin na wajen kofa tana jiran ta inda zata ga bullowar Bilal, har Abbu ya riga shi dawowa yau. Bai shigo ba sai wajen tara na dare, sallamar shi ta amsa a hankali tana kallon shi ya wuce kitchen ya zubo wani abinci da ko Huda yayiwa kadan ya dawo falon ya samu kujera ya zauna

"Me ake kallo ne Ayya?"

Numfashi ta sauke tana nazarin yanayin shi, gashin daya ajiye a fuskar shi bai hanata ganin ramewar da yayi ba, yau sai take ganin kamannin da akan ce yanayi da ita sun fito sosai, saboda ramar ta kara fito da hancin shi
Chapter 61 · 0% Book details